KAMAR yadda ya saba yi a duk shekara, fitaccen mawaƙin siyasa Alhaji Dauda Kahutu (Rarara), ya raba wa wasu daga cikin abokan aikin sa maza da mata kyautar kuɗi a matsayin tallafin azumi.
Sanarwar bada tallafin ta fito ne daga mai taimaka wa mawaƙin a soshiyal midiya, wato Rabi’u Garba Gaya.
A ɓangaren iyaye maza da su ka samu tallafin N50,000 kowannen su, akwai Umarun Gaya, Magaji Mijinyawa, Iliyasu Abdulmumini Tantiri, Babandi Daɗin Kowa, Bashir Bala Ciroki, Malam Haruna Hayaƙi, Malam Inuwa, Sani Idris Kauru (Moɗa), Garba Gashuwa, Billy O, AGM Bashir, Bala Anas Babinlata, Sa’idu Gwanja da kuma Hankaka.
Dukkan su za su karɓi saƙon su a wurin fitacciyar jaruma Aisha Idris Ahmad (Ayshatulhumaira), wadda ta na ɗaya daga cikin hadiman Rarara.
A ɓangaren iyaye mata, akwai Baba Duduwa, Hajiya Tambaya, Hajiya Sadiya, Lubabatu Madaki, A’ishatu Umar Mahuta, Rabi Sufi, Ladidi Tubles, Safiya Kishiya, Hindatu Bashir, Bilkin RK, Hajiyar Nas Kaduna, Maryam CTV, da Halima Kara-Da-Kiyashi.
Su ma za su karɓi saƙon N50,000 kowannen su a wurin Ayshatulhumaira.
Sai kuma mata matasa, akwai Fati Mohammed, Ummi Nuhu, Rahama Sirace, Farida Jalal, Maryam Giɗaɗo, Hafsat Shehu, Fati Al-Amin, Rahama MK, Firdausi Kwalli da Sayyada Sadiya Haruna.
Su ma a wurin Ayshatulhumaira za su karɓi tallafin su na N50,000 kowacen su.
A kuma ɓangaren matan aure mawaƙa, akwai A’isha Nagudu, Zainab Deman, Sa’a Vocal, Aina’u Adam Yabo, Ummi Abdullahi Yabo, Fa’iza Badawa, Maryam A. Baba, Murja Baba, Naja’atu Ta-Annabi, Firdausi ‘Yar Dubai, Asiya Sudan, Suhaima Danko, Sa’a A. Yusuf, Zuwaira Isma’il, Zahra’u Sharifai, Husaima M. Fire, Fati Rayuwa da Asma’u Sadiq.
Su kuma za su karɓi saƙon N30,000 kowacen su a wurin matar Rarara, Hajiya Sadiya.
Mutane da dama sun yaba wa mawaƙin a kan wannan hoɓɓasa da ya yi.