AN zaɓi Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) a matsayin shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano.
An zaɓe shi ne ya jagoranci sabon kwamitin gudanarwa na reshen ƙungiyar, mai membobi 12, wanda aka rantsar a wani taro da aka yi a ɗakin taro na Kannywood TV da ke Tudun Yola, Kano, a yau Laraba, 27 ga Afrilu, 2022.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa ba kaɗa ƙuri’a aka yi a zaɓen ba, kawai amincewa kowa ya yi cewa a faɗi sunayen ‘yan takarar muƙaman ƙungiyar, a yi wa waɗanda su ka cancanta mubayi’a ba tare da wani ɓata lokaci ba, wato abin da ake kira ‘consensus’ a Turance.
Shugaban kwamitin zaɓe na ƙungiyar, fitaccen jarumi Umar Gombe, shi ne ya gudanar da zaɓen.

Ɓullar labarin zaɓen a yau ya yi wa ‘yan fim da dama daɗi, ganin cewa waɗanda aka zaɓa ɗin nagartattu ne kuma gogaggu a harkar fim, don haka ‘yan fim na gida da na waje sun taya su murna.
Rassan MOPPAN na Filato da Jigawa na daga cikin rassan ƙungiyar na jihohi da su ka aika da saƙon taya murna tare da fatan alheri.
Bashir Lawan Gumel, Sakataren MOPPAN na reshen Jigawa, ya ce: “Ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Jigawa na taya sababbin shugabanni na Jihar Kano murnar samun wannan muƙamai, da fatan Allah ya ba su ikon sauke nauyin da ya rataya a kan su.”
Daga Kano kuma, fitaccen darakta kuma mai ba gwamna shawara kan harkokin nishaɗi, Ishaq Sidi Ishaq, cewa ya yi, “Duk da yake an ce ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara arba’in, amma ga dukkan alamu zan iya cewa waɗannan bayin Allah za su taɓuka abin arziki!
“A ra’ayi na, ba a taɓa samun irin wannan haɗin a shugabancin Kano MOPPAN ba – sai dai mantuwa. Fatan mu shi ne Allah ya sa su ba maraɗa kunya, Allah ya yi masu jagora, ya ba su ikon gabatar da ayyukan cigaba cikin nasara, amin.”
A nasu ɓangaren, jagororin Majalisar Dattawan Kannywood (Kannywood Foundation and Kannywood Elders Forum) sun ce su na “matuƙar farin cikin taya sabbin shuwagabannin MOPPAN” na Kano murna.
A saƙon da ya aika a madadin kwamitin yaɗa labarai na Majalisar Dattawan, fitaccen jarumi Alhaji Kabiru Mohammed Maikaba ya ce, “Mu na taya ku murna da addu’ar Allah yai maku jagora kuma ya sa ku zama sanadiyyar kawo cigaba da ɗaukakar wannan masana’anta.
“A matsayin mu na dattawan wannan masana’anta mai albarka, mu na so mu tabbatar maku goyon bayan mu wajen ba ku shawarwari nagari da kuma ba ku taimako a inda buƙatar hakan ta taso.

“Mu na taya ku da addu’ar Allah ya shige mana gaba wajen haɓaka harkokin wannan masana’anta mai albarka. Allah ya sa albarka.”
Waɗanda aka zaɓa ɗin dai su ne:
1. Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) – Shugaba
2. Garba Sunusi Kalambaina – Mataimakin Shugaba
3. Kamal S. Alƙali – Sakatare
4. Balarabe Murtala Baharu – Mataimakin Sakatare
5. Sulaiman Abubakar (mpeg) – Ma’aji
6. Nura Shariff – Sakataren Tsare-tsare
7. Asma’u Sani – Jami’ar Walwala
8. Misbahu M. Ahmad – Jami’in Yaɗa Labarai (I)
9. Mubarak Abba – Jami’in Yaɗa Labarai (II)
10. Isma’il Khalil Ja’en – Sakataren Kuɗi
11. Hayatuddeen Yakubu – Mai Bincike (I)
12. Sudais Ahmad – Mai Bincike (II)
![]()







