• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Labari na: Tsakanin gimbiyar Zuru da ‘Yartsana

by DAGA IBRAHIM SHEME
April 23, 2022
in Marubuta
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WANI lokaci, ba ka shirya ba sai kawai ka tuno da wani aikin alheri da wani ya yi maka ko wata gudunmawa da ya bayar a rayuwar ka. Wani lokaci gudunmawar ƙanƙanuwa ce idan an auna ta, to amma kuma ta yi babban tasirin da ba ka kula da shi sosai ba, kuma wani wanda ke tare da kai bai sani ba. Abin da ya faɗo mani a rai kenan a rana mai kamar ta yau.

Idan an dubi hotunan da ke tare da wannan rubutun, za a ga shafin littafi a rubutun hannu da na shafin mujalla da na wata mace da kuma guda biyu na bangon littafin ‘Yartsana da aka wallafa.

Hoton farko na shafi na 136 ne na littafi na mai suna ‘Yartsana a lokacin da na rubuta shi da hannu. Na rubuta shi a cikin 1992/93 domin samar da nishali ga masu karatu a cikin mujallar mako biyu-biyu mai suna Rana, ta kamfanin Hotline a Kaduna. A lokacin, ni ne editan mujallar. An riƙa gutsura labarin a duk mako biyu da mujallar ke fitowa; wani lokacin, a ranar da za a tafi buga mujallar na ke rubuta cigaban labarin da za a buga!

Hoto na biyu, shafin mujallar ne kamar yadda ake buga shi.

Hoto na uku, wata matashiya ce mai suna Mary Isah Chonoko. Ba kowa ya san ni da Mary ba a yanzu, amma duk wanda ya san ni daga wajen 1999 zuwa sama da shekara 15, to ya san ni da Mary. Ita ce sakatariya ta bayan na kafa kamfanin wallafa littattafai na Informart a cikin 1995, kamfanin da ya kasance mai wallafa mujallar Fim daga 1999 zuwa yau. Sai da ta kai daga baya har Mary ta zama manajar kasuwanci ta kamfanin.

Mary ce ta buga littafin ‘Yartsana a komfuta, wato ‘typesetting’. Na tattaro mata shafukan da mujallar Rana ta buga, sannan kuma da yake ita Rana ba ta kammala buga littafin ba aka rufe ta (lokacin ina Ingila), sai na ci gaba da rubuta ƙarashen labarin, ina ba Mary, ita kuma ta na bugawa a komfuta. 

A lokacin da Mary ta ke wannan aikin ne kuma ta bada wata gagarumar gudunmawa ga littafin wanda ba a sani ba sai a yau – wato sauya sunan tauraruwar labarin littafin daga Balaraba zuwa Asabe! Da farko ma sunan littafin ‘Balaraba’, kuma tauraruwar labarin ma sunan ta kenan. A haka aka buga shi a mujallar Rana tun a 1992/1993 – shekaru da dama kafin haɗuwa ta da Mary. 

To, Mary na tsakar wannan aikin na shigar da littafin cikin komfuta sai fitacciyar jarumar finafinai ɗin nan Balaraba Mohammed ta rasu a ranar da aka ɗaura mata aure, a wani haɗarin mota a kan hanyar kai ta gidan miji daga Kaduna zuwa Kano. Duk da yake labarin littafin bai da wata alaƙa da marigayiyar (domin an buga shi a Rana tun na kafin Balaraba ta shiga harkar fim har duniya ta san ta), Mary ta hango cewa fito da littafin da sunan Balaraba zai iya damun wasu, su ce ai saboda ficen jarumar ne aka raɗa wa tauraruwar littafin sunan ta, musamman ma dai tunda an san alaƙar mu da harkar fim. Mary ta ce mani lallai in sauya sunan tauraruwar daga Balaraba zuwa wani sunan.

Shi kenan, na tafi na shiga kogin tunani ina ninƙaya. Can sai na sanya mata sunan rana, Asabe. Dalili shi ne a ranar Asabar na sauya sunan. Sai na koma cikin littafin na sauya wani waje a labarin inda ake alaƙanta sunan “Balaraba” da kyawun fuskar ta, na alaƙanta shi da sunan rana na Asabe, wadda sunan ta na yanka Zainab.

Na tabbatar marubutan ƙirƙira da dama za su tuna yadda irin hakan ta faru da su, wato na wani dalili da ya saka tilas su ka sauya wani suna a cikin labarin da su ke rubutawa, ko ma su ka sauya sunan littafi baki ɗaya.

Hoto na huɗu, bangon littafin ne a yadda ya fara fitowa. Hoto na biyar kuma bangon bugu na uku ne na littafin.

A yau, Ranar Littafi Da Kare Haƙƙin Mallaka ta Duniya (World Book and Copyright Day), na ga ya dace in yi wa Mary godiya kan wannan gudunmawa da ta bayar, da sauran ƙwazon da ta nuna a wajen aiki. Duk wanda ya san Mary, irin su Aliyu A. Gora II (wanda ya taɓa zama Editan mujallar Fim a wancan lokaci), to ya san ta da sauƙin kai da girmama jama’a da aiki tuƙuru, sannan da bada kyakkyawar shawara ga duk wanda ya dace. Mary, sarauniyar Zuru komai nama, na gode! Da fatan komai naki na tafiya daidai a jihar ku ta Kebbi, inda ki ke da zama a yanzu.

(Bayanin ƙarshe: Hukumar UNESCO ta Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware 23 ga Afrilun kowace shekara a matsayin Ranar Littafi ta Duniya. An fara a ranar 23 ga Afrilu, 1995. An zaɓi wannan ranar ne domin ta yi daidai da ranar mutuwar shahararren marubucin Ingila William Shakespeare da fitaccen marubucin ƙasar Spain mai suna Inca Garcilaso de la Vega).

Loading

Tags: Adabin HausaAliyu Gora IIBalaraba MohammedGarcilaso de la VegaHotlineInformart PublishersIngilaKebbiMajalisar Ɗinkin DuniyaMary Isa ChonokoRanaRanar Littafi ta DuniyaUNESCOWilliam ShakespeareWorld Book and Copyright DayYartsanaZuru
Previous Post

Jarumi Umar Gombe ya zama jami’in shirye-shirye a Northflix

Next Post

Gidan Dabino ya zama shugaban MOPPAN reshen Kano

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ya na jawabi a wajen taron rantsar da sababbin shugabannin MOPPAN reshen Jihar Kano

Gidan Dabino ya zama shugaban MOPPAN reshen Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!