KAMFANIN nuna finafinai ta hanyar yanar gizo, Northflix Nigeria Limited, ya naɗa fitaccen jarumi Umar Gombe jami’in shirye-shirye.
Kamar yadda mujallar Fim ta taɓa ba ku labari, Northflix kamfani ne da ke sayen finafinan Hausa su na nunawa a manhajar su, inda mai kallo zai biya kuɗi ya kalla a manhajar su mai suna Northflix a yanar gizo, kamar Netflix na Amurka.
An ƙaddamar da manhajar Northflix a Kano a ranar 9 ga Yuni, 2019.
Sanarwar naɗin Umar Gombe da ke ɗauke da sa hannun shugaban Northflix, Alhaji Jamilu Abdulsalam, ta nuna cewa an naɗa shi wannan muƙami na jami’in shirye-shiryen kamfanin na farko.
Sanarwar ta ce Umar zai jagoranci fannin shirye-shirye na kamfanin wajen bunƙasa harkar kasuwancin finafinan Hausa a duniya.
Da ya ke ƙarin haske dangane da kamfanin, Alhaji Jamilu, wanda kuma ake kira Jamil Hajaj, ya nuna cewa musabbabin buɗe Northflix shi ne domin ƙara haska finafinan Kannywood a idon duniya ta hanyar kasuwanci wanda, a cewar sa, tuni duniya ta koma yanar gizo wajen sarrafa harkokin kasuwanci, musamman ma na finafinai.
A cewar sa, kamfanin ya samu yin haɗin gwiwa da wasu kamfanonin shirya finafinai na Kannywood, waɗanda su ka haɗa da FKD Productions, Saira Movies, Falalu A. Ɗorayi Movies, Uzee Concept, Maishadda Movies, da sauran su.
Takardar sanarwar ta ce ana sa ran Umar Gombe zai yi amfani da ƙwarewar sa wajen tafiyar da ayyukan da aka ɗora masa.
Umar dai shi ne mataimakin sakataren Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN).
Mujallar Fim ta samu sanarwar daga kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma.