• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda gwamnati ta ƙaryata MOPPAN da Ahmad Sarari kan bikin Zuma

by DAGA ALI KANO
May 5, 2022
in Labarai
0
Dakta Chidia Maduekwe, Manajan Daraktan NFC

Dakta Chidia Maduekwe, Manajan Daraktan NFC

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation, NFC) ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar fim da su yi watsi da ƙudirin ƙaurace wa Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma wanda ‘yan fim na arewacin ƙasar nan su ka hau.

Idan kun tuna, a jiya ne mujallar Fim ta ba ku labarin sanarwar da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners’ Association of Nigeria, MOPPAN) da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (Arewa Filmmakers Association of Nigeria, AFMAN) su ka bayar cewa kada membobin su su halarci bikin na Zuma wanda ake gudanarwa yanzu a Abuja.

Ƙungiyoyin sun zayyano wasu ƙwararan dalilai masu nuni da irin wariyar da su ka ce hukumar ta NFC na nuna wa ‘yan Arewa a game da bikin.

Shugabannin ƙungiyoyin, Dakta Ahmad Sarari (na MOPPAN) da Alhaji Sani Sule Katsina (na AFMAN) su ne su ka rattaba hannu a kan takardar koken su kan lamarin wadda su ka rubuta wa Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed.

To amma ita ma hukumar NFC ta yi kakkausan martani cikin wata takarda ga manema labarai da Daraktan Hulɗa Da Jama’a na hukumar, Mista Brian Etuk, ya saki a yau Laraba a Abuja.

Hukumar ta ce, “Mu na kira ga masu ruwa da tsaki a harkar fim a Nijeriya baki ɗaya da su yi watsi da sanarwa ga manema labarai da  MOPPAN ta bayar wadda ke ɗauke da duk wasu nau’o’i na  baƙar yaudara a matsayin ‘yan kwangilar ɗaura yaƙi a madadin wasu, wanda sam bai dace ba.

“A bayyane yake cewa wasu ne ke ɗaukar nauyin ƙaryar da aka yaɗa domin su tozarta mu da nufin lalata babbar nasarar da bikin ya cimmawa ya zuwa yanzu, kamar yadda ake gani a rahotanni da dama da aka buga a jaridu da yanar gizo da sauran kafofi.” 

A cewar Mista Etuk, a sabon tsarin da aka yi wa Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma da ake yi shekara-shekara, tun daga 2017 ake gudanar da shi a ko yaushe daga ranar 1 zuwa 7 ga Disamba. 

Ya ce: “Da aka duba aka ga buƙatar cewa a tabbatar da bikin ya zama na ƙasa gaba ɗaya a zahirance, a cikin 2018 sai NFC ta samu Hukumar Gundumar Birnin Tarayya (FCTA) domin su riƙa yin haɗin gwiwar shirya bikin tare da naɗa Abuja matsayin ‘Birnin Baƙunci’ na bikin.

“Wannan ya haifar da sakamakon rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) cikin Nuwamba 2021.

“Daga nan ne aka sauya lokutan bikin zuwa ranakun 2 zuwa 9 ga Afrilu, 2022. Matsalolin da aka samu wajen shirya bikin masu alaƙa da aiwatar da haɗin gwiwar da aka tsara su ka sa aka yanke shawara tare da juna cewa a matsar da bikin zuwa ranakun 1 zuwa 7 ga Mayu, 2022.”

Jami’in na NFC ya ce ganin cewa akwai shagulgulan Sallah a daidai lokacin fara bikin, sai aka maida manyan abubuwan da za a yi a bikin zuwa ranakun 4 zuwa 7 ga Mayu, 2022.

Etuk ya ce: “An tsara cewa a ranakun 1 – 3 ga Mayu, 2022 za a yi  shirin horaswa (wato ‘training’) na sababbin ‘yan wasa wanda matasan Nijeriya sama da 500 da aka zaɓo daga wasu jami’o’i daga jihohin arewa da kudu na Nijeriya za su shiga, kuma daga addinai mabambanta, ana horas da su kan dabarun shirya fim da kasuwancin sa.

“Hakika, a wajen tsare-tsaren bikin, masu shirya shi sun ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Abuja domin kai masu abincin Sallah da tufafi kamar yadda jaridu da dama su ka buga, kuma an ɗauki nauyin nuna fim kyauta saboda Sallah a gidan sinima na Silverbird domin gudunmawa ga shagulgulan da ake yi a wannan lokacin.

“Ya kamata a kula da cewa an yayata waɗannan ranaku sosai tare da sani da kuma amincewar Shugaban MOPPAN, Dakta Ahmad Sarari, wanda shi ya zaɓi kan sa (don shiga bikin) da sakataren sa na yaɗa labarai da wasu mutum biyu ta hanyar saƙon tes da ya aiko a ranar 28 ga Afrilu, 2022, amma wai daga baya sai su ka je su ka rattaba hannu kan waccan takardar sanarwa ga manema labarai a ƙarƙashin MOPPAN.”

Ya ƙara da cewa an tsara cewa dukkan su za su iso wajen Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma a ranar 4 ga Mayu, 2022, kuma har an aje masu ɗakuna a otal ɗin Nicon Luxury da ke Abuja.

Ya ce: “Ya na da muhimmanci a kula da cewa tun daga lokacin da Manajan Darakta kuma Babban Shugaban NFC na yanzu, Dakta Chidia Maduekwe, ya kama aiki, a ko yaushe ya kan yi ƙoƙari sosai wajen tafiya tare da MOPPAN a dukkan tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar.

“Sanin kowa ne cewa MOPPAN da membobin ta su ne guruf na farko na ‘yan fim da Hukumar Finafinai ta Nijeriya ta yi wa jagora su ka haɗu da Shugaba Muhammadu Buhari.

“Haka kuma Manajan Daraktan ya sha yin zama na musamman domin tattaunawa da kuma musayar ra’ayi da shawara tare da masu ruwa da tsaki a harkar fim da ‘yan industirin fim daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Hakan ya haɗa har da ‘yan Arewa. 

“A yanzu haka, akwai wani fitaccen memba na MOPPAN da Hukumar Finafinai ta Nijeriya ta ba aiki ya na shirya mata wani shirin faɗakarwa (documentary) mai taken ‘Ɗanfodiyo: Mujaddadin Afrika ta Yamma’ (‘Ɗanfodio: The Reformer of West Africa’.”

Loading

Tags: 'yan gudun hijiraAFMANAhmad SarariArewa filmmakersbajekoliBrian EtukChidia MaduekweDanfodioEid el-FitrFCTAIDP campsLai MohammedMOPPANMuhammadu BuhariNFCNigerian filmsSallahSani Sule KatsinaSilverbird CinemaZuma Film Festival
Previous Post

Saboda wariya, ‘yan Kannywood sun ƙaurace wa Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma

Next Post

Adabin Bariki

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post

Adabin Bariki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!