• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Adabin Bariki

by DAGA G. AUWAL ƊANBARNO
May 7, 2022
in Marubuta
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

(Na sadaukar da rubutun nan ga malami na, Farfesa Ibrahim Malumfashi)

YANYU idan na tambaye ki me ya sa ki ke wannan sana’a, me za ki ce? Mecece ribar ki a wannan sana’a? Yaushe ki ka fara, yaushe za ki daina? Nawa ki ka tara, kadarar nawa ce da ke a ƙasa?

Na san ba ki da wata amsa. Abin da duk karuwa ‘yar’uwar ki ke faɗi, ta gudo ne ko ta shiga sana’ar karuwanci saboda gudun auren dole. Ke ma na san amsar kenan. Ta yiwu wanda aka ba ki kin guje shi ne saboda tsufan sa, ko rashin wayewar sa, ko munin sa ko rashin tsabtar sa.

Daga lokacin da ki ka fara sana’ar karuwanci za ki iya lissafa mazan da ki ka kwanta da su? A cikin su akwai tsofaffi, akwai gajeru da dogaye, akwai baƙaƙe da farare, akwai ƙazamai da kucakai. Akwai masu lafiya da marasa lafiya. Har ma da kucakai da ƙazamai sun kwashi rabon su. A’ah! to wa zai ƙi tunda sokuwa ta buɗe zani? Kin guji zaɓin iyaye, kin zaɓi son zuciyar ki.

Ba ki ga yadda kamannin ki su ka juye ba, kin zama kamar wata karya, matar kare. Yanzu dubi ɗakin nan da ki ke ciki, ko tagar kirki babu. Dubi wata tsinanniyar katifa. Katifar da kowa da kowa ke kwanciya in har ya biya kuɗi; kin zama uwani ware-ware.

Nawa ne farashin naki? Ko kuma duk mutumin da ya zo ki na masa farashi gwargwadon shigar da ya yi? A kullum ki na samun kamar nawa a wannan haja da ki ka ke kasawa? Ga alama dai babu faɗuwa a wannan sana’a. E mana, ina faɗuwa a kayan da ba sayo shi ki ka yi ba?

Ni kai na da ki ka ga na shigo ɗakin ki, kin ɗauka komar ki ta kama wani babban kwastoma. Ni aiki na wa’azi da nasiha ga karuwai irin ku. Ki na gani na kin san ba gugan da ke shiga kowace rijiyar kwakware ne ba.

Matsala ta da ku karuwan Hausawa, ba kamar ƙabilu ba. Ita karuwa ƙabila za ki same ta ta na karatu ko ta sa lokacin barin karuwancin. Ko ta kama sana’ar saye da sayarwa. Amma ku karuwan Hausawa kamar dabbobi ku ke, ba kwa ko lissafin lokacin shiga da lokacin dainawa. Kullum fa mutuwa ku ke yi, daga wadda ciwo zai kama sai wanda za ta yi hatsari. Wasu kuma shaye-shaye ke kashe su.

Kullum cikin fargabar kamun ‘yan sanda ku ke, shi ya sanya da dama ku ke son yin saurayi da mai ɗamara – soja ko ɗan sanda ko ɗan anti-drug agency, dss.

Su kuma masu ɗamara mutane ne masu son na banza. Tunda ba biya su ke yi ba dole su tsaya su kwashi bonanza.

Abin da na ke so na ji daga gare ki, shin me ya shigar da ke wannan sana’a?

* Auwal Garba Ɗanbarno marubuci ne a Kano

Loading

Tags: adabin barikiaureauren doleDanbarnoIbrahim Malumfashikaruwakaruwancisana'ar
Previous Post

Yadda gwamnati ta ƙaryata MOPPAN da Ahmad Sarari kan bikin Zuma

Next Post

2023: INEC ta ƙayyade wa jam’iyyu wa’adin kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Mista Festus Okoye

2023: INEC ta ƙayyade wa jam'iyyu wa'adin kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!