FITACCEN mawaƙi kuma jarumin Kannywood Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) ya bayyana cewa a masana’antar finafinai ta Kannywood sai mace ta bada kan ta an yi zina da ita sannan ake sanya ta a fim.
Naziru ya yi wannan iƙirarin ne a wani gajeren bidiyo mai tsawon minti 6:45 da ya ɗora a shafin sa na Instagram a daren jiya inda ya ke sukar masu da’awar cewa maganar da fitacciyar ‘yar wasa Ladin Cima ta yi ba daidai ba ce, wato da ta ce ba a taɓa biyan ta sama da N5,000 ba a aikin fim.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito a jiya cewa jarumai biyu, Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi, su na daga cikin ‘yan fim da maganar da Hajiya Ladin Cima (Tambaya) ba ta yi wa daɗi ba, har su ka fito su ka bayyana cewa su sun biya ta dubban nairori a wasu ayyukan fim da ta yi masu.
A martanin bidiyo da ya wallafa a daren jiya, wanda ya yi wa take da “‘Yan Fim A Ji Tsoron Allah Fa”, Naziru ya faɗa wa su Ali da Falalu cewa, “Gaskiyar magana, gaskiyar magana, gaskiyar magana, ‘yan fim ba Allah a ran ku. Babu!”
A cikin ɗacin zuciya, ya ci gaba da cewa, “Kwata-kwata waɗanda su ka yi magana su ka yi ‘againsting’ maganar matar nan da ta yi, wallahi ba Allah a ran ku. Babu! Babu! Yanzu kamar waɗanda na ga maganganun su su biyu, Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi, don Allah don Annabi ku ne za ku ce ba ku san anai wa mutanen nan, anai wa dattijan nan wannan abin ba? Su tashi aiki a ɗau biyu dubu ɗaya a ce masu za a kira su. Haba! Haba! Haba! Ittaƙul-Lah! Ku ji tsoron Allah mana; kun san ana yi.
“Matar nan ku ƙirga; yanzu bari in fara daga kan Falalu Ɗorayi, matar nan a ƙirga fim nawa ta yi a industiri? Falalu, matar nan ta yi fim ya fi nawa? Fim nawa ne ka sa ta har za kai ‘againsting’ maganar ta don ta ce dubu biyu dubu huɗu ake ba ta?
“Ai a ta yi fim ma ya kai ashirin, to ya kamata a ce sai fim ta yi goma sha takwas an biya ta wannan kuɗin, shi ne in tai maganar ba ta yi daidai ba. Amma fim ɗin, in ta yi ashirin ɗin fim nawa aka sa ta? Falalu Darakta, mu yi maganar gaskiya mana! Mu yi maganar gaskiya mana!
“Mu da ku mun san akwai yaran nan, za ka zo ka sa mutum a fim, furodusa ya kuma dinga cutar mutane. Ba ma ƙoƙari mu biya su da kan mu. Mun san da wannan.
“Ko kuma a’a, shi Ali Nuhu fim nawa ya sa ta? Nawa ne ya ba ta dubu arba’in?
“Mun sani, ba ƙarya ba ne ba. ‘Recently’, an yi wannan. Na kira mutane su yi shutin ; tsofaffi ne na kira su su ka zo su ka yi shutin. Ina tambaya nawa ake biyan su, aka ce dubu biyu-biyu. Na kira wata, ta yi shutin ta gama, an ɗau kuɗi za a ba ta, ana ba ta kuɗin na ce nawa ake biyan su? Da bakin ta ta ce ga shi ga shi, kuma na bincika na ga haka ne.
“Haba, mun san wannan maganar man. Ku bar tsohuwa ta zauna lafiya. Wannan da gaske ne, ba ita kaɗai ba ce ba, ba kuma ma tsofaffi kawai ake wa ba. Duk wanda za a sa a fim, in dai zai fito a sin ɗaya biyu ne, sai dai a ba shi irin wa’innan kuɗin – dubu ɗaya dubu biyu. Ba shi ya sa harkar ta ke ta yin ƙasa ba?
“Kawai in ku na da niyyar ku gyara, ku fito ku gyara. In kun kawo akto, ku biya shi da kan ku in ku na da wannan kyakkyawar niyyar. Amma mu yi maganar gaskiya.
“Ni na san finafinan da ba ma biyan mutum ake ba, shi ya ke biya – kuma kun san da wannan, to meye abin wata magana a nan?
“Yanzu wannan tsohuwar da aka sa ta gaba ake ta wannan magana, so ku ke hankalin ta ya tashi, wani abu ya zo ya same ta na ciwo daban?
“Na rantse da Allahn da ya halicce ni, ni na rantse, in kuma wani ya isa shi ya fito ya rantse ya ce ba haka ake wannan zaluncin ba.
“Wallahi tallahi haka ake yi. Dubu biyu, wani ma tura shi za a yi a ce za a yi mar waya. Wasu kuma sai sun biya kuɗi ko sun bada wani abu makamancin kuɗi. Ba abin da mu ke ‘facing’ ba kenan a industirin? Ko ki bada kuɗi ko kuma ki bada kan ki! Ba shi ne abubuwan da ake fama da su ba?
“Haba, meye ma wannan maganar ta faɗa ana ba ta dubu biyu? Ai kowa ma ya sani, sai dai wanda ya ke ƙin Allah.”
Naziru Sarkin Waƙa ya ce su Ali da Falalu su je su yi gyara, kuma idan mutum ya ga ba ya da kuɗi to kada ma ya fara shirya fim.
Ya ce kada a ga kamar ba ya cikin ‘yan fim ko da yaushe a ɗauka cewar bai san abin da ke faruwa ba. Kuma duk da yake shi ba furodusa ba ne, amma maganar haka ta ke – “a ɗau dubu biyu a ba mutum, a ce masa je ka za a turo, ba a turo ba. Ko kuma mace ce a ce sai an yi wani abu da ita za a sa ta a fim. Wannan maganar haka ta ke, ba ƙarya ba ne ba!
“In kuma kun ji haushi an faɗa, ku ku ka jawo saboda kun so ku danne gaskiya.”
A ƙarshe, ya ragargaji shugabannin Kannywood da cewa: “Dukkan wanda su ke kiran kan su manya a masana’antar nan, ba lissafin yadda ‘yan masana’antar za su ci gaba gare su ba, lissafi ne na yadda su ya za ai sabis ɗin su ya ƙaru; in darakta ne, tunani ya ke me zai kawo; in furodusa ne, tunani ya ke me zai kawo ya sayar; in akto ne tunani ya ke ya zai yi ya yi gaba; in mawaƙi ne, tunani ya ke me zai yi sabo.”
Tura bidiyon ke da wuya, mutane su ka dinga sharhi a kai, wasu na goyon baya, wasu kuma na cewa mawaƙin bai yi daidai ba.
A cikin masu goyon bayan maganar tasa har da wasu ‘yan fim, wa]anda su ka haɗa da Rashida Lobbo, Sumayya Galadi, Salis Yomen, Stephanie Daɗin Kowa, Intisar El-Fallatah, Stella Arewa 24, Ali Artwork, da wasu.
Wasu ‘yan fim da kuma ba su goyi bayan sa ba sun haɗa da Saraki Tijjani, Abba Muhammad, Khalid Yusuf Ata da sauran su.
Da alama dai, wutar wannan maganar da Naziru ya cinno za ta ci gaba da ruruwa a cikin kwanaki masu zuwa.