JARUMI a Kannywood, Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale, zai angwance a mako mai zuwa.
Katin gayyatar ɗaurin auren ya nuna cewa za a ɗaura auren sa da masoyiyar sa Maryam Farouq Sale a ranar Juma’a, 27 ga Janairu, 2023, da misalin ƙarfe 1:30 na rana a masallacin Juma’a na Uhud da ke Na’ibawa a birnin Kano.
Ya kuma nuna cewa iyalan marigayi Alhaji Ado Tsakuwa da na Alhaji Umar Farouq Sale ne masu gayyatar.
Katin na ɗauke da lambobin waya guda uku domin tuntuɓar neman ƙarin bayani.
Sai dai katin gayyatar ne aka fitar, ba a ga hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) ba, kamar yadda aka saba ganin ‘yan fim su na saki kafin aure.
Katin na ɗauke da hoton Abale shi kaɗai, ya sha babbar rigar shadda da gilashi, ya na murmushi.
Ɗimbin masoyan sa sun taya shi murna da su ka ga katin gayyatar a soshiyal midiya.