FITACCEN furodusa Abdul Amart Mohammed (Maikwashewa) ya bayyana dalilin sa na jawo ‘yan fim cikin hidimar takarar shugaban ƙasa ta Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello.
Ya ce: “Babban buri na shi ne mu yi kira ga shi Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello, da ya fito ya yi mana takarar shugaban ƙasa, kuma mu bi mutane, mu nuna masu waye Yahaya Bello. Babban burin mu ya amsa kiran mu.”
Amart ya faɗi haka ne lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim bayani jim kaɗan bayan kammala wani taro na ƙaddamar da ƙungiyar ‘Yahaya Bello Network Group’ a jiya Laraba, 22 ga Satumba, 2021 a babban ɗakin taro na otal ɗin NUT da ke Mogadishu Layout, Kaduna.
Da ya ke bayani kan maƙasudin taron, ya ce, “Da farko mu na yi wa Allah godiya da ya ba mu ikon kiran taro, kuma an amsa. Wannan ya na nuna nasara ce ke tafe.
“Taro mu ka yi kusan jihohi 19 na Arewacin Nijeriya na ‘YBN’, wato ‘Yahaya Bello Network Group’.
“A yau mun ƙaddamar da wannan guruf, kuma mun bayyana tsare-tsaren da za mu yi a cikin wannan guruf ɗin.”

Amart ya nuna farin cikin sa ganin yadda matasa su ka haɗu don ganin an jaddada wannan tafiya. Ya ce, “Ku san ko da yaushe idan mu ka kira taro haka jama’a ke taruwa. A kowane lokaci na kira taro, na ga an yi taro haka sai na ji daɗi da farin ciki.
“Sannan kuma ya kamata su matasa su san kai waye. Don kusan yanzu babu wani matashi da za a zo a yaudara da magana ko da wani abu. Me ka yi, ya ka ke, ya mu’amalar ka ta ke da mutane, wannan shi ne sirrin nasarar mu. Kuma mu na zaman lafiya da kowa, kuma buƙatar matasa, buƙatar mu ce.”
Amart ya faɗa wa mujallar Fim cewa shi ba zai yi takarar siyasa ba, amma shi mutum ne mai tallata ɗan siyasa wanda ya yarda da nagartar sa.
“Kuma wannan tafiya tamu idan ka duba za ka ga matasa ne masu jini a jika, kuma kowa da shirin sa ya fito. Don haka wannan tafiya tafiya ce ta Yahaya Bello kawai,” inji shi.
Shi dai wannan taro, an fara shi da misalin ƙarfe 1:10 na rana, lokacin da fitaccen mawaƙi Alfazazee ya buɗe taro da addu’a.
Daga nan aka kira shi uban gayyar, wato Abdul Amart, inda ya yi jawabin maraba, sannan kuma Salisu Muhammad Officer ya gabatar da taƙaitaccen jawabin godiya ga mahalarta.
Daga nan sai aka kira jerin shugabannin wannan ƙungiya matakin ƙasa, su ka yi rantsuwar kama aiki, aka kuma kira jakadun ƙungiyar, waɗanda gaba ɗayan su ‘yan fim ne mata da maza, su ma su ka karɓi rantsuwar kama aiki.
Sai kuma aka fara kiran membobi jiha-jiha, amma su sai aka umarce su da duk wanda aka kira sunan sa ya tashi tsaye a inda ya ke zaune, sannan su ma aka rantsar da su. A kowace jiha an samu mutum biyar, wasu kuma shida.
An gayyaci wakilin gwamnan Jihar Kogi a taron, Kwamared Ahmad Jibril, wanda shi ne mai ba gwamnan shawara na musamman a kan matasa da ɗalibai, ya yi taƙaitaccen jawabi a madadin gwamna.
A jawabin nasa, Ahmad ya ce, “Jama’a wannan babban abin farin ciki ne a gare ni, domin na kafa shaida da irin ƙaunar da ake yi mana. Dalili shi ne lokaci ya yi wanda dole matasa su tashi su ce lokaci ya yi su jagorancin al’ummar su.
“Ya kamata matasa su tashi su ce lokaci ya yi wanda ya kamata mu faɗa wa juna cewa rigingimun da ake samu a Arewa ya ishe mu. Lokaci ya yi da ya kamata mu faɗa wa juna gaskiya da cewa talaucin da jama’ar mu ke ciki ya ishe mu.
“Lokaci ya yi da matashi ya kamata ya ɗana tunda dattawa sun yi, mun gode su ɗan ba mu dama mu samu albarka da shawarwarin su, don haka su ba matasa dama su yi jagorancin wannan tafiyar.
“Mu na so a kafa gwamnatin matashi na matasa a wannan ƙasa.

“A yau zan faɗa maku wata magana. Gwamna Yahaya Adoza Bello shi ne shugaban matasa, wakilin Arewa, Sarkin Yaƙin Kogi, Sarkin Yaƙin Talakawan Nijeriya. Yahaya Bello mutum ne wanda ya san darajar mutane, ya san menene ma’anar haramun, kuma ya san adalci.
“Ina so in nuna maku a yau yadda mu ke nuna masa ƙauna, ya na godiya. Kuma za mu nuna godiyar mu a lokacin da ya kamata.
“Kannywood tun a wancan lokacin ta na ƙoƙari. Kuma a Kano aka fara, abin na tuƙawa, aka zo Arewa ta Gabas, a ka zo Arewa ta Tsakiya, aka zo Nijeriya, aka zo Afrika, aka zo Amerika, aka zo Europe, kuma an rinƙa tafiya kenan domin Allah.
“A Kannywood ne kaɗai a Nijeriya mace za ta yi shiga wanda bai dace ba kuma a gyara mata. A Kannywood ne kaɗai namiji zai abin da ba daidai ba a gyara masa, domin duk wanda ya san mu a Arewa mun san darajar kawunan mu, kuma ba za mu bar wani ya janyo mana magana ba ko kuma ya yi abin da bai kamata ba.
“Jihar Kogi mu na kewaye da jihohi goma sha ɗaya, amma kuma duk da waɗannan jihohi da ke zagaye da mu, ba a taɓa cewa akwai ‘corona virus’ a Jihar Kogi ba.
“An samu shugaba wanda ke kishin talakawan sa, wanda ya ce ‘hunger virus’ ta fi kashe mutane fiye da ‘corona virus’.
“Mutum ne da bai bambanta fari da baƙi. Idan gwamna zai iya tashi ya ɗauko ma’aikaci daga Maiduguri, kun ga idan ya zo Jihar Kano ko Kannywood kwashewa kawai za mu yi mu wuce sai Villa.
“Mu na ƙara jaddada maku cewa Yahaya Bello abokin tafiya ne, ɗan amana ne. A ci gaba da yi masa iyakacin ƙoƙarin da za a yi. Idan Allah ya yarda lokaci ya yi, ku ma za ku san kun iya godiya.
“Allah ya ida mana da nufi, Allah ya tabbatar mana da alheri. Allah ya karkato mana da shi ya amince ya yi takara. Allah ya kawo mana zaman lafiya da arziƙi a ƙasar nan, mu na godiya.”
Daga nan kuma sai aka shiga fagen nishaɗi, inda aka cashe da waƙar haɗakar da mawaƙan Kannywood su ka yi wa Yahaya Bello, wanda aka yi gasar rawa a kan ta kwanakin baya.
Mawaƙa da ‘yan fim ɗin da su ka fito a cikin bidiyon waƙar sun bayyana a lokacin cashewar sai dai ‘yan ƙalilan a cikin waɗanda ba su samu damar halartar taron ba.
An ɗauki tsawon awa ɗaya ana rafka nishaɗi kawai.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Kwamared Ahmad Jibril (wakilin gwamna), Kwamared Gambo Ibrahim Gujungu, Salisu Muhammad Officer, Adam A. Zango, Lawal Ahmad, Sadiq Ahmad, Bello Muhammad Bello, Hamza Talle Maifata, Haruna Talle Maifata, Adamu Hassan Nagudu, Nazifi Asnanic, Abubakar Sani, Sadiq Sani Sadiq da Auta Waziri.
Akwai kuma Ado Gwanja, Ibrahim Ibrahim, Sani Sabo Kwarko, Ɗanmusa Gombe, Ahmad Shanawa, Abdu Boda, Tahir I. Tahir, Aliyu Nata, Isah Bawa Doro, Kabir Sa’idu Bahaushe, Al-Amin Dagash, Rabi’u Na’auwa, Halima Atete, Jamila Nagudu, Fati Muhammad, Fati Shu’uma, Teema Yola, A’isha Najamu, Rakiya Moussa Poussi, Sadiya Kabala, Momee Gombe, Hauwa Waraka, Maryam Aliyu (Madam Korede), da sauran su.
Shugabannin ƙasa na wannan ƙungiya da aka ƙaddamar su ne: Abdul Muhammad Amart – Ciyaman; Abdullahi Abbas – Vice-Chairman, North-west; Adamu A.D. – Vice Chairman, North-east; Bala Mu’azu Kufaina – Vice-Chairman, North-central; Salisu Muhammad – Secretary General.
Sauran su ne: Sadiq Mafiya – Assistant Secrtary General; Halima Atete – Treasurer; Sani Yarima – Financial Secretary; Fatima Adamu Assistant Financial Secretary; Bello Muhammad Bello – Publicity Secretary; Tahir I. Tahir – Organising Secretary; Jamila Niger – Welfare Officer, da Nazifi Asnanic – Auditor.
Jakadun ƙungiyar kuma su ne: Ali Nuhu, Adam A. Zango, Ibrahim Ibrahim, Ado Gwanja, Musa Maisana’a, Baba Ari, Lawan Ahmad, Ɗan’auta, Auta Waziri, Ɗanmusa Gombe, Teema Yola, Fati Shu’uma, Maryam Yahaya, Momee Gombe da A’isha Najamu.
Shi dai Abdul Amart, tun a shekarar 2015 ya fara haɗa mawaƙan industiri don su yi waƙar siyasa, inda ya fara da waƙar ‘Lema Ta Yage’. An yi waƙoƙi da dama bayan ita, har aka zo kan ‘Sakamakon Canji’ a 2019.

A yau ya na ɗaya daga cikin mutanen da ke motsa Kannywood, domin lokaci zuwa lokaci ya kan shirya abubuwan da jama’a za su ƙaru kasancewar a yanzu masana’antar ta na cikin garari. Amma da ire-iren waɗannan abubuwa da ya ke yi, ya na taimakon abokan sana’ar sa ta hanyar ya je ya samo, ya ƙirƙiri abin da kowa zai amfana.
Ta haka shi ma ya samu damar da ya ke raba kyautar motocin hawa ga abokan sana’ar sa sama da mutum goma, ban da kayan abinci da kuɗaɗe da ya ke rabawa.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com