DUKKAN abin da aka saka wa rana, komi tsawon lokacin, sai ya zo. Allah cikin ikon sa, fitaccen furodusa kuma jarumi a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, Abdullahi Abbas (Ubangari), shi ma ya ƙara shiga sahun masu iyali, bayan zaman gwauranci da ya yi na kusan shekara ɗaya.
A ranar Asabar, 25 ga Satumba, 2021 aka ɗaura auren sa da santaleliyar amaryar sa, Zulaihat Ishaq Abdulrasheed.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:15 na rana a masallacin Adarawa da ke Layin Maidubun Tsumma, Jantiti, Rigasa, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.


‘Yan fim da dama, musamman na Kaduna, sun halarci ɗaurin auren. Daga cikin su akwai Abdul Amart, Sadiq Mafiya, Malam Musa Muhammad Abdullahi, Malam Maiwada Gwanki, Malam Carki, Ɗayyab Maiɗa’a, Najib Marubuci, Abdullahi Abu Uku, da Sufi Nakowa.


Kafin ranar ɗaurin auren an gudanar da shagulgula inda ranar Laraba aka yi Ranar Ƙauyawa; ranar Alhamis aka yi bikin Ranar Fulani, sai Juma’a kuma aka yi wasan ƙwallon ƙafa da kuma dina.


‘Yan fim da su ka halarci dina sun haɗa da Abdul Amart, Al-Amin Ciroma da matar sa Wasila Isma’il, Tahir I. Tahir, Sadiq Sani Sadiq, Jamilu Adamu Kochila, Wassh Waziri Hong, Usman Ɗan Matashin Dattijo, Abdul M. Shareef, Sadiq Mafiya Halima Atete, da sauran su.
Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.
Comments 1