WAJEN shekara bakwai kenan ba a ji fitaccen mawaƙi Alhaji Adamu Hassan Nagudu ya fito da sabon kundin waƙoƙin sa ba. Kwatsam, a makon jiya sai ga shi ya yi wa masoyan sa albishir da cewa su shirya ganin sabon album a ƙarshen shekarar da mu ke ciki ta 2021.
Nagudu, wanda shi ne Sarkin Mawaƙan Sarkin Borgu, sanannen jarumi ne a a Kannywood wanda ya fito a finafinai da dama. Ya shafe shekara kusan ashirin ana damawa da shi a masana’antar, inda ya ciri tuta da daɗaɗan waƙoƙi, masu ma’ana, waɗanda ke jefa duk mai sauraro cikin kogin tunani. A dalilin haka, ya samu ɗaukaka da farin jini irin waɗanda ba su misaltuwa.
Wani abu da yawancin mutane ba su sani ba shi ne mawaƙin ya ɗauki hutun yin album ɗin waƙoƙin sa kimanin shekara bakwai da ta gabata, wato tun bayan da ya saki wani album mai suna ‘Ɗan Saurayi’. Daga nan ne aka ji shi shiru a ɓangaren fitar da album, sai dai lokaci zuwa lokaci ya kan saki ɗaiɗaikun waƙoƙin sa a YouTube.
Mujallar Fim ta tattauna da Adamu Nagudu kan wannan sabon albishir da ya yi wa masoyan sa, kamar haka:
FIM: Tsawon shekaru kusan bakwai zuwa takwas masoyan ka na ci gaba da dakon ganin kundin waƙoƙin ka. Menene ya janyo wannan tsaikon na fitowar album ɗin?
ADAMU NAGUDU: Saɓanin yanayin canjin lokaci da kuma zamani shi kan sa da kuma kasuwar tamu gaba ɗaya da kowa ya san idan ka na da buƙatar album ka kan je kasuwa ne ka saya, kuma duk wani mawaƙi da ya taso idan ka na son sayen kaset ɗin sa sai ka je kasuwa, to a zamanin yanzu shekaru wajen goma da su ka shuɗe kasuwar kaset a yanzu ta na neman ɓata ko kuma in ce ta ma ɓata saboda shigowar kafafen sada zumunta da sauran abubuwa na cigaba.
Ni yanzu rabo na da na yi album mai sunan album tun album ɗi na na ‘Riƙe Gwanin Ka’ ko in ce album ɗi na na ‘Ɗan Saurayi’. Shekaru kusan takwas kenan rabo na da album, saboda yanzu kasuwar ta koma sai dai yanzu ka yi waƙa ita kaɗai ka ɗora ta a shafin YouTube ko kuma wani shafin ka na Intanet da ka ke da shi ko ma wani afilikeshin ɗin ka da masoya za su iya samu. To amma dai ana yin kaset ɗin kaɗan ne, mu ke yi.
FIM: Yanzu ya batun yin sabon album, ko za a ci gaba da tafiya a haka ne?
ADAMU NAGUDU: A’a, domin kuwa zan yi album kala biyu – na bidiyo da na murya. Na shirya kuma zan buga faifan sidi ko da ba yawa yadda mutanen da ba sa amfani da soshiyal midiya, domin kuwa akwai waɗanda har yanzu ba sa amafani da irin wannan kafafen sada zumunta, sidi kawai su ka sani, da sauran su.

FIM: Ka faɗi cewa za ka yi album amma ba ka faɗi sunan sa ba.
ADAMU NAGUDU: To sunan dai album ɗin ‘Lokaci’.
FIM: Me ka kalla ka sa wa wannan album naka ‘Lokaci’?
ADAMU NAGUDU: Alhamdu lillah! Na zauna na yi duba da dogon tunani a kan wannan suna. Wani nazari na yi a kan shi kan sa lokacin. Kalma ce wacce ta ke da matuƙar girma. Idan ka kalli lokaci, a kan sa kowa ke tafiya. Ita kan ta duniyar a kan lokaci ta ke tafiya. Shi kan sa ɗan’adam da ya ke rayuwa a cikin ta da duk wata dabba da ta ke ciki a kan lokaci mu ke tafiya.
Sai na ga to tunda komai lokaci ne, ita kan ta ɗaukakar ta na da lokacin ta. To shi ya sa na ce bari na yi waƙa a kan lokaci, kuma shi ya sa na sa wa album ɗin su na ‘Lokaci’, saboda akwai waƙoƙi da su ka danganci shi kan sa lokacin. Wannan shi ne dalilin da ya sa na sa wa shi kan sa album ɗin ‘Lokaci’.
FIM: Waƙoƙi nawa kundin ya ƙunsa?
ADAMU NAGUDU: Ya ƙunshi waƙoƙi kamar goma sha uku zuwa sha huɗu.

FIM: Zuwa yaushe ake sa ran wannan album zai fito?
ADAMU NAGUDU: Da dai mu na so mu sake shi ne a sabuwar shekara, gaskiyar magana kuma yanzu mun gama odiyo ɗin kuma mu na so mu sake shi tare da bidiyo. To sai dai ya kasance sabuwar shekara da za mu shiga za mu saki odiyo da bidiyo, to amma dai in-sha Allahu za mu fara sakin odiyon da ɗai-ɗai ɗin kamar waƙa ita kaɗai a wata mai kamawa a YouTube canal mai suna Adamu Hassan Nagudu, da afilikeshin ɗin mu da yanzu mu ke kan aikin sa. Za mu bayyana wa mutane sunan sa da dai sauran gurare da masoya za su iya zuwa su samu waƙoƙin mu in-sha Allahu, kafin kuma mu fitar da album ɗin gaba ɗaya zuwa sabuwar shekara.
FIM: Duk da cewa ka ɗauki tsawon lokaci har shekara bakwai ba tare da ka fitar da album ba, sai ga shi kwatsam yanzu za a fitar da ‘Lokaci’. Ba ka ganin hakan ya na yi wa masoyan ka ciwo na ba sa samun album ɗin ka a kai a kai?
ADAMU NAGUDU: E, gaskiya masoya na sai dai in ce su yi haƙuri. Haƙiƙa mu na samun irin wannan kiraye-kiraye, to ba komai ba ne ni da man duk wanda ya san ni tun daga lokacin da na fara waƙa ban fiya sakin album a kai a kai ba; zan iya yin album ya kai shekara biyu, uku, huɗu har ma biyar kan na yi sabo. Yanzu kuma sai na tadda ita kan ta kasuwar ta na buƙatar nutsuwa; tsarin kasuwanci ya canza, saboda haka sai ka bi abin a hankali kafin ka samu biyan buƙatar da ka ke nema. To wannan dai sai dai mu ce masoya su yi haƙuri da yadda za mu dinga kawo musu al’amuran namu sannu a hankali kafin komai ya warware da kasuwancin duniyar ma gaba ɗaya.
FIM: Kowane mawaƙi idan ya yi sabon kundi ya na da fata a kan sa. Ko Adamu Hassan Nagudu ya na da fata a kan wannan album?
ADAMU NAGUDU: Gaskiya ina da fata a kan wannan album nawa. Babban fata na a kan sa shi ne yayin da masoya na su ka ji waɗannan waƙoƙi da na rera ba zan ce ban taɓa yin irin su ba, amma dai na daɗe ban yi irin su ba, waƙoƙi ne waɗanda akwai faɗakarwa a ciki, akwai nuni a kan sa shi lokaci, akwai nuni a kan ɗaukaka, akwai nuni a kan zamantakewa, akwai kuma nuni a kan mu’amala a kan ɗaukaka idan ta same ka, akwai kuma nuni a kan ɗaukaka idan ya sauka da yadda za ka gudanar da rayuwar ka a cikin al’umma. A dai jira fitowar sa domin a ji me ke ƙunshe da shi domin su da kan su za su san cewa shirin ba bacci ba ne, ja da baya ba tsoro ba ne, shirin tafiya ne!

FIM: Wane albishir ka ke da shi ga masoyan ka?
ADAMU NAGUDU: Ina albishir ga masoya na masu bin waƙoƙi na na kallo da na ji, kamar yadda na daɗe ban fitar da odiyo da na kallo ba, to su gyara zama su buɗe idon su, za su ga wasu abubuwa na ban-al’ajabi da hirar da ba su taɓa gani ba, zan wanke musu zuciyar su na shekaru bakwai ko takwas da ba su ji ni ba.
Sannan kuma abin da zan gaya wa masoya na da ma ‘yan’uwa na na sana’ar fim da waƙa, farko dai shi ne duk mutumin da ya riƙe gaskiya, to in-sha Allahu gaskiyar nan za ta kai shi ga gaci da inda ka ke buƙatar zuwa.
Masoyan mu kar su gaji da ba mu shawara da kuma addu’o’i da kuma nuni a kan wani abu; in mun yi kuskure a tunasar da mu domin shi kan sa addini ma ai nasiha ne kamar yadda Manzon Allah s.a.w. ya faɗa. Saboda haka kar su gaji da da wannan shawarwarin da su ke ba mu da saƙo kan wani abu in mun yi da ya saɓa wa al’adu ko ya saɓa wa shari’a da al’ada domin ɗora mu a kan daidai kan abin da mu ke.
Al’ummar gari kuwa su dinga yi mana kyakkyawan zato, su dinga kallon mu a matsayin wato mutane kuma ‘ya’ya waɗanda su ke neman na kan su, wanda su ke neman halal kuma su ke ci da halalin su.

FIM: Mun gode da wannan lokaci da aka ba mu.
ADAMU NAGUDU: Na gode ni ma ƙwarai da gaske.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com