A RANAR Alhamis, 12 ga Satumba, 2019 aka yi bikin buɗe kamfanin Sa’a Global Multimedia, mallakin Salisu Abubakar, wanda aka fi sani da Salisu Arabi.
Arabi ya na ɗaya daga cikin masu rubuta ƙagaggun labarai da kuma waƙoƙi iri daban-daban, sannan memba ne a ƙungiyar gamayyar mawaƙan gwamnan Katsina mai suna Masari Modern Singers Association.
Haka zalika jigo ne a kwamitin shirya taron Ranar Mawaƙan Hausa wanda aka riƙa yi a shekarun baya.
A lokacin da ya ke yi wa manema labarai jawabi game da maƙasudin buɗe kamfanin, Salisu Arabi ya ce, “Ra’ayi na shi ne ina yin waƙoƙi da rubutun labarai, sai na fahimci akwai matasan mu da ke tasowa masu ƙwaƙwalwa amma ba su da majingina.
“Sai na yi tunanin idan na buɗe kamfani zai iya taimakon matasa domin su samu aikin yi. Wasu ba su yi karatun zamani ba, wasu kuma ba su yi karatun allo ba, amma a kamfanin za mu riƙa ba su horo na musamman wanda a yanzu haka mu na da aƙalla ma’aikata goma sha ɗaya waɗanda za su riƙa aiki a ƙarƙashin kamfanin; wasu na da iyali, sannan kuma su na waƙoƙin biki, siyasa, sarauta da sauran su. Duk mun jawo su mun ba su aikin yi domin dogaro da kan su.”

Taron ya samu halartar wasu daga cikin mawaƙan Hausa, ‘yan fim da marubuta na Jihar Katsina.
Kaɗan daga cikin waɗanda su ka halarci hidimar bikin buɗe kamfanin sun haɗa da Mansur Ya’u (Alhaji Babba), Ja’afar Usman Dattijo, Isah Randawa, Aliyu Nata, DJ Imran, Salisu Hafijo, Kosan Waƙa da Usman Na Manzon Allah.