• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Abin da ya sa ‘yan Kannywood ba su shiga bikin fim na Kaduna’

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 30, 2020
in Labarai
0
Wasu daga cikin masu halartar bikin ta hanyar manhajar Zoom

Wasu daga cikin masu halartar bikin ta hanyar manhajar Zoom

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MASU shirya Bikin Duniya kan Finafinai na Kaduna (‘Kaduna International Film Festival’) sun bayyana dalilin da ya sa ‘yan fim ɗin Hausa ba su halartar taron bikin.
 
Mun dai kawo maku labarin an fara gudanar da bikin baje kolin finafinai karo na uku a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2020. A ciki, mun faɗa maku cewa a wannan karon ta intanet aka gudanar da bikin.
 
To, Allah cikin ikon sa, ya bada damar gudanar da bikin cikin natsuwa da kwanciyar hankali, akasin yadda wasu da farko wasu na tunanin ta su ka ce za a gudanar da bikin ta intanet har a samu abin da ake so.
 
Bikin dai an kammala shi kamar yadda aka tsara shi a jadawalin da mu ka kawo maku a cikin labarin sanar da fara gudanar da bikin. 
 
Da farko da misalin ƙarfe 9:00 na safe an gabatar da buɗe bikin da taken Nijeriya, sai kuma Fr. Chimaobi Ohaji ya buɗe taron da addu’ar Kiristoci. Bayan ya gama sai Abayomi Muhammad ya yi addu’ar Musulunci don buɗe taron.
 
Shugaban bikin, Mista Israel Kashim Audu, ya yi jawabin maraba ga waɗanda su ka samu halartar bikin buɗe taron na tsawon minti 15. Haka kuma tsohon Sanatan mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya yi jawabin minti 10, sai kuma Honarabul Chinyere Emmanuel Igwe ya yi jawabin buɗe taron. 
 
Daga nan kuma sai ya gabatatar da maƙala game da yadda za a samu cigaba da raya samuwar zaman lafiya ta hanyar nishaɗantarwa, na tsawon minti 30. Dakta Betta Edu (Kwamishinan Lafiya na Jihar Rivers), ya yi jawabin saƙon fatan alheri na minti 10. Daga shi sai Alhaji Adedayo Thomas, shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), ya yi nasa jawabin. Sai kuma Fred Amata, wato shugaban Ƙungiyar Daraktoci na Nijeriya, ya yi nasa jawabin. 
 
An gama jawaban da misalin ƙarfe 11:00 na safe. 
Daga nan aka ci gaba da gudanar da bikin kamar yadda aka tsara, kuma kusan dukkan waɗanda aka gayyata sun samu halarta, ba kamar yadda wasu ke tunanin abin ba zai yiwu ba. 
 
An gudanar da tattaunawa da dama kan yadda za a zai ciyar da harkar fim gaba a ƙasa baki ɗaya.
 
Tattaunawar kuma a kullum akan gudanar da ita sau uku zuwa huɗu a kowace rana. 
 
An ɗauki tsawon kwana biyar ana gabatar da bikin.
 
A ƙarshen bikin, mujallar Fim ta tambayi shugaban bikin, Israel Kashim Audu, yadda bikin ya gudana, musamman ganin ta intanet aka yi.
 
Sai ya ce: “Ina yi wa Allah godiya da ya ba mu dama mu ka gabatar da bikin cikin nasara. Ka san mun yi bikin ne a intanet, mun yi amfani da Zoom da Instagram. Komai da mu ka yi, mun yi amfani da data ne da sauran su na tsawon kwanaki biyar da mu ka yi.
 
“Kuma cikin yardar Allah duk mutanen da mu ka gayyata sun samu halarta har na tsawon kwanakin da mu ka yi, kuma sun ba mu haɗin kai sosai. Akwai irin su Zack Orji, Kunle Afolayan, Rabi’u Rikadawa, Wassh Waziri Hong, duk sun samu halartar tattaunawar ɓangarori da aka gudanar. 
 
“Kuma Honarabul Chinyere ne ya buɗe biki daga Jihar Rivers. Haka kuma Kwamared Shehu Sani ya bada keynote address.”
 
Game da matsayar da aka samu a kan bikin, Mista Audu ya ce, “Gaskiya an samu matsaya mai ƙarfi, tunda ga shi mun gabatar da bikin lafiya. Kuma ina iya cewa bikin wannan karon ya fi duk na baya da aka yi armashi. 
 
“Wannan shekarar saboda COVID-19 ya sa mu ka yi a intanet, amma mu na duba yadda za ta kasance shekara mai zuwa; za mu duba yiwuwar cigaba da gudanar da taron yadda mu ke yi a baya, a karo na 4 kenan.”
 
Mujallar Fim tambaye shi abin da ya sa ‘yan Kannywood ba su taka rawa a cikin bikin ba, sai ‘yan tsiraru. Sai ya amsa da cewa, “Na farko zan ce gaskiya mun yaɗa a ko’ina, kuma ni da kai na na kira da dama daga cikin su, ba su bada wani ƙwaƙƙwaran goyon baya ba. 
 
“Amma ina iya cewa saboda ba su saba da irin wannan abin ba ne a Arewa, ni a gani na. Ka san wannan shi ne biki na farko da aka fara gabatarwa a nan Arewa. Ana yi a Kano, amma wannan ‘international’ ne.
 
“Kuma yawancin su ba za su san muhimmancin wannan biki ba, ko an neme su za su ga cewa ba lallai ba ne su bada goyon baya. Amma kuma na san cewa a sannu za su fara ganewa. 
 
“Ka ga ‘yan Nollywood sun yi nisa, sun san muhummancin Film Festival. Shi ya sa ka ga su su ka fi yawa wurin halartar bikin. 
 
“Mu na iyakacin bakin ƙoƙarin mu don ganin cewa mun sako ‘yan Kannywood a ciki. Mutum uku ne kaɗai su ka gabatar mana da finafinan su, kuma ba za mu ba mutum awad bai gabatar mana da fim ɗin sa ba. Ko Hadiza Gabon da mu ka ba, mun yi duba ne ga irin ‘achievement’ ɗin da mutum ya samu ne, shi ya sa a Kannywood mu ka zaɓe ta, a Nollywood kuma mu ka ɗauki Zack Orji.
 
“Sannan abin da zan ce game da wannan biki shi ne, gaskiya akwai cigaba a cikin lamarin, tunda har a cikin wannan lokacin na batun annobar COVID-19 mun gabatar da bikin. Wannan babban cigaba ne. 
 
“Kuma duk wanda ya ji sunan Kaduna zai ɗauka gwamnatin Jihar Kaduna ke gudanar da bikin. Yanzu haka na gama ganawa da da ‘Kaduna State Ministry of Rural Services’. Wannan wani cigaba ne na ciyar da harkar gaba. 
 
“A nan Nijeriya akwai ‘yan ƙasar waje da su ka halarci bikin. Kuma daga UK, Uganda da sauran su sun halarci bikin. Kuma wasu sun samu awad a cikin su. 
 
“Kenan wannan bikin ya yi nisa. Kuma bikin wannan karon, zan iya cewa ya fi duk wani Festival da aka yi a Nijeriya.”  
 
A nan ƙasa ga jerin sunayen waɗanda aka ba kyaututtikan karrawa a bikin:
Zack Orji (a hagu) da Kwamared Shehu Sani a lokacin taron
1. BEST ACTOR – RITA DOMINIC IN THE MOVIE ‘LIGHT IN THE DARK’
 
2. BEST SCREENPLAY – ‘GHETTO BLUES’ BY JOHN CHUKA
 
3. BEST DIRECTOR – EKENE MEKWUNYE IN ‘THE MOVIE LIGHT IN THE DARK’
 
4. BEST INDIGENOUS FILM – ‘TUNTUƁE’ BY AHMED BELLO 
 
5. BEST SHORT FILM – ‘HIDING PLACE’ BY PRINCE DANIEL
 
6. BEST DOCUMENTARY – ‘GUTTED: THE FIGHT OF KALK BAY’ BY ANGELO LOUW  
 
7. BEST CINEMATOGRAPHY – JOHNPAUL NWANGANGA (DGN) IN THE MOVIE ‘TWILIGHT’
 
8. BEST INTERNATIONAL ACT – ZAKARIYA IN THE MOVIE ‘SUDANI’ FROM NIGERIA
 
9. BEST EXPERIMENTAL FILM – ‘BARBARA’ BY LULIIA PEREVERZEVA
 
10. BEST SUPPORTING ACTOR – LINDA OSIFO IN THE MOVIE ‘COMPLICATED LIES’
 
11. BEST MAKE-UP – OLAMIDE ODUYOMI IN THE MOVIE ‘ALUBARIKA’ 
 
12. BEST FEATURED FILM – ‘DRAWING STRENGTH’ BY DIMBO ATIYA
 
13. BEST STUDENT FILM – ‘KEN AND THE RABBIT’ BY GEOFREY KING
 
14. BEST FAST RISING ACTOR – LILIAN EJIRO IN THE MOVIE ‘BROKEN WATERS’
 
15. GOLDEN JURY AWARD – JOKE SILVA IN THE MOVIE ‘LIGHT IN THE DARK’
 
KADIFF2020 ACHIEVERS AWARDS
 
1. Her Excellency Dr. Mrs Olufolake Abdulrazaq (First Lady, Kwara state)
 
2. Hajiya Hafsat Mohammed Baba (Kaduna State Commissioner for Human Services and Social Development)
 
3. Alh. Adedayo Thomas (Executive Director, NFVCB) 
 
4. ZACK ORJI (Veteran Nollywood actor)
 
5. HADIZA GABON (Kannywood star)
 
6. HON. CHINYERE EMMANUEL IGWE (REPRESENTING PORT HARCOURT 2 FEDERAL CONSTITUENCY)
 
7. DCP Frank Mba (P.R.O., Nigerian Police Force)
 
8. Her Excellency, Catriona Liang CB (British High Commissioner, Nigeria)
 
9. Sen. Shehu Sani

Loading

Previous Post

Cutar daji ta kashe jarumin ‘Black Panther’, Chadwick Boseman

Next Post

Abin da ya sa Kannywood ta zama kaico – Salisu Officer

Related Posts

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Next Post
Malam Salisu Muhammad Officer ya ce ba Kano ce kaɗai Kannywood ba

Abin da ya sa Kannywood ta zama kaico - Salisu Officer

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!