SHUGABAN Ƙungiyar Jarumai ta Ƙasa, Malam Alhassan Kwalle, ya rabauta da muƙamin siyasa a Ƙaramar Hukumar su ta Ungogo da ke Jihar Kano.
A makon da ya gabata, Shugaban Ƙaramar Hukumar ya naɗa shi a matsayin Kansila marar gafaka, irin wanda ake wa lakabi da ‘Kansilan komai da ruwan ka’.
Alhassan Kwalle tsohon ɗan fim ne da aka daɗe ana damawa da shi a Kannywood, kuma yana ɗaya daga cikin ‘yan fim da suka goyi bayan kafa gwamnatin Abba Kabir Yusuf a zaɓen bara.