A RANAR Talata, 25 ga Afrilu, 2023 Allah ya yi wa babban malamin addinin Muslunci da ke garin Azare, Jihar Bauchi, Malam Barde Muhammad, rasuwa. Shi ne mahaifin babban furodusan Kannywood Alhaji Habibu Barde Muhammad.
Marigayin, mai shekaru 96 a duniya, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya in inda aka kwantar da shi a babban asibitin Federal Medical Centre da ke Azare na tsawon lokaci kafin a sallame shi ya koma gida in da kuma daga baya Allah ya yi masa cikawa a gidan sa.
Malam Barde fitaccen malami ne wanda ya shafe tsawon rayuwar sa ya na koyar da Ƙur’ani da sauran littattafan Muslunci.
Ɗan sa, Alhaji Habibu, shi ne furodusan fim ɗin ‘Nihla’ kuma Mataimakin Shugaban ƙungiyar MOPPAN na yankin arewa-ta-tsakiya. Shi ne na uku a cikin ‘ya’yan sa guda 34.
Tuni dai Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya aika da saƙon ta’aziyyar sa kamar yadda Kakakin kungiyar Al-Amin Ciroma ya wallafa.
Ciroma ya ce a takardar ta’aziyya da Sarari ya aika wa Habibu Barde, ya bayyana rashin a matsayin babbar jarrabawa ce, kuma ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomar sa, sannan ya kyautata bayan sa.
Ita ma Majalisar Ƙoli ta Dattawan Kannywood, ta hannun Sakataren ta Malam Kabiru Muhammad Maikaba ta bayyana ta’aziyyar ta tare da alhini. Ƙungiyar ta ce: “Wannan majalisa na taya ɗan’uwa Alhaji Habibu Barde Muhammad da sauran ‘yan’uwa jimamin wannan babban rashin da aka yi. Mu na taya ka tare da sauran ‘yan’uwa addu’ar Allah ya jiƙan Baba, Allah ya yafe masa kurakuran sa, ya sa Aljanna ce makoma. A madadin masana’antar Kannywood, wannan majalisa na tare da ku wajen yi wa Baba addu’a Allah ya kula da abin da ya bari. Ku kuma Allah ya ba da ladar haƙuri.”