• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An fara rukunin ‘C’ na shirin N-Power tare da matakan da matasa za su bi

by DAGA WAKILIN MU
March 12, 2021
in Nijeriya
1
An fara rukunin ‘C’ na shirin N-Power tare da matakan da matasa za su bi
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta kawo ƙarshen dogon jiran da ake yi na fara aiwatar da rukuni na uku (Batch C) na shirin N-Power wanda za a shigar cikin jerin shirye-shiryen rage matsin rayuwa, wato ‘National Social Investment Programmes’ (NSIPs).


Mai bada shawara kan aikin jarida ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Madam Nneka Ikem, ita ce ta bayyana haka a ranar Alhamis cikin wani saƙo da ta tura a Twitter. 


A cewar ta, ana kira ga dukkan waɗanda su ka cike takardun nema shiga shirin da su ci gaba da sauraren bayanai kan tantancewar su. 


Ta rubuta cewa: “Labari da ɗumi-ɗumi! Za a ƙaddamar da @npower_ng rukuni na C a yau a manhajar @NSIP_NG wato NASIMS.

 
“Masu neman shiga #BatchC su ci gaba da duban fitowar bayanai kan tantancewar su. @nairaland @NigerianYouthC2 @Npower_Reps”. 

Idan an tuna, kimanin matasan Nijeriya miliyan biyar ne su ka rubuta takardar neman shiga shirin N-Power a cikin 2020. Rajistar shiga kashin farko na shirin an fara ta ne a ranar 26 ga Yuni, 2020, kuma manufar shirin shi ne a sama wa matasa 500,000 aikin yi.


 A cewar minista Sadiya Umar Farouq, ana so ne a sama wa matasa damarmaki da za su ƙware ta yadda za a iya ɗaukar su aiki ta hanyar ba su dabarun yin sana’a.


Tun ba a je da nisa ba, a yau ne ma’aikatar ta bada sanarwar cewa duk wanda ya cike buƙatar shirin na N-Power ya shiga mataki na gaba na rukunin ‘C’ kamar yadda aka ce za a sanar. 


Saboda haka a sanarwar da Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura Alkali, ya bayar a yau, ma’aikatar ta yi kira ga dukkan waɗanda su ka nemi shiga cikin rukunin da su gaggauta bin waɗannan matakan ba tare da ɓata lokaci ba:

1. Su duba imel ɗin su da su ka bayar lokacin neman shiga shirin domin ganin matakan da za su bi su shiga gidan yanar shirin.


2. Su shiga www.nasims.gov.ng domin shiga gidan yanar masu neman a ɗauke su a shirin saboda su bada ƙarin bayanan da ake nema game da su.


3. Su bi umarnin da aka jera a gidan yanar tare da yin jarabawar intanet da aka tsara a wajen.

Previous Post

Iyan-Tama: Har yanzu da ni ake damawa a Kannywood

Next Post

Na sha gamuwa da masu sha’awa ta – Nafisa Salisu, jarumar ‘Macen Sirri’

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Na sha gamuwa da masu sha’awa ta – Nafisa Salisu, jarumar ‘Macen Sirri’

Na sha gamuwa da masu sha’awa ta - Nafisa Salisu, jarumar 'Macen Sirri'

Comments 1

  1. Usman shuaibu says:
    4 years ago

    Usmanshuaibuadamu19@yahoo.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!