• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗandugaji: Yadda mu ka assasa masana’antar Kannywood

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
November 9, 2020
in Tattaunawa
0
Alhaji Tukur S. Tukur (Ɗandugaji)

Alhaji Tukur S. Tukur (Ɗandugaji)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TUKUR S. TUKUR (Ɗandugaji) ya na cikin zubi na biyu na ‘yan fim ɗin Hausa, wanda su ne su ka assasa harkar da daga baya ta rikiɗe ta zama masana’antar Kannywood. Su ne su ka biyo bayan ajin farko na ‘yan wasan dirama, wato irin su Ɗanhaki, Karo-Da-Goma da Ƙasimu Yero. Tun kafin shigowar su Ali Nuhu kenan.

Ɗandugaji, wanda ya yi fice a finafinan bidiyo na farko a matsayin ɗan wasan barkwanci, ya daɗe daga ɓacewa daga akwatunan talbijin ɗin mu. Mutanen da su ka san shi sun sha tambayar wai ya na ina ne. Wasu kuma sun manta da shi, kai wasu ma ba su san shi ba.

Mujallar Fim ta gano cewa Ɗandugaji dai ya na nan da ran sa, kuma lafiyar sa ƙalau. Hasali ma dai, rayuwa ta yi albarka, domin kuwa babban jami’i ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a birnin Kano. 

Shahararren jarumin ya yi tattaunawar musamman da mujallar Fim inda ya bada labarin rawar da ya taka wajen kafa masana’antar Kannywood. Ya kuma faɗi matsalolin harkar da dalilin da ya jawo wa ‘yan fim farin jini da baƙin jini a wajen jama’a. Haka kuma ya ce bai bar harkar fim ba, a’a harkar ce ta guje shi. “Ko yau aka gayyace ni fim, in dai ba zai zubar da mutunci na da ƙima ta ba, zan amsa, kuma na ga ina da wani abu da zan taka rawa in bada gudunmawa ta,” inji shi. 

Ga yadda hirar ta Alhaji Tukur Ɗandugaji da MUHAMMAD LAWAN RANO ta kasance:

FIM: Mai karatu zai son jin da wa mu ke tare?

ƊANDUGAJI: To, ni dai suna na Tukur S. Tukur wanda kuma duniya ta fi sani na da Ɗandugaji. Don kuma a faɗaɗa sani, bari in faɗi dogayen sunan, wato Bazallahi Najasi, Albagadazi Abu Ali Abdussamadul Muhammadul Tajul Arafina na Abulwafa Kakisu Malam Ɗandugaji, wato Ɗandugaji Nakowa!

FIM: Ko za ka tunatar da mu taƙaitaccen tarihin ka? 

ƊANDUGAJI: To, tarihin rayuwa ta dai ya fara ne daga cikin shekarar ta 1971, ranar 18 ga watan Afirilu, ranar Lahadi da aka haife ni a unguwar Chiranci da ke cikin birnin Kano kusa da gidan Sarki.

 Na yi firamare ta Ƙofar Na’isa daga 1977 zuwa 1983, na kuma samu damar zuwa sakandire ta Gwale a shekarar 1983 zuwa 1984, saboda kuma cinkoso da aka samu na ɗalibai ya sa aka yi mana canji zuwa ƙaramar sakandire ta Goron Dutse wacce da a cikin FCE Kano ta ke amma yanzu ba ta cikin ta. Na kuma kammala ta a shekarar 1986 inda kuma mu ka yi jarrabawar ‘6-3-3-4 system’ da kuma jarrabawar shiga Makarantar Kimiyya da Fasaha, inda kuma na samu nasarar shiga Makarantar Wudil Technical a shekara ta 1986 zuwa da 1987, kuma na karanci ɓangaren lantarki a wannan makaranta ta Wudil zuwa shekara 1989, inda na kammala. Sannan kuma na samu damar zana jarrabawar shiga Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Bauchi, wato Federal Polytechnic, Bauchi, inda kuma na karanci difiloma ta a kan dai ɓangaren wayarin, wato Electrical Engineering. Bayan na kammala a shekarar 1993 zuwa da huɗu, to a wannan shekara ne kuma abin da ya faru ya faru!

FIM: Ya aka yi aka tsinci ka a cikin harka fim? 

ƊANDUGAJI: Yayin da na gama makaaranta ina zaune a gida, akwai wani bawan Allah ana ce da shi Aminu Zubairu. Aboki na ne a unguwar Kwanar Ɗisu. Sai ya gabatar min da wata ƙungiyar wasan kwaikwayo, ai ya kamata kuwa in je. Saboda haka mu ka je. Sai kawai abin ya ba ni sha’awa, kuma na je na tarar akwai wani Auwalu Ɗankuki – Allah ya jiƙan sa, ya rasu – akwai kuma Ƙasimu wanda ya ke fitowa a ɗan Hankaka a yanzu kuma shi ne Kwamared A.A. Ayagi shugaban NGOs na ƙasa kenan, shi ne darakta na ɗaya, Ali Lawan Sagagi shi ne darakta na biyu a wannan ƙungiyar.

 To, ina zuwa dai aka gabatar da ni kuma su ka yi farin ciki, su ka ɗauke ni ɗan gida domin kuwa an gabatar da ni a matsayin ɗan gidan Malam Mustapha Muhammad (Ɗanhaki) wanda shi ma jarumi ne da ya yi zamanin sa a wannan lokacin. Kuma aka karɓen hannu biyu. Na ga kuma yadda su ke gwaji, wato ‘rehearsal’ a kan dan damali, wato ‘stage drama’. Kuma abin ya ban sha’awa. 

Washegari kuwa ina zuwa aka sa ni don ni ma in gwada. Kuma na gwada, abin ya burge mutane  aka yi dariya. To ka ji daga wannan lokaci na fara wasan kwaikwayo.

 Bayan kuma mu na wannan gwajin, tun kafin a fara haska mu a kyamara, sai aka fara gayyatar mu zuwa gidan biki da gidan suna; kamar yanda ake gayyatar DJ a yanzu, mu ma haka ake gayyatar mu mu yi wasa a gaban mutane a biya mu, har ta kai mun fara fita wasu ƙananan hukumomin mu yi wasa, in na kwana ne mu yi da safe mu yi kuma da daddare.

FIM: A lokacin da ku ke wannan wasa ana ɗaukar ku da kyamara ne ko kuma ku na yi ne ba ita?

ƊANDUGAJI: Ina! A wannan lokacin ba a fara harkar ‘home video’ ba. Wanda su ke harkar su ma ba harkar su ke ba, a gidan talabijin ne su ke na CTV. Su ne su Alhaji Ibrahim Mandawari da su ke yin wani fim mai suna ‘Jamila da Jamilu’, duk a gidan na talabijin kenan. 

 Cikakken kuma wanda su ka fara ‘home video’ su ne irin su Bala Hassan Babinlata da su ka fara da ‘Munkar’. Sannan kuma su Alhaji Ibrahim Mandawari su ka yi ‘Gimbiya Fatima’ a ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Tumbin Giwa. A kuma sa’annin mu, wanda mu ka fara daidai lokacin sai mu ka haɗu mu ka yi fim ɗin ‘Ɗandugaji’. A daidai lokacin kuma Sarauniya Films su ka fito su ka yi fim ɗin ‘Sartse’. 

 To waɗannan finafinan na ‘Ɗandugaji’ da ‘Sartse’ da ‘Sumbuƙa’ su ne su ka girmama su ka buɗe ‘home video’ a Jihar Kano.

FIM: Shi wannan suna na Ɗandugaji, ka samo shi ne a fim ko kuwa kafin ka fara harkar fim ka samo shi? 

ƊANDUGAJI: To lokacin bayan waccan ƙungiya da na ke ciki ta ruguje, mu ka buɗe wata mai suna Dabo Fim Production ƙarƙashin jagorancin shi dai Auwalu Ɗankuli da Sani Garba S.K. da wani Ashafa. Sai mu ka haɗu i mu i mu, mu ka harhaɗa kuɗi kuma mu ka yi gwaji, wato ‘rehearsal’, aka kuma fito da wani labarin ‘Sauna Jack’, kuma irin tsari da ya ke yin shirmen nan na sauna, to shi ne aka tafi da nufin za a yi fim mai suna ‘Sauna’ a garin Zakirai. To a kan hanya ne mu na tafiya sai kuma mu ka ga wani gari mai suna Zugaji, a kan hanyar mu ta zuwa Zakirai kenan, to bayan mun sauka, ni mu na cin abinci da wani aboki na mai suna Ashafa, Allah ya jiƙan sa, ya ke cewa wai ina ma laifin a maimakon saunan nan a sawa  fim ɗin suna ‘Ɗan Zugaji’? Sai na ce Zugaji ko Dugaji? Daga nan dai mu ka canza mai suna zuwa ‘Dugaji’, mu ka kuma ba wa daraktan mu mai suna Balarabe Tela shawara kuma ta karɓu, kawai mu ka maida fim ɗin ‘Ɗan Dugaji’ a take. Wanda kuma ni ne na ja ragamar fim ɗin, wato ni na fito a Ɗandugaji kuma ka ga sunan fim ɗin ‘Ɗan Dugaji’. Kuma ka ga a lokacin ina aikin koyarwa a makarantar sakandire da ke Gwale, sai na fara ganin mutane su na bi na da gudu su na, “Shi ne, shi ne Ɗandugaji!” Sai kawai na zama Ɗandugaji.

FIM: Ya gwagwarmayar ku da kyamara lokacin da aka fara sa ma ita da zummar ɗaukar ka?

ƊANDUGAJI: To gaskiya ai kamar mutum ne ya zauna ya yi babbaƙu ya yi farfaru, a tashi kuma za a yi takara a ce masa fara, ka ga ai ba shi da jin wani abu. Ai wannan gwajin da ka ke a gaban mutane wanda za su taru a kan ka, ga abokan ka da ‘yan yara sai kuma ku ke zuwa wajen jama’ar gari gidan biki gidan barka, mata su na kallon ku ku na yi a gaban su har ma ku ka fara barin garin ku ku na zuwa wani garin ku na yi ana kallon ku, to ka na zaton akwai wata kyamara ma da in an dasa ma za ka yi wani fari? Babu ita! Ai idon mutane shi ne kyamara tunda idon kyamara sama da dubu sun dasa ma ita wanda kuma tsoro za ka ji, ai kawai ana sa ma kyamara ji za ka yi an sauƙaƙa ma saboda abu ɗaya ne zai kalle ka. Saboda haka da mu ka zo sai mu ka yi shi cikin ƙwarewa. Sannan kuma a lokacin da son abin a cikin zuciyar mu yi mu ke da gaske, domin lokacin da na ke aktin ɗin ‘Ɗandugaji’ ji na na ke kamar wannan sakarai-sakaren, wawa-wawa, duk  dai ‘concept’ ɗin sa ne, wato mara ji, mai fitina, mai tsokana. To a daidai lokacin sai na zama haka; in dai ka ce min “Action!” to ka ji.

Ɗandugaji ya yi amanna da cewa shigo da rawa da waƙa a finafinan Hausa ne ya soma ɓata wa ‘yan fim suna a idon jama’a

FIM: A wancan lokacin na farkon fara fim, wasu sun fito su na zagin ku da aibata ku. Shin ya ka ke ji in hakan ta faru?

ƊANDUGAJI: In ka kula, mu a wancan lokacin daga yanayin tarbiyyar mu daga yanayin shigar mu na suturar da ake sawa daga lokacin ma’amalar mu da mutane. Duk da haka mun samu ƙalubale daga wajen mutane, ganin cuɗanya ɗanya da mata da ake. Amma ba a fara samun ƙorafi sosai ba sai da aka fara yin wannan rawa da waƙa a cikin fim, saboda haka wannan ita ta tsokano mutane su ka fara ɗan aibata ɗan fim. Amma don yanzu a zo a zauna a yi, da ma can ai iyayen mu sun yi dirama, kuma babu wanda ka ji ya na aibata su. Ga Malam Mamman ko ga Karo-Da-Goma ko ga a Kaduna irin su Ƙasimu Yero; ai da mata su ma su ke yi. To mu ma da mu ka zo mu ka fara yin irin namu, akwai diramar da za mu yi ga baki ɗaya mace ba ta fi guda biyu ba. Mu ma ba mu samu  illa ba, ba mu samu matsala ba. To amma da zarar da aka fara waƙa da raye-raye ta sako wannan waƙa da aka yi, to daga nan mu ka fara samun ƙalubale, ake ganin ‘yan fim kaza ne.

 To kuma wata waƙar ta na jan hankali ne, wata waƙar ta na da amfani, wata waƙar kuma kawai shirme ce, wata waƙar kuma in ka kalla ba ta dacewa ma da labarin fim ɗin. misalin waƙar da ta dace a fim a can ita ce duk wanda ya kalli ‘Sartse’, ya kalli aiki ya yi kyau tunda gida ya gyaru tsaf-tsaf. Ka ga ai wannan faɗakarwa su ka yi, kuma ta dace da labarin fim ɗin. 

Sannan kuma abin da ya ƙara jawo wa ‘yan fim ƙalubale shi ne ya alkinkata kan sa ya zama wani, wato mai ɓoye kan sa a wajen al’umma ya zama tsada ne da shi, sai a dinga ganin su a wata unguwan can su na taruwa ana zuwa ana ganin su, su na wani nuna su ne, wata kuma ta fito ta goya ‘yartsana ana yawo a Zoo Road ɗin nan. Ku yi hakuri ‘yan fim, amma abin da ya dinga faruwa kawai za a gan ka a talabijin ana ganin kuma kai daga sama ka ke kawai sai ka zo ka ballagazar da kan ka, ka fito a gefen titi ka na ciye-ciye ka na kaza, sai darajar ka ta zube. Amma ka ɓoye kan ka, wanda ma ganin ka sai an sha wahala kamar yadda mu ke.

FIM: Ya ka ke ganin irin cigaba da aka samu a masana’antar Kannywood a yanzu? 

ƊANDUGAJI: Gaskiya an samu cigaba kala biyu ta fannin aikin shirya fim, musamman aikin da ake na hannu irin su ɗaukar hoto, kyamara, kwalliya, rubuta labari, gurin shiryawa da sauran su. Da kuwa ai ba mu da wannan; mu ana yin abu ne ‘manual’, ka ga kuwa an samu cigaba.

 Kuma komai da amfanin sa da rashin amfanin sa.A da mun taɓa zuwa fim, a lokacin na ƙirƙiri labari kuma aka yi shi kamar fim ɗin ‘Ɗangaye’, wanda kuma ka ga a yanzu ba zai yiwu ba. A yanzu haka zan iya shirya ma fim ba tare da na rubuta ba, in ce a yi kaza a yi kaza. 

FIM: Ya ake shiga fim a wancan lokacin ko in ce hanyoyin da ake bi? 

ƊANDUGAJI: To gaskiya a da ba a bin hanyoyin nan dogaye idan mutum zai shiga fim. Kawai in ka na da wanda ka sani a harkar, kuma iyayen ka su ka yarda, to ba ka da matsala. Yanzu bari in ma misali da Ɗan’auta, ka ga da yaron gida na ne, ya na min ɗan ayyuka, kuma na ga ya nuna ya na son shiga harkar. Na ɗauke shi na haɗa shi da wani dan ce anashi a madadi na, lokacin aiki ya yi min yawa. Kuma shi a wannan lokacin ya na kwaikwayar marigayi Ibro ne, kuma fim ɗin da mu ka shirya mai na farko shi ne ‘Ɗan’autan Ibro’. Ka ga kuwa a lokacin nan ba sai ka kashe wani kuɗi ba ko ka san wani ba; kawai in ka na sha’awa zuwa za ka yi ka kai kan ka kuma da yardar iyaye.

FIM: Za ka iya tuna adadin finafinan ka daga farko zuwa yanzu?  

ƊANDUGAJI: A gaskiya ba zan iya tuna adadain finafinan da na yi ba, don kamar kai ne a tambaye ka mutanen da ka haɗu da su, ai ba za ka iya lissa fa su ba.

 Amma wanda na shirya nawa da kai na kuma na fito da kai na su ne guda huɗu; akwai ‘Alƙawari’, ‘Ɗangaye’ da kuma  ‘Ruwan Rayuwa’, akwai kuma ‘Sabo Turken Wawa’ amma kuma ɗaukar nauyin sa ba ni ba ne, wani  aboki na ne.

FIM: Wanne jarumi ne ya ya ke burge ka ko jaruma a Kannywood?

ƊANDUGAJI: Mu lokacin da mu ka yi yayin mu, jarumin da ya fi burge ni shi ne abokin karawa ta, Bashir Bala. A wancan lokacin kenan, saboda ko ana ɗaukar fim ya san abin da zai ce na san abin da zan ce saboda a da, ba a rubuta wani ‘script’, kawai dai cewa za a yi za mu ga gidan wane ana faɗa amma ba za a ce ma me za ka faɗa ba; ku ne wanda za ku shirya da kan ku, ba irin na yanzu da komai sai an gaya ma ba.

 Yanzu kuma masu burge ni a jarumai su ne kamar su Sadiq Sani Sadiq, Ali Nuhu da ma wannan Adamu Zango don su na ƙoƙari matuƙa. Masu shiryawa kuma akwai su Maishadda, Mu’azzam Idi Yari da Falalu A. Ɗorayi don ya fito da wani fim sai da na ji da ma ina ciki, wato fim ɗin nan mai dogon zango wanda tashar talabijin ta Arewa24 ke haskawa, wato ‘Gidan Badamasi’. Ɗan fim ɗin ya zo da wani salo na daban. Da kuma masu bada umarni irin su Aminu S. Bono da Ɗansmall, su na matuƙar ƙoƙari.Yauwa  akwai kuma Bosho don ya na matuƙar burge ni a cikin masu barkwanci, don shi kaɗai ne na ke sawa a gaba in kalla in ta dariya yadda na ke so kuma na kira shi na ce, “Ka na tsula tsiyar ka!”

FIM: Shin ko da yiwuwar Ɗandugaji zai dawo harkar fim gadan-gadan?

ƊANDUGAJI: Ai da ma ba guduwa na yi ba, don tun farkon fara fim ɗi na ba wai zuwa na yi na tambaya ake sa ni a fim ba, wani ne da man ya ga dacewa ta bayan na fito na yi tashe ya ke gayyata ta. Duk wanda ya gayyace ni zan amsa kiran sa gayyatar fim ɗin sa na zo, idan kuma ba ka gayyace ni ba ina gefe.Ko yau aka gayyace ni fim, in dai ba zai zubar da mutunci na da ƙima ta ba, zan amsa, kuma na ga ina da wani abu da zan taka rawa in bada gudunmawa ta ko faɗakarwa ko kuma nishaɗantarwa. Yanzun gaskiya ban daina ba.

FIM: Shin har yanzu ka na rubutawa da kuma shirya fim?

ƊANDUGAJI: E, don yanzu ma da a ce akwai wanda zai ɗauki nauyin finafinan da na rubuta, ina maraba. Kuma abin da ya sa ba zan ɗau nauyi da kai na ba shi ne yanzu ayyukan sun yi min yawa.

 Tun da farko da man na gaya ma ina aiki ne a filin tashi da saukar jirage ta Malam Aminu Kano. Ka ga kuwa ban da lokacin da za a ce ko da yaushe za a same ni, don wani lokacin ma ba na tasowa daga aiki sai dare ko kuma yammaci duk ba yanda aikin ba ya kayawa. Kai, a tsakiyar dare ma za a iya kira na in aikin gaggawa ya taso. Kuma ka ga ni ne shugaba a sashen da na ke.

FIM: Wanne albishir ka ke da shi zuwa ga masoyan ka? 

ƊANDUGAJI: Masoya na kamar yadda na ke haɗuwa da wasu a filin tashi da saukar jirage su kan nuna min damuwar su da ƙorafin su a kan me ya sa ba sa gani na. A Facebook ina samun saƙon su na roƙon don Allah na koma fim.  

To gaskiya ina ba ku haƙuri saboda shi harkar fim ba ni zan komar da kai na ba, sai an komar da kai, wato ina nufin sai an gayyace ni tukuna, in ba a gayyace ni ba ba yadda za a yi na kai kai na. Misali, don na iya fenti ba zan ga gini kawai in ce zan yi mai fenti ba ba tare da an sa ni ba, sai an ce zo ka yi tukuna. Amma kamar yadda na ke gaya ma, ni yanzu a harkar fim in an gayyace ni ina maraba kuma ina da gudunmawar da zan bayar. In ma da wanda zai ɗauki nauyin fim ɗi na ya ma zo ya saurari labarin tukuna. Sannan kuma ina dai ƙara ba su haƙuri, ba wai na gudu na bar fim ba ne, a’a mai yiwuwa fim ɗin ne ya guje ni. Amma dai na koma gefe ina aiki a nan iyafot, ina ICT Department, wato ni ne H.O.D. na nan.

FIM: A ƙarshe kuma ya batun aure kuma? 

ƊANDUGAJI: Ina da aure, mata ta ɗaya da ‘ya’ya na tara a halin yanzu.

FIM: Mu na godiya. 

 ƊANDUGAJI: Ni ma ina godiya. 

Loading

Previous Post

Menene laifin Rahama Sadau?

Next Post

Farfesa Yakubu ya miƙa ƙwaryar shugabancin INEC ga AVM Mu’azu

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Next Post
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Farfesa Yakubu ya miƙa ƙwaryar shugabancin INEC ga AVM Mu'azu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!