TSANA ce da kishi da wasu ke yi da Rahama Sadau ya sa ake ta ce-ce-ku-ce a kan shigar da ta yi. Mata nawa ne su ke ɗinka kaya matsattsu duk surar jikin su ana gani daga kan ‘yan fim ɗin har zuwa ‘yan matan da ba ‘yan fim ba, matan aure da zawarawa?
Ni dai ban san ko akwai wani abu daban wanda Rahama ta yi ba saɓanin kaya da ta sa mai nuna gadon bayan ta, saboda haka a kan wannan kaɗai zan yi magana ta.
Ban taɓa ganin Rahama Sadau da ido na ba sai a talabijin, ban taɓa magana da ita ba, ko na san ina ta ke da zama ba, kuma ni ban taɓa goyon bayan abin da ta ke yi ba, amma duk wata tsangwama ce aka ɗora mata wadda ta ke ƙara mata ɗimbin masoya, ta ke daɗa samun masu tausaya mata, kuma tausayi shi ne tushen ƙauna.
Masu yamaɗiɗi a kan shigar da ta yi su na cewa wai ta yi saɓo. Ta dai yi laifi, amma wanne irin laifi ne wanda za ta ce a yi haƙuri ta tuba, wanda za a ce kuma sai an hukunta ta?
Mun yi imani mu Musulmai ne, koyarwar Manzo Muhammad (S.A.W.) mu ke bi. To ni ba malami ba ne, balle wasu su ce in kawo aya, amma ina so masu surutun su kawo aya ko hadisi inda aka ce laifin ka ko da ya kai girman zina ba za a yafe maka ba idan ka tuba.
Akwai kuma raini da ‘yan fim su da kan su su ke jawo wa kan su sanadiyyar neman tonon asirin ‘yan’uwan su. Zuzuta abu da su ke yi idan wasu daga waje sun tsangwami ɗan fim ɗan’uwan su shi ne ya janyo wasu ke ganin duk ‘yan fim ‘yan iska ne.
Ashe a cikin mutane masu hankali, masu kamala, masu faɗakarwa a ce kullum doron ‘yan’uwan su su ke son gani? Kullum burin su a ce tir da ɗan’uwan su? Ba a ganin cewa dakatar da Rahama da ƙungiyar MOPPAN wadda mu mu ka kafa ta ta yi wa Rahama a baya ce ta daɗa kawo mata ɗaukaka ta samu karɓuwa a duniya ba Nijeriya kaɗai ba?
Tabbas, duk laifin da ɗan’adam ya yi wa Allahn sa Allah mai rahama ne a gare shi, amma idan aka cika zaƙewa kuma sai mai zaƙewar ya zama mai laifi.
Tabbas, Allah ya kasance mai gafara ga bayin sa.
Wata ma da na karanta nata labarin maida martani ga Rahama da ta yi, cewa ta ke da Rahama ‘yar ta ce wai da ta kashe ta. Wannan lafazi ne na neman suna. Duniya ta san ta, ita mai maganar, kuma burin ta ya fara cika tunda da ban taɓa sanin ta ba sai da ta yi maganar, amma ba gaskiya ba ce. Me Rahama ta yi na kisa? Ina hurumin zuwa ta kashe ‘yar ta a Musulunci? Idan da ‘yar ta ce, ƙarya ce ta yi yunƙurin kashe ta; ɓoye ta za ta yi!
Waɗanne irin sutura ita mai maganar ta ke sanyawa? Su wa ta ke yawo da su? Ina da ina ta ke zuwa? A waɗannan amsoshin ne za a gane.
Shi ma mai ƙarar Rahama Sadau ga ‘yansanda, ina hurumin ƙara ga ‘yansanda ya ke a kan abin da ake iƙirarin laifi ne na shari’ar Musulunci?
Ya raina kotunan shari’ar Musuluncin ne ko bai san inda su ke ba? Ƙara ga ‘yansanda a kan maganar Rahama Sadau a laifin da ta yi a yanzu, mai ƙarar ta ya nuna bai san darajar kotunan shari’ar Musulunci ba, ko kuma bai yarda za su yi aiki da ayoyin Alƙur’ani mai girma a wajen yin hukunci ba, ko kuma ya na gaggawar ganin an ci zarafin Rahama Sadau ne kawai.
Kuma yawancin lokuta idan ka ga mutum na zaƙewa a kan abu irin wannan, za ka ga in ka bincika, wataƙila shi ma mai laifin ne, ya na yin wannan kokawar ne domin neman suna. Ko ya taɓa cewa ya na son ta ta ƙi! Zaƙewa ta furuci, zaƙewa a yi hukunci, zaƙewa dai ta wuce gona da iri babu abin da ta ke janyowa illa jin kunya.
Idan aka ce a yi binciken laifukan mutum tsakanin shi Allahn shi, laifukan da ba ya so a tona, mutum nawa za su tsira? Idan ba a tsince ka a wannan ba, za a tsince ka a wancan.
Kwanan nan ‘yar tsohon shugaban EFCC, Malam Nuhu Ribaɗu, ta auri ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ta saka kayan auren Yahudawa, kayan masu nuna fatar ta. Wa ya kai ta ƙara?
Ko saboda ita ta fito tsakankanin masu faɗa a ji a ƙasar nan, waɗanda ba za a iya taɓa su ko ‘ya’yan su a kwana lafiya ba? Waɗanda duk kuɗin shigar da shari’a da za ka kashe, su za su kashe dubun su? A maimakon ka kulle ‘yar tasu, sai su su kulle ka?
Ita kuma Rahama wataƙila ‘yar talakawa ce, taka haye. Za kuwa ta bada mamaki tunda ta bada haƙuri ba a haƙura ba, to Allah zai kasance tare ita. Tunda Allah ne ya ce ku zama masu neman gafara idan kun aikata laifi, ku zama masu gafara idan an yi maku laifi. To an yi laifi an tuba, sai me?
Sani Muhammad Sani ya taɓa zama wakilin mujallar Fim na farko a Jihar Filato. Shi ne tsohon mataimakin sakataren Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa, da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar na reshen Jihar Filato. Yanzu kuma mataimakin shugaba na ƙasa na ƙungiyar masu wallafa jaridu na jihohin Nijeriya, kuma wakilin jaridar The Nation a Jihar Zamfara
![]()






