MUTUMIN nan da ya rubuta takardar koke kan Rahama Sadau ya gindaya wa ‘yansanda sharuɗɗan da za su bi kafin su ba ta beli.
Idan kun tuna, mutumin, wani mazaunin Abuja mai suna Malam Lawal Muhammad Gusau, ya kai koke ga Sufeto-Janar na ‘Yansandan Nijeriya a kan fitacciyar jarumar ta Kannywood da Nollywood, shi kuma ya bada umarnin a kama ta.
A yau ne dai ake sa ran Rahama za ta bayyana a ofishin Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna, Umar Muri, don amsa gayyatar da ya yi mata bisa umarnin na Sufeto-Janar.
Wata majiya mai tushe ta faɗa wa mujallar Fim cewa kwamishinan ya ɗaga wa jarumar ƙafa ne a kan zuwan ta ofishin sa jiya kamar yadda aka tsara, ya ce ta je a yau Lahadi.
Rahama da ƙannen ta mata su uku da mahaifiyar ta sun iso Kaduna a makare daga Abuja jiya bayan sun fasa tafiyar da su ka ƙudiri aniyar yi zuwa Dubai saboda umarnin na Sufeto-Janar.
‘Yansanda na binciken ta ne bisa zargin da Lawal Gusau ya rubuta a kan cewar wai ta aikata saɓo a kan Manzon Allah (SAW).
Tuni dai Rahama ta sha nuna wa jama’a cewa ba ita ce ta ci zarafin Annabi (SAW) ba, wani mutum ne daban ya aikata hakan a ƙarƙashin wasu hotuna da ta tura a Tuwita.
Haka kuma tuni ta goge hotunan tare da bada haƙuri ga ɗaukacin Musulmi kan abin da ya faru.
Sai dai a yayin da ta ke shirin zuwa hedikwatar ‘yansanda ta Kaduna, Lawal Gusau ya gindaya wa ‘yansandan sharuɗɗan bada belin ta a wata sanarwa ga manema labarai da ya saki a daren jiya.
Mujallar Fim ta fassaro sharuɗɗan kamar haka:
Na ɗaya, tilas ne lauyan Rahama Sadau ya kasance Musulmi. Dalilin sa shi ne lauya Musulmi ne kaɗai ya san yadda ake shari’a a kotun Shari’ar Musulunci inda ake aiki da Alƙur’ani da Hadisan Annabi (SAW), ba kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ba.

Na biyu, tilas ne aikin ‘yansanda ya tsaya ga aikin su na ɗaukar Rahama su na kai ta kotun Shari’ar Musulunci kaɗai bayan sun yi binciken sirri kan al’amarin.
Na uku, Malam Lawal ya bada sunayen malaman da ya ke so su zauna su yi wa Rahama alƙalanci kan saɓon da ya ke zargin ta da aikatawa.
Malaman da ya zaɓa, waɗanda dukkan su daga ɓangaren Izala ne, su ne: Sheikh Dakta Ahmed Mahmoud Gumi daga Kaduna; Sheikh Ahmed BUK daga Kano; Sheikh Kabir Haruna Gombe daga Gombe; Sheikh Nura Khalil (Digital) daga Abuja da kuma Ministan Sadarwa Sheikh Ali Isa Pantami.
Sharaɗi na huɗu da ya bayar kuma shi ne kada wani lauya daga Kaduna ko ma Arewa baki ɗaya ya tsoma baki cikin wannan magana ta Rahama Sadau.
A ƙarshe, Malam Lawal Muhammad Gusau ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalin su domin, kamar yadda ya ce, za a yanke wa Rahama hukuncin da ya dace da ita.
Wata majiya ta ce lauyan Rahama Sadau ne zai take mata sawu zuwa ganin Kwamishina Umar Muri a safiyar yau.