* Za su yi bikin cikar tashar Zinariya TV shekara 1 da fara haska fim ɗin ‘A Duniya’
FITACCEN Jarumi Tijjani Abdullahi (Asase) ya bayyana cewa yayin da ake yi yanzu na haska finafinan Hausa a manhajar YouTube shi ne ya ceci masana’antar Kannywood daga durƙushewa baki ɗaya.
A hirar sa da mujallar Fim, Asase ya ce: “Masana’antar ta nemi ta durƙushe, amma sanadiyyar shirye-shiryen fim masu dogon zango (series) ta farfaɗo, kuma ba a san alherin da zai zo nan gaba ba.
“Idan ka duba da, a masana’antar Kannywood kamfanoni a rana sama da talatin su na fita domin ɗaukar fim wanda har sai da ya zamana da kasuwar ta juya kamfani uku zuwa huɗu ne za su fita saboda durƙushewar da masana’antar ta so ta yi, amma yanzu zuwan wannan YouTube sai ka ga a yanzu ana samun kamfanoni sama da goma su na fita domin yin aiki.
“Wannan luɗufi ne na Allah wanda ba don ya canza mana daga wani abu zuwa wani abu ba da tuni masana’antar ta durƙushe.”
Asase ya yi wannan bayanin ne a cikin hirar da ya yi da mujallar Fim kan ƙoƙarin da ya ke yi na shirya wani taro domin murnar cika shekara ɗaya ana nuna fim ɗin sa mai dogon zango mai suna ‘A Duniya’ a manhajar ta YouTube.
Za a yi taron a ranar Lahadi, 16 ga Mayu, 2021 da misalin ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 10:00 na dare a wurin taro na Banana Event Centre da ke Kano.
‘A Duniya’ dai mallakin Asase ne, kuma ana haska shi a tashar sa ta Zinariya TV a YouTube.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa shirin ya zo da wasu abubuwan ban ta’ajibi da kuma salo wanda mutane ke kallon sa a matsayin wata hanya ta magance matsalolin tsaro, musamman yadda ake nuna ayyukan wasu ɓatagari da ma hanyoyin magance su.
Haka zalika, shirin ya zaƙulo wasu sababbin jarumai domin a bayyana wa duniya su da kuma irin rawar da za su iya takawa a cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
Karɓuwar fim ɗin a gun jama’a ce ta sanya mashiryin shirin kuma jagoran tashar Eagle Eye, Tijjani Asase, ya ga dacewar shirya wannan taro da ya yi wa taken “Daren Girmamawa” domin karrama wasu daga cikin zaɓaɓɓun mutane a cikin al’umma domin sada zumunci da kuma bayyana musu wasu daga cikin kurakuran su domin su gyara.
Ya ce a taron, za “mu haɗu mu ci mu sha mu kuma sada zumunci, mu kuma gayyato masoya waɗanda su ka bada gudunmawa daga kan ‘yan jaridu zuwa su kan su kan su ‘yan fim ɗin har ma da ‘yan’uwa da abokanan arziki.”
A hirar da ya yi da mujallar Fim, Asase ya yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa su ke ƙoƙarin shirya wannan taro, ya ce: “Fim ɗin ‘A Duniya’ yau tsawon shekara ɗaya kenan da fara shirya shi, wanda in ban manta ba a cikin watan azumin bara mu ka fara haska wannan shirin, kuma alhamdu lillah fim ya karɓu a gun jama’a.
“Duk da dai ga shi fim ne da ake sa shi a kafar YouTube, amma duk inda ka shiga za ka ga mutane su na kallon sa.
“Sannan kuma mu na amfani da sababbin jarumai, wasu ma ba a taɓa ganin su a fim ba, wani bai taɓa zuwa inda ake yin fim ba sai sanadiyyar wannan fim ɗin ya fara zuwa, kuma yau ga shi Allah ya ɗaukaka darajar sa.
“Tunda har ka tara mutane sababbi, to dole sai ka koya musu wani abu na shiga cikin mutane domin zumunci da yadda za su ma’amalanci junan su.
“Mun fara wannan fim da watan azumi. Mun kira taron shan ruwa ma a cikin watan da ya gabata, wanda mu ka kira wasu daga cikin waɗanda su ke kallon fim ɗin mu wanda mu ke ganin saƙwannin su a ko da yaushe domin karrama wasu daga cikin ‘yan wasan da ma mabiyan su zaɓaɓɓu kan yadda su ka bada gudunmawa a cikin masana’antar.”
Jarumin kuma furodusa ya bayyana cewa shi wannan taro da za a shirya, iya waɗanda aka gayyata ne kaɗai za su je, ba na gama-gari ba ne.
A ƙarshe, ya gode wa al’umma saboda yadda su ke ba shi goyon baya da haɗin kai wajen cigaban sa.