• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Asiya Ahmad: Abin da ya hana aure na da Adam Zango

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
May 10, 2020
in Taurari
0
Asiya Ahmad: 'Buƙata ta ta biya'

Asiya Ahmad: 'Buƙata ta ta biya'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ASIYA Ahmad ta na daga cikin matasan jarumai mata da su ka yi fice a Kannywood. Jarumar, wadda ake yi wa laƙabi da Asiya Maikyau, ƙanwa ce ga fitacciyar ‘yar wasan nan Samira Ahmad. 
 
Ya zuwa yanzu, Asiya ta samu kamar shekara biyar da fara yin aktin. Kuma ta shigo ne da ƙafar dama, saboda a lokacin da ta fara an yi wasoson ta.
 
Hakan bai rasa nasaba da cewa da gaske mai kyau ce, santala, doguwa, wato dai son kowa ƙin wanda ya rasa.
 
Haka kuma ga shi ta yi sabo da yawancin ‘yan fim saboda yayar ta Samira da mijin yayar a lokacin da ta shigo, wato fitaccen jarumi kuma mawaƙi, T.Y. Shaban. ‘Yan fim da dama na zuwa gidan su.
 
Bugu da ƙari, Asiya ta yi iya aktin ƙwarai da gaske, sannan ta shigo a daidai lokacin da furodusoshi da daraktoci su ke buƙatar matasan jarumai mata irin ta.
 
Waɗannan dalilai su ne su ka sa duk wanda zai saka Asiya a fim, to za ka taras a matsayin tauraruwar fim ɗin ya ke saka ta, wato mai jan fim ɗin.
 
Sai dai a hasashen da mujallar Fim ta yi, jarumar ta shigo Kannywood ne a daidai lokacin da harkar fim ta fara yin ƙasa. Hakan ya rage mata tashin gwauron zabon da ta fara yi, domin ba da jimawa ba aka shiga wani yanayi inda shirya fim sai wane da wane.
 
Idan masu karatun mu za su iya tunawa, mun taɓa bayyana maku a ‘yan shekarun baya cewa Asiya Ahmad budurwar fitaccen jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango ce. Abin nasu ma sai da ya rage kaɗan a ƙulla auren su, amma sai bai yiwu ba.
 
MUKHTAR YAKUBU na mujallar Fim ya tattauna da Asiya Maikyau don jin tarihin ta, da yadda aka yi ta zama ‘yar fim, da batun yadda Zango ya so ya aure ta. A ƙarshe, ta faɗa mana abin da ya fi damun ta game da ‘yan fim, har ta ba su wata shawara.
 
Ga yadda hirar ta kasance:
 
FIM: Da farko, ki fara da ba mu tarihin rayuwar ki a taƙaice.
 
ASIYA AHMAD: To ni dai suna na Asiya Ahmad, kuma an haife ni ne a garin Kano a shekarar 1994. Kuma na yi makarantar firamare a Giginyu, na yi sakandare a Da’awa.
 
FIM: Ya aka yi ki ka samu kan ki a cikin harkar fim?
 
ASIYA: Tun ina ƙarama ni na ke da sha’awar yin aktin, shi ya sa ma na ke tsayawa a gaban madubi ina gwada yadda ake yin aktin ina gani saboda abin ya na burge ni. Don haka sai na ke kallon kai na a matsayin jaruma!
 
To da na taso kuma sai na samu yaya ta, Samira, ta na yi. To babu yadda za a yi a ce ita ta na yi ni ma ina yi, dole sai ta matsa ni ma na samu na shiga. 
 
To kuma da ta yi aure ka ga babu damar ta yi fim ɗin haka, sai na fara yi. Kuma alhamdu lillahi ko da na fara sai ya zama abin ya zo mini da sa’a.
 
Don haka a yanzu na cimma buri na, na zama jaruma.
 
FIM: Shi laƙabin ‘Maikyau’, ya aka yi ki ka same shi?
 
ASIYA: To sunan Maikyau da ka ji ana cewa Asiya Maikyau, na same shi ne tun daga fim ɗin da na yi na farko. Sunan sa ‘Mai Kyau’. A nan na samu wannan sunan, wanda kuma a yanzu ina jin fim ɗin zai kai shekaru biyar. 
 
Kuma abin alfahari, daga fara fim ɗi na zuwa yanzu, duk da dai ba zan ce na fito a finafinai da yawa ba, amma waɗanda na fita za su kai wajen ashirin, don ina tuna wasu daga cikin su, kamar wanda na fito na farko, ‘Mai Kyau’, ‘Ranar Aure’, ‘Gida ‘Uku’, ‘Yankan Baya’, ‘Ƙanwa Ta’, da dai sauran su. 
 
Kuma abin da ya fi burge ni shi ne duk finafinan da na ke fitowa ni ce na ke jan fim ɗin, wato jarumar fim ɗin.
 
FIM: Shin ko kin samu matsala a shigar ki harkar fim?
 
ASIYA: A gaskiya zan iya cewa ban samu matsala ba domin tun kafin na shiga harkar fim ɗin duk wani jarumi ya san ni na san shi, saboda su na zuwa gidan mu, don haka babu wata matsala da na samu, saboda na saba da su.
 
FIM: To yanzu da yake kin zama jaruma, wanne buri ki ke da shi?
 
ASIYA: To ni dai kusan zan iya cewa buri na ya cika, domin a yanzu duk inda na shiga an san ni a matsayin jaruma. 
 
Wasu wuraren ma da ban isa na shiga ba, amma a matsayi na na jarumar da duniya ta sani sai na shiga har ma na shigar da wani.
 
FIM: A yanzu wanne abu ki ka saka a gaba da ki ke so ki cimma nan gaba?
 
ASIYA: A yanzu dai burin da na sa a gaba shi ne ina ci gaba da karatu, domin a baya ba ni da burin da ya wuce na shiga harkar fim, to da na shiga kuma na samu karɓuwa sai na ga kuma ina da burin na ci gaba da karatu. Don haka a yanzu abin da na sa gaba na kenan.
 
FIM: A can baya, an san labarin soyayyar ku da jarumi Adam A. Zango, wadda har ma ta kai ga an so a yi aure, sai dai daga baya aka ce maganar ta rushe. Ko menene gaskiyar maganar?
 
ASIYA: To ni dai da man a cikin harkar fim ban taɓa yin soyayya da wani jarumi ba, kuma har yanzu haka ne. Shi kuma Adam A. Zango, da man ya na zuwa gidan mu ne tun ina ƙarama, ban ma yi wayo ba, kuma tun a lokacin ya ce ya na so na kuma zai aure ni. Aka tafi a haka har ma da na girma ya na kan maganar.
 
To ni dai daga baya abin da zan ce da kai, Allah ne bai yi zan aure shi ba. Amma dai na san an yi maganar auren. Allah ne bai yi za a yi auren ba.
 
FIM: Ko akwai wani dalili wanda ki ke ganin shi ne ya hana a yi auren?
 
ASIYA: To, gaskiya dalilin da zan faɗa maka shi ne dai Allah bai sa za a yi ba. In ma akwai wani dalilin, to ka ɗauka Allah ne ya sa ba a yi ba.
 
FIM: Daga ƙarshe, wanne jan hankali za ki yi wa abokan sana’ar ki ‘yan fim? 
 
ASIYA: To abin da zan ja hankalin abokan sana’a ta a kan sa shi ne don Allah a rinƙa kiyaye mutuncin juna, domin ni abin da ya fi ba ni haushi a game da wannan harka sai kawai a je a rinƙa faɗar magana a kan ka wanda kai ma ba ka san da ita ba, amma sai a ce kai ne. 
 
Wannan ta sha faruwa a kai na, amma daga ƙarshe waɗanda su ka san ni idan sun ji maganar sai su ce wannan ba hali na ba ne.
 
Don haka ina kira ga jama’a a rinƙa kiyayewa da mutunci.

Loading

Tags: Adam Zango
Previous Post

Cewar Musa Maisana’a: ‘Yan sanda ba su kama ni ba

Next Post

Ɗan’iyan Kano Yusuf Bayero (1933-2020)

Related Posts

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan
Taurari

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

August 24, 2025
Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Next Post
Marigayi Ɗan'iyan Kano, Alh. Yusuf Bayero

Ɗan'iyan Kano Yusuf Bayero (1933-2020)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!