RANA ba ta ƙarya. A yau Juma’a, 4 ga Disamba, 2020 aka ɗaura auren fitaccen jarumi Nuhu Abdullahi da kyakkyawar amaryar sa, Jamila Abdulnasir (Siyama). An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:08 na rana a masallacin Juma’a na Alfurƙan da ke Alu Avenue, Nassarawa G.R.A., Kano.
Nuhu, wanda ake wa laƙabi da Mahmud na cikin shirin dirama mai dogon zango na ‘Labari Na’ da ake nunawa a gidan talbijin na Arewa24, ya biya sadakin Siyama N100,000.
Ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin jama’a da su ka haɗa da iyaye, iyayen gida, ‘yan’uwa da abokan arziki.
Abokan aikin angon a Kannywood manya da ƙanana sun yi kara sosai, sun halarta. Sun haɗa da Nazifi Asnanic, Kamal Sirrinsu, Garzali Miko, Feros Khan, Yusuf Magarya, Abdul Amdaz, Ibrahim Maishunku, Abdul Amart Maikwashewa, Nasiru Naba, Abdul’aziz A.Z., Ado Ahmad Gidan Dabino, Abdul’aziz Ɗansmall, Ibrahim Birniwa, Ibrahim Hausa da sauran su.
Kammala ɗaurin auren ke da wuya, mujallar Fim ta so jin ta bakin ango Nuhu game da irin farin cikin da ya ke ciki a wannan rana, to amma dai dandazon jama’a bai ba shi damar yi mana cikakkiyar magana ba. Sai dai kawai ya bayyana cewa: “Ina ina cikin farin ciki mara misaltuwa, sannan ina miƙa saƙon godiya ta ga duk wanda su ka halarci wannan ɗaurin auren. Na gode.”

A daren jiya dai aka yi walimar cin abincin dare wadda ita ma ‘yan fim masu yawa su ka halarta tare da ‘yan’uwa da abokan arzikin amarya da ango daga sassa daban-daban na rayuwa.
Nuhu dai yanzu ya tashi daga tazuru, ya zama maigidan kan sa. Allah ya ba su zaman lafiya da ƙaruwar arziki shi da Siyama, amin.
