• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za mu raba kuɗin tallafi ga matan karkara ko’ina a Nijeriya – Minista Sadiya a taron Imo

by DAGA WAKILIN MU
December 4, 2020
in Nijeriya
0
Minista Sadiya Umar Farouq ta na bada tallafin N20,000 ga wata tsohuwa a Owerri, Jihar Imo

Minista Sadiya Umar Farouq ta na bada tallafin N20,000 ga wata tsohuwa a Owerri, Jihar Imo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
DUKKAN jihohi 36 da ƙasar nan da kuma yankin Abuja za su amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na Agajin Kyautar Kuɗi ga Matan Karkara, wato ‘Special Cash Grant for Rural Women’, inji Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq.
 
Ta sha wannan wannan alwashin ne a wajen taron ƙaddamar da shirin a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ranar Alhamis, 3 ga Disamba, 2020.
 
A jawabin da ta gabatar a taron, ministar ta ce al’ummar Jihar Imo su ma masu cin moriyar shirin nan ne na tura wa mata agajin tsabar kuɗi, wato ‘Conditional Cash Transfer’ wanda aka ɗauki gidajen marasa galihu guda  11,697, da shirin N-Power, da shirin ciyar da ɗalibai da ke zaune a gida (Home Grown School Feeding) da kuma shirin tallafin yin sana’a na GEEP, wato ‘Government Entrepreneurship Empowerment Programme’.
 
Sadiya ta ce, “Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi maida hankali ga matsalolin marasa galihu a ƙasar nan tun daga 2015 kima mutum 150,000 ake sa ran za su ci moriyar shirin ta na bai wa matan karkara tallafin kuɗi a dukkan ƙananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan.
 
“Tun daga farkon shirin nan na ‘National Social Investment Programme’ a matsayin wani tsari na yaƙar talauci a tsakanin yawanci al’ummar mu, rayuwar talakawa faƙirai a Nijeriya ta inganta sosai. Da yawa daga cikin irin waɗannan mutanen sun samu cikakken sauyin rayuwar su. Saboda haka, ina farin cikin ganin taruwar ku a nan  domin ƙaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya na raba wa matan karkara agajin kuɗi, wanda ya na daga cikin shirye-shirye masu yawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu ta fito da su saboda ta ɗaga rayuwar yawancin jama’a daga ƙuncin rayuwa.
 
Wani sashe na ɗimbin matan da su ka halarci taron
Ministar ta ƙara da cewa manufar wannan agajin musamman ɗin ita ce a kai tsabar kuɗi kai-tsaye ga gidajen da su ke buƙata wanda hakan zai taimaka wa iyalan wajen sayen kayan masarufi, yin amfani da kayan magance matsalar yunwa sayen kayan abinci da kula da lagiyar jiki, da shigar da yara da biya masu kuɗin makaranta da dai sauran su. 
Ta yi kira a gare su da su yi amfani da kuɗin wajen yin ƙananan kasuwanci wanda hakan zai taimaka wa dogaro da kai  da samun sana’a. 
 
Tun da farko, sai da mai ba Gwamnan Imo Shawara kan shirye-shiryen cigaban al’umma na SDGs da ayyukan jinƙai,  Gimbiya Christina Udeh, ta ce ziyarar da ministar ta kai a jihar, shaida ce da ke nuna yadda ta ke damuwa da matsalolin tattalin arzikin al’ummar Jihar Imo, ciki har da naƙasassu da faƙirai da ke zaune a yankunan karkara.
 
Ta ce, “Shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin kuɗi ga   matan karkara zai rage fatara da yunwa, ya hana marasa galihu cigaba da faɗuwa cikin ramin fatara da yunwa kuma ya ba su kariya daga bala’o’i. 
 
“Haka kuma ministar ta zo nan ne domin ta ƙaddamar da Ranar  Mutane Masu Fama da Nakasa ta Duniya sannan ta raba N20,000 ga kowace macen karkara domin ta ja jari wanda zai taimaka ya sauya mata rayuwar ta da halayya.”
 
Daga bisani ministar ta miƙa tsabar kuɗi ga wasu daga cikin matan karkarar.
 
Matan sun bayyana godiyar su ga Shugaba Buhari saboda wannan tsari da ya fito da shi.

Loading

Previous Post

Hotuna: Dinar auren Nuhu Abdullahi da Siyama

Next Post

Aure: Nuhu Abdullahi da Siyama sun zama ɗaya

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Nuhu Abdullahi a tsakiyar dandazon jama'ar da su ka halarci ɗaurin auren sa a yau

Aure: Nuhu Abdullahi da Siyama sun zama ɗaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!