• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Aure: Nuhu Abdullahi da Siyama sun zama ɗaya

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
December 4, 2020
in Ranar Murna
0
Nuhu Abdullahi a tsakiyar dandazon jama'ar da su ka halarci ɗaurin auren sa a yau

Nuhu Abdullahi a tsakiyar dandazon jama'ar da su ka halarci ɗaurin auren sa a yau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
RANA ba ta ƙarya. A yau Juma’a, 4 ga Disamba, 2020 aka ɗaura auren fitaccen jarumi Nuhu Abdullahi da kyakkyawar amaryar sa, Jamila Abdulnasir (Siyama). An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:08 na rana a masallacin Juma’a na Alfurƙan da ke Alu Avenue, Nassarawa G.R.A., Kano. 
 
Nuhu, wanda ake wa laƙabi da Mahmud na cikin shirin dirama mai dogon zango na ‘Labari Na’ da ake nunawa a gidan talbijin na Arewa24, ya biya sadakin Siyama N100,000.
 
Ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin jama’a da su ka haɗa da iyaye, iyayen gida, ‘yan’uwa da abokan arziki. 
 
Abokan aikin angon a Kannywood manya da ƙanana sun yi kara sosai, sun halarta. Sun haɗa da Nazifi Asnanic, Kamal Sirrinsu, Garzali Miko, Feros Khan, Yusuf Magarya, Abdul Amdaz, Ibrahim Maishunku, Abdul Amart Maikwashewa, Nasiru Naba, Abdul’aziz A.Z., Ado Ahmad Gidan Dabino, Abdul’aziz Ɗansmall, Ibrahim Birniwa, Ibrahim Hausa da sauran su.
Kammala ɗaurin auren ke da wuya, mujallar Fim ta so jin ta bakin ango Nuhu game da irin farin cikin da ya ke ciki a wannan rana, to amma dai dandazon jama’a bai ba shi damar yi mana cikakkiyar magana ba. Sai dai kawai ya bayyana cewa: “Ina ina cikin farin ciki mara misaltuwa, sannan ina miƙa saƙon godiya ta ga duk wanda su ka halarci wannan ɗaurin auren. Na gode.”
Kowa cike da murna a wajen ɗaurin auren Nuhu Abdullahi
A daren jiya dai aka yi walimar cin abincin dare wadda ita ma ‘yan fim masu yawa su ka halarta tare da ‘yan’uwa da abokan arzikin amarya da ango daga sassa daban-daban na rayuwa.
 
Nuhu dai yanzu ya tashi daga tazuru, ya zama maigidan kan sa. Allah ya ba su zaman lafiya da ƙaruwar arziki shi da Siyama, amin.
Nuhu Abdullahi da Siyama a wajen dinar auren su jiya a Kano

Loading

Previous Post

Za mu raba kuɗin tallafi ga matan karkara ko’ina a Nijeriya – Minista Sadiya a taron Imo

Next Post

Jamila Kogi: Yadda mu ka tsallake rijiya da baya

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Jamila Kogi na nuna raunukan da ta ji a hannayen ta; a sama kuma motar da ta faɗi da su ce

Jamila Kogi: Yadda mu ka tsallake rijiya da baya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!