TSOHON Shugaban ƙungiyar masu shirya fim na farko a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Majalisar Dattawan Kannywood, Malam Auwal Isma’il Marshall, a wannan rana ta Lahadi 5 ga Fabarairu, 2023 ya aurar da ‘yar sa, Aisha ( Humaira) ga angon ta, Abubakar Sulaiman.
An ɗaura auren a Masallacin Juma’a na Umar Ibn Khattab da ke Shatale-talen Dangi, Kano, da misalin ƙarfe 11 na rana.
Jama’a da dama ‘yan Kannywood sun halarci ɗaurin auren.
Allah ya ba da zaman lafiya da ƙaruwar arziki a cikin zaman auren.
