• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba da tallafin wutar lantarki kashi 85 ya ƙara nuna Tinubu mai son jama’a ne – Minista

by WAKILIN MU
April 6, 2024
in Nijeriya
0
Ba da tallafin wutar lantarki kashi 85 ya ƙara nuna Tinubu mai son jama’a ne – Minista

Alhaji Mohammed Idris ya na jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 cikin 100 da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi ya ƙara nuna gwamnatin a matsayin dimokiraɗiyya mai son jama’a.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a jawabin sa na buɗe Taron Ministoci Karo na 4 a Cibiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa da ke Abuja.

Ministan ya ce: “A kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da wani tsari na cigaba a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da nufin bunƙasa wadatar wutar lantarki ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

“Wani muhimmin al’amari na wannan tsarin shi ne gwamnatin Tinubu na ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ga kashi 85 na masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayin gwamnatin dimokiraɗiyya mai son jama’a tare da yin ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kashi 15 na masu amfani da wutar lantarki kawai.”

Tun da farko, Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu ta samu a baya-bayan nan. A cewar Idris, “Tun bayan ganawar da muka yi da ku (’yan jarida) na baya-bayan nan an samu gagarumar nasara a tattalin arzikin mu, kasancewar dukkan mu shaida ne kan yadda ta hanyar aiwatar da wasu sauye-sauye na tattalin arziki, kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta daidaita, sannan kuma naira yana samun ƙarfi kullum.

“Kafa Majalisar Daidaita Tattalin Arziki da Tawagar Gudanar da Tattalin Arziki na Shugaban Ƙasa na kwanan nan ya jaddada ƙudirin Shugaban Ƙasa don samar da wani tsari mai muhimmanci na gudanar da tattalin arziki wanda ke yin amfani da ƙwarewa da fahimtar manyan masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu. Waɗannan ƙungiyoyin za su zama dandamali don tattaunawa mai ƙarfi, bincike, da yanke shawara don haɓaka ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa, samar da ayyukan yi, da wadata ga dukkan ‘yan Nijeriya.

“Ƙaddamar da Asusun Raya Gine-gine na Sabunta Fata (RHIDF) yana da niyyar tara kusan naira tiriliyan 20 don saka hannun jari a sassa masu muhimmanci kamar su tattalin arziki, sufuri, noma, da Fasahar Sadarwar Bayanai (ICT) da sauran su.

“Asusun yana neman tallafawa ayyukan da ke haɓaka ci gaba, samar da guraben aikin yi, da haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ketare.”

Idris ya ƙara da cewa, “Ayyukan da asusun zai sa a gaba sun haɗa da gina babbar hanyar Legas zuwa Calabar da aka fara kwanan nan, titin Sokoto zuwa Badagry, Legas zuwa Kano, hanyar jirgin ƙasa na Gabas da zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da na jiragen sama a faɗin ƙasar.

“Don faɗaɗa hanyoyin samun ilimi a matsayin makamin yaƙi da talauci, Shugaban Ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin dokar Lamunin Ɗalibai ta 2015, ta zama doka. Wannan yunƙurin ya wuce doka kawai – hanya ce ta juyin juya hali don kafa tsari na dindindin wanda zai tallafa wa neman ilimi daga matasan mu.”

Loading

Tags: gwamnatin TinubuMohammed Idristallafi
Previous Post

Zan kawo sauye-sauye kan yadda ake tafiyar da ƙungiyar ɗaliban Hausa ta BUK – Kabiru Anka

Next Post

Haihuwa ta 13: Baba Ari ya samu Nana Khadija

Related Posts

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa
Nijeriya

Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

May 13, 2025
Next Post
Haihuwa ta 13: Baba Ari ya samu Nana Khadija

Haihuwa ta 13: Baba Ari ya samu Nana Khadija

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!