• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zan kawo sauye-sauye kan yadda ake tafiyar da ƙungiyar ɗaliban Hausa ta BUK – Kabiru Anka

by MUKHTAR YAKUBU
April 6, 2024
in Labarai
0
Zan kawo sauye-sauye kan yadda ake tafiyar da ƙungiyar ɗaliban Hausa ta BUK – Kabiru Anka

Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SABON Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Harshen Hausa ta Jami’ar Bayero, Kano, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka), ya sha alwashin zai kawo sauye-sauye da za su canza yadda ake tafiyar da ƙungiyar a baya.

Ya faɗi haka ne bayan an zaɓe shi a matsayin sabon ƙungiyar a ranar Juma’a a zangon karatu na 2022/2023.

Anka, wanda ɗalibi ne a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya inda yake karatun digirin farko a fannin harshen Hausa, fitaccen marubucin littattafan Hausa da finafinan Kannywood ne.

An zaɓe shi tare da wasu masu dafa masa su 11 da suka haɗa da Nasiru Abubakar a matsayin Mataimakin Shugaba; Hisnuddin Auwal Tahir, Magatakarda; Umar Nasir, Mataimakin Magatakarda; Isa Garba Usman, Jami’in Shirye-shirye, da Khadija Yahaya Ɗanjuma, Jami’ar Walwala.

Akwai kuma Zulaihat Safiyanu da aka zaɓa a Ma’aji; Zubairu Ɗahiru Turaki, Jami’in Hulɗa Da Jama’a na farko (PRO 1); Mujahid Mansur; Mataimakin Jami’in Hulɗa Da Jama’a (PRO II); Jami’ar Wayar Da Kai Da Wasanni; Amina Sunusi Shamaki; da Hajara Shu’aibu Muhammad, Jami’ar Kuɗi.

Anka tare da sauran jagororin ƙungiyar

Kabiru Yusuf Fagge ya ce ya karɓi wannan shugabanci ne domin kawo sauye-sauye da yake ganin za su canza yadda ake tafiyar da ƙungiyar a baya.

Daga cikin abubuwan da yake da burin ganin ya samar domin farfaɗo da Ƙungiyar Hausa ta BUK akwai shirya tarukan wayar da kai ga sababbin ɗalibai, shirya tarukan sanin makamar karatu a zangon karatu da uwa-uba shirya taron Ranar Hausa da ake yi a ƙungiyar.

Haka nan kuma ya na so ya ga an gyara ofishin ƙungiyar da samar da littattafai don ɗalibai, da samar da motar zirga-zirga ta ƙungiya.

Sannan idan suka kammala wannan zango na shugabancin za su shirya zaɓe don a fitar da wasu shugabannin.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa shi dai wannan zaɓe ana gudanar da shi ne a duk bayan shekara a kowane zangon karatu domin samar da sababbin shugabanni, musamman saboda ‘yan aji 4 za su tafi sai a maye gurbin su.

Ana yin zaɓen ta hanyar kafa Hukumar Zaɓe, tare da bai wa ɗalibai damar yin zaɓe a junan su, ƙarƙashin kulawar hukumar makarantar.

Kuma ana zaɓo sababin shugabannin ne daga ‘yan aji na 1 zuwa na 4, sai dai an fi zaɓar ‘yan aji na 4 a matsayin shugaba da mataimaki ko sakatare.

An dai kafa Ƙungiyar Hausa ta BUK ne kamar sauran ƙungiyoyin jami’o’i domin haɓaka wannan sashe na Hausa aiwatar da tarukan da suka shafi cigaban harshen Hausa da al’adun Hausawa. Kuma ƙungiyar ta ce za su riƙa sanin darajar ilimin da su ke koya da kuma fito da kyawawan ayyukan sashen na Hausa.

Loading

Tags: Harshen HausaKabiru Yusuf Fagge Ankaƙungiyar ɗalibai
Previous Post

Makaɗi a Kannywood, Ahmad Yarima ya samu ƙaruwa da Afreen

Next Post

Ba da tallafin wutar lantarki kashi 85 ya ƙara nuna Tinubu mai son jama’a ne – Minista

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ba da tallafin wutar lantarki kashi 85 ya ƙara nuna Tinubu mai son jama’a ne – Minista

Ba da tallafin wutar lantarki kashi 85 ya ƙara nuna Tinubu mai son jama'a ne - Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!