• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba na neman kujerar Afakallah duk da yake ya kashe Kannywood – Salisu Officer

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 4, 2021
in Labarai
0
Ba na neman kujerar Afakallah duk da yake ya kashe Kannywood – Salisu Officer
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MATAIMAKIN Sakataren ƙungiyar masu shirya finafinani Hausa ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Salisu Mohammed (Officer), ya ce ba shi da niyyar neman wata kujera a gwamnati da ta danganci ta Hukumar Tace Finafina ta Jihar Kano duk da yake bai gamsu da yadda shugaban hukumar ke gudanar da ita ba.

Officer ya na daga cikin ‘yan fim waɗanda su ka yi amanna da cewa shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah) ba ya ɗaukar matakan da su ka dace domin haɓaka Kannywood.

A hirar da ya yi da mujallar Fim a yau, ya ce, “Faɗan da mu ke yi da Afakallah shi ne kowa ya sani kuma a bayyane ta ke cewa ya ƙi ya tsaya ya taimaki masana’antar. Hasali ma so ya ke ya binne ta da ran ta. Kuma yanzu in aka kalla za a ga ya riga ya binne ta da ran ta.”

Faɗin waɗannan bayanai sun biyo bayan maganar da wasu su ka riƙa ne da su ka ga wani hoto da Officer ɗin ya ɗauka tare da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya wallafa a Instagram.

Mujallar Fim ta fahimci cewa an ɗauki hoton ne a lokacin da shi da wasu ‘yan fim su ka  kai wa gwamnan ziyara a ofishin sa. 

Waɗansu masu nazarin al’amuran masana’antar finafinan sun yi zaton ko Salisu Officer ya je ne domin yin zawarcin kujerar shugabancin hukumar tace finafinai.

A hirar sa da mujallar Fim, Officer ya faɗi dalilin su na zuwa wajen gwamnan, ya ce, “Abu ne na gaskiyar magana ya kai mu gun gwamna, cewar idan ka na tafiya ya kamata ka na waiwaye ka na duba abubuwan da su ke faruwa, domin kuwa gaba ɗaya ba za mu yi kuɗin goro mu ce Ganduje bai taimaki masana’antar mu ba.

“Ganduje ya taimake mu, sai dai kawai an ɗan samu wasu matsaloli ne a wasu gurare domin kuwa an sha ji na ina magana domin akwai abubuwa da dama wanda idan su ka taso sai a yi wa masana’antar kuɗin goro bayan mu na da mabiya.”

Ya ƙara da cewa, “Ziyarar da mu ka kai wa gwamna a matsayin shugabanci mun kai masa ne domin mu nuna jin daɗin mu kan irin abubuwan da ya yi, musamman na bada muƙamai a wannan masana’anta, duk da muƙaman da ya bayar an samu wasu matsaloli daga cikin masu riƙe da wannan muƙaman.

“Gaskiya in ana tafiya ya kamata ana jinjina wa wanda ya ba wa masana’anta wata gudunmawa, domin kuwa ko da mu ka je shi da kan sa gwamnan ya ke tuntuɓar mu cewa ko akwai wata matsala? Domin ya na so ya ga ya ɗinke duk wata matsala shi daga ɓangaren sa. 


“Wannan shi ya sa ya ce mu zo ya ji daga gare mu, sannan mu kuma mu ga ta yaya za mu yi mu ga mun agaza masa a kan abubuwan da ya taho da su da zai ciyar da mu gaba.”

Officer ya ce Ganduje ya ɗaga darajar Kannywood ta hanyar bai wa ‘yan fim muƙamai guda shida zuwa bakwai, “to don haka babu yadda za a yi ka ci ribar gwamnati a shugabanci ba ka waiwayar irin waɗannan abubuwan da aka yi muku a masana’anta.”

Ya kuma ce su a matsayin su na shugabanni sun kalli irin abubuwan da gwamnan ya yi musu kuma su na so ya ɗora domin taimakon masana’antar a daidai wannan lokaci da ta ke kan ganiyar ta.

“A yayin ganawar tamu, mun kai wa gwamna wasu ƙudirirrika da dama da mu ke so ya taimaka mana, kuma mu na ganin In-sha Allahu zai taimaka domin mu na ganin za a ɗora.”

Mujallar Fim ta nuna wa Officer batun da wasu ke yi cewa da ma can ya na adawa da Afakallah ne saboda ya na harin kujerar sa, shi ya sa ya yi hoto da gwamna, wanda har ta kai ga wasu sun fara cewa idan hakan ta tabbata za su yi murna. Shin ko me zai ce kan wannan abu?

Salisu Officer (a dama) tare da Gwamna Ganduje

Sai Officer ya kada baki ya ce, “Ni ban taɓa kallon kujerar Afakallahu a matsayin wata kujera da zan bibiye ta ba. Ba na shiga harkar sa, sannan kuma na faɗa ko da taimakawa ne na yi aka ci gwamnati ba na buƙata. 

“Kowa ya buɗe kunnen sa ya ji: ba na buƙatar kujerar Afakallahu, saboda ni na yi aikin gwamnati, na san menene irin wannan kujerar, me za ta haifar ma. 

“Kuma menene a wurin? Babu wani abu a wurin illa kawai dama ta zo ka taimaka wa jama’a, masana’antar ka taimake ta.”

Da ya ke bayyana dalilan da su ka haifar da rashin jituwa tsakanin sa da Afakallahu, Officer ya ce, “Faɗan da mu ke yi da Afakallah shi ne kowa ya sani kuma a bayyane ta ke cewa ya ƙi ya tsaya ya taimaki masana’antar. Hasali ma so ya ke ya binne ta da ran ta. Kuma yanzu in aka kalla za a ga ya riga ya binne ta da ran ta.

“Ya ɗauke ni a matsayi na na shugaba. Ba za ka ɗauki abu a karan kan ka ka ce shi naka ne ba, kai gwamnati ne. Akwai ƙungiyoyi, akwai shugabanci, akwai komai da komai, don haka ya kamata ka buɗe hannu ka taimaki masana’antar domin a yaba ma wata rana ko da ka bar aiki.”

Officer ya ce, “Ni ba na faɗa a kan kujerar sa, saboda ni na yi aiki a Babban Bankin Nijeriya. Ka san na je ƙoli kenan. Kuma na yi aiki wanda har ta kai ga da hannu na na rubuta cewar na bar aiki a daidai lokacin da na kusa kaiwa muƙamin manaja. To don haka ba ni da wani wuri da na ke kallon wani matsayi.

“Amma inda na ke da amfani, na ke cin abinci a wurin, so na ke na ga an girmama an kuma karrama wurin domin shi ma (Afakallah) daga wurin ya fito kuma wannan ma na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa mu ke dabi.”

Ya kuma sha alwashin cewa “ko yau aka samu gyara da canji na tashin masana’antar daga faɗuwar da ta yi da kuma samar da aikin yi, don yanzu ba mu da aikin yi, shi ma kuma ba shi da aikin yi domin shi ma sama wa kan sa abin da zai ci abinci ya ke yi da mu, don sai mun yi aiki zai je ya duba, yanzu kuma babu aikin. 

“Kuma abin da ya ke ƙirƙirowa ba ya cikin doka. Amma kuma ba na nema kujerar sa. Ba abin da ya shafen da kujerar sa.”

To sai dai tuni wasu jarumai su ka fara nuna goyan bayan su ga yiwuwar naɗin Officer bayan sun ga hoton da ya yi da gwamna.

Fitaccen jarumi Mustapha Nabraska, wanda ɗan adawa da Afakallah ne, ya rubuta a ƙasan hoton cewa: “Babu shakka za mu kasance tare in-sha Allah. Ba za a ji kunya ba.”

Shi kuma jarumi kuma mawaƙi TY Shaban, tsokaci ya yi kan halin da masana’antar ta ke ciki a yau, musamman dangane da haƙƙin da ya rataya a wuyan Hukumar Tace Finafinai.

Ya rubuta a ƙasan hoton na Officer tare da Ganduje cewa, “Rashin jagoranci fal a cikin Kannywood, rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin Hukumar Tace Finafinai da ‘yan Kannywood; rashin bada damar ƙaro ilimin sana’ar Hausa fim a Kannywood da bunƙasa kasuwancin fim; rashin sabunta dokokin Hukumar Tace Finafinai; rashin bada goyon baya a wurin gwamnati wurin samar da katafaren  tsangayar adabi da ke garin Bebeji; bambaɗanci, hassada, ƙyashi, rufa-rufa, duk ƙaruwa su ka yi a Kannywood. Mun gode Baba (Ganduje), don Allah a gyara mana!”

A kan waɗannan maganganu da su ka bijiro a yau, wakilin mujallar Fim ya kira Afakallah ba sau ɗaya ba, amma bai amsa wayar ba, kuma bai kira ba har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.

Loading

Tags: Censorship in Nigeriahausa filmsIsmail na'abba afakallahKannywoodKano State Censorship BoardMOPPANMustapha NabraskaSalisu Mohammed OfficerTY Shaban
Previous Post

Ƙa’idojin rubutun Hausa: ANA za ta gudanar da bita a Kano jibi

Next Post

Bango ya faɗi: Ta’aziyyar Isiyaku Forest

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Bango ya faɗi: Ta’aziyyar Isiyaku Forest

Bango ya faɗi: Ta'aziyyar Isiyaku Forest

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!