• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba na shaye-shaye, inji Alhassan Kwalle

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 27, 2021
in Labarai
2
Ba na shaye-shaye, inji Alhassan Kwalle
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram


* Ya zama ambasadan NDLEA

SHUGABAN Ƙungiyar Jaruman Hausa ta Nijeriya (Hausa Actors Guild of Nigeria), reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Aliyu Kwalle, ya bayyana cewa shi ba ya shan miyagun ƙwayoyi ko wani abu mai sa maye.

Ya faɗi haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim a yau kan naɗa shi jakaɗe da Hukumar Yaƙi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta yi masa.

An naɗa Kwalle wannan matsayin ne a lokacin bikin Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi wanda hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Jami’ar Bayero, Kano, a jiya Asabar, 26 ga Yuni, 2021.

A hirar sa da wannan mujallar, Kwalle ya ce, “Wani zai ga ya samu wannan damar domin ya kai ga wata manufa ko wani gaci da ya ke son ya kai, to sai ni na ke kallon tunda har aka tabbatar da cewar ni mai hankali ne kuma aka tabbatar da cewar ba na shaye-shaye sannan kuma ake ganin zan iya taimaka wa al’ummar mu wajen ganin an daina wannan sha da fataucin ƙwayoyin da sauran kayan maye.

“Wannan matsayi ya nuna cewar ba na shaye-shaye, in ma ina shaye-shaye in daina, ballantana Allah ya taimake ni ma ba na yi. 

“Wannan zaburarwa ce aka yi mani. Su kan su abokan sana’a ta ya kamata a ce sun yi la’akari da haka saboda ba ni kaɗai aka yi wa wannan naɗin ba, don a cikin ɗimbin mutane aka zaɓo ka aka yi maka wannan naɗi ai ka ga ba ƙaramar nasara ba ce.”

Fitaccen jarumin ya bayyana farin ciki bisa wannan cigaba da ya samu, ya ce wannan naɗi wata manuniya ce ta irin zaman lafiya da kuma aiki tuƙuru a tsakanin sa da jama’a har ma da abokan sana’ar sa.

Lambar naɗin da aka yi wa Alhassan Kwalle

Ya ce, “Ina gode wa Allah da kuma abokanan sana’a ta da ke cikin wannan masana’anta. Sun ba ni gudunmawa ɗari bisa ɗari ta fannin yadda zan tsaya wajen gabatar da ayyukan shirye-shirye da su kan su masu kallon mu bisa yadda su ke nuna ƙwazo da gyararrakin da su ke yi mani, domin da wannan ne na samu wannan nasara har na kai ga wannan hukuma wanda shiga aikin su ma sai ka yi da gaske.

“A yanzu Allah ya kawo mu wani ƙadami wanda ko naɗin sarauta za a yi maka ko muƙamin gwamnati za ka samu sai an je an auna ƙwaƙwalwar ka a ga cewa ka na shaye-shaye ko ba ka yi.

“Cikin taimakon Allah aka ɗauke ni aka yi mani wannan ambasada na wannan hukuma. Ba ni da abin da zan ce da Allah sai godiya.”
 Shugaban ya ƙara da cewa wannan naɗi da aka yi masa ya zame masa wata igiya tare da ƙara zage damtse wajen yin aiki tuƙuru don ƙara daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin jarumai.

Shugaban ya yi kira ga ‘yan fim da su maida hankali wajen zama da kowa lafiya da yin mu’amala tagari a tsanin al’umma.

Ya ce, “A har kullum ina gaya wa jama’a da abokanan sana’a ta cewa mu a masana’antar nan mun gode wa Allah, saboda ba wai ka zo ka fara sana’a ka yi suna ko ka yi kuɗi ba shi ne abin nema ba. 

“Wannan wani abu ne in ka samu sai ka gode wa Allah, amma babban abin da ake so a ko’ina ka tabbatar da cewa wanene kai? Daga ina ka fito? Kuma ka na yi ka na waige ka ga daga ina ka fito. Abin da na ke nufi a nan shi ne ba wai an naɗa ka a ambasada na mai wannan sana’ar fim ba, a’a, ambasada ne na al’ummar ka ta Hausawa kuma ambasada ne kai na addinin ka, don haka idan da ba mu da mutunci ba za mu samu wannan damar ba.”

Ban da Kwalle, wasu daga cikin jarumai da su ma aka naɗa su jakadun hukumar sun haɗa da Shehu Hassan Kano, Hankaka, Bashir Bala (Ciroki) da Ruƙayya Dawayya.

Ruƙayya Dawayya da Shehu Hassan Kano sanye da lambobin naɗa su jakadun NDLEA da aka yi a wurin taron, jiya a Kano

Loading

Tags: Alhassan KwalleDrugs warHausa Authors GuildKannywoodNDLEA
Previous Post

Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Next Post

Lawan Ahmad ya sa gasar karatun Alƙur’ani

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Lawan Ahmad ya sa gasar karatun Alƙur’ani

Lawan Ahmad ya sa gasar karatun Alƙur'ani

Comments 2

  1. Pingback: Ba na shaye-shaye, inji Alhassan Kwalle – HausaLoaded.Com
  2. Pingback: Gaskiyar: Ba na shaye-shaye, inji Alhassan Kwalle – Arewarank.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!