A JIYA Talata, 7/4/2020, Allah ya azurta fitaccen jarumin barkwanci Aminu Baba Ari da samun ƙaruwar ‘yan biyu.
Jarumin ya shaida wa mujallar Fim cewa matar sa ta haifi tagwaye, dukkan su maza.
Ya ce, “Alhamdu lillahi, su na cikin ƙoshin lafiya, da yaran da mahaifiyar su. Don haka ina yi wa Allah godiya bisa wannan kyauta da ya ba ni.”
Tuni dai Baba Ari ya yi ta samun saƙwannin taya murna bayan ya ɗora sanarwar a soshiyal midiya inda ɗimbin jama’a su ka riƙa yi masa fatan alheri.
Su dai waɗannan ‘yan biyu, su ne cikon ‘ya’ya 10 na jarumin.
Allah ya raya su cikin aminci.