BAYAN dogon lokacin da ya ɗauka ya na zaman gudun hijira a Legas da Abuja sakamakon ƙin yarda da ya yi rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, a yanzu fitaccen jarumi Adam A. Zango ya dawo ya bi sahu.
Zango ya taɓa shelanta cewar ba zai yi rajista da hukumar ba saboda shi ba ɗan Kannywood ba ne, har ma ya sanar wa da duniya cewar ya fita daga masana’antar ya koma mai cin gashin kan sa, don haka duk abin da ya same shi to ya same shi ne a karan kan sa ba don Kannywood ba.
Tun daga lokacin sai shiga Kano domin gudanar da wani aiki da ya shafi harkar fim ta gagare shi, gudun kada ya yi aikin da ya shafi fim a Kano a kama shi.
To a yanzu dai jarumin ya sama wa kan sa lafiya, sakamakon miƙa wuya da ya yi ga hukumar.
Mujallar Fim ta ga fom ɗin sa da ya yi rajistar mai lamba 1002.
Wata majiya a hukumar ta faɗa wa mujallar cewa a yanzu jarumin kuma mawaƙi zai iya shiga Kano ya gudanar da harkokin sa na fim ba tare da wata tsangwama ba.
Majiyar ta ce tun kusan makwanni uku da su ka gabata ne Zango ya nemi ya yi rajista da hukumar, ta hanyar aika wani makusancin sa domin ya saya masa fom.
Da aka je sayen fom ɗin sai shugaban hukumar ya shaida masa cewa a dokar hukumar ba sa yi wa mutum rajista sai ya biyo ta hanyar ƙungiya, saboda haka in dai Zango ya na so a yi masa rajista, to ya je ya yi rajista da ƙungiyar jarumai, ya kawo shaida.
Hakan ya sa sai da jarumin ya je ya yi rajista da ƙungiyar a ƙarƙashin shugabancin Alhassan Kwalle sannan ya je hukumar aka yi masa rajista.
Ba Zango kaɗai ba ba ne ya bijire wa hukumar sannan daga baya ya je ya yi biyayya.
Fitaccen jarumi Garzali Miko ya taɓa lashar takobi ya ce ba zai yi rajistar ba, amma daga baya ya je ya yi.
Akwai wasu jarumai da ba fitattu ba su ma sun je sun yi, bayan da farko sun ce ba za su yi ba.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da mujallar Fim da cewa shi ma darakta Sunusi Oscar cikin wannan satin ya je hukumar domin ya yi rajista.
Idan kun tuna, a kwanan baya sai da hukumar ta kama shi ta kai shi kotu, wadda ta sa aka tsare shi a kurkuku a kan wata waƙa da hukumar ta ce ba a yi wa rajista ba.
![]()







