• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babu uzirin kasa cimma nasara a zaɓen Abuja, inji shugaban INEC

by DAGA WAKILIN MU
January 27, 2022
in Nijeriya
0
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gabatar da jawabi a taron

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ƙalubalanci jami’an zaɓe na hukumar da ke ofishin ta na Gundumar Babban Birnin Tarayya da su tabbatar da cewa an cimma nasara a zaɓuɓɓukan da za a yi na ƙananan hukumomin yankin a ranar 12 ga Fabrairu.

Farfesa Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga jami’an zaɓe da sauran ma’aikatan INEC da ke ofishin hukumar na gundumar a garin Abuja a ranar Laraba inda su ka tattauna kan zaɓen da za a yi.

Yakubu ya ce ofishin INEC na yankin Abuja bai da wani uziri da zai iya ba ‘yan Nijeriya idan ya gaza cimma nasara, domin kuwa hedikwatar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata ta yi wa ofishin ta na gundumar domin gudanar da wannan zaɓe.

Ya bayyana fatan alherin cewa da yake akwai ƙwararrun jami’an zaɓe a ofishin INEC na gundumar waɗanda sun gudanar da zaɓuɓɓuka a baya, ba su da wani uziri da za su bayar a kan gudanar da wannan zaɓe na ƙananan hukumomin.

Ya ce, “Mun shata layin inganci wajen gudanar da karɓaɓɓen zaɓe a Nijeriya, don haka zaɓen gundumar Abuja ba zai kasa a hakan ba.

Ma’aikatan INEC na ofishin gundumar Abuja a wajen taron

“Ko ma menene, za ku ga an samu ƙarin inganci wajen shirya karɓaɓɓen zaɓe a gundumar Babban Birnin Tarayya.”

Yakubu ya ce kamar yadda aka aiwatar da zaɓuɓɓuka kwanan baya a jihohin Anambra da Delta, hukumar INEC za ta yi amfani da na’ura mai suna ‘Bimodal Voter Accreditation System’ (BVAS) a zaɓen Abujan.

Ya ce, “Za mu sake tsara na’urar don ta yi daidai da kowace rumfar zaɓen Abuja daga yanzu zuwa ranar Juma’a.

“Mu na da isassun ma’aikata, kuma mun horas da su. Mu na da isassun masu tallafawa ta ɓangaren kayan aiki a Cibiyoyin Rajista waɗanda za su garzaya su kai ɗauki don gyara duk wata matsalar na’ura da aka samu a ranar zaɓen.

“Mun gama duk wani shiri na sufuri saboda su samu damar yin zirga-zirga a ranar zaɓe ko da ana buƙatar su je wajen zaɓe.

“Kamar yadda mu ka yi a zaɓuɓɓukan baya, za mu riƙa wallafa sakamakon zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin kai-tsaye ta hanyar intanet daga rumfunan zaɓen, sannan za mu bayyana wanda ya ci zaɓe ba kawai na ciyamomin ƙananan hukumomin ba har ma na kansiloli.”

Ya ƙara da cewa an tsara kayan aikin zaɓe masu haɗari bisa yawan jam’iyyun da za su shiga zaɓen.

Har wa yau, shugaban hukumar ya ce akwai ‘yan takara 475 a zaɓen waɗanda jam’iyyu 17 da ke takarar su ka zaɓa domin neman muƙamai 68.

Tun da farko a nasa jawabin, Kwamishinan Zaɓe na INEC (REC) na yankin, Alhaji Yahaya Bello, ya yaba wa Shugaban kan saurin da aka yi wajen sakin kuɗin da ake buƙata don gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin.

Bello ya bayyana cewa ya zuwa ranar 24 ga Janairu, jimillar katinan masu zaɓe na dindindin (PVC) da aka karɓa a gundumar su ne 103,68 yayin da ba a karɓi guda 265,868 ba.

Shugaban INEC da Manyan Kwamishinonin hukumar a wajen taron

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da karɓar katinan zaɓen a dukkan ofisoshin INEC na Ƙananan Hukumomi shida da kuma hedikwatar hukumar da ke Area 10, sannan ya ƙara da cewa za a dakatar da karɓar a ranar 4 ga Fabrairu.

Kwamishin zaɓen ya bayyana cewa jimillar masu zaɓe da su ka yi rajista a gundumar Abuja Abuja ya kai mutum 1,373,492.

Bello ya ce a cikin shirye-shiryen da ake yi na zaɓen, hukumar ta fara horas da jami’an kula da zaɓe, wato ‘Supervisory Presiding Officers’ (SPOs), da jami’an tsaro da sauran su.

Ya ƙara da cewa a cikin Disamba 2021 hukumar ta buɗe gidan yana domin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi, wanda aka rufe a ranar 6 ga Janairu, ya na mai ƙarawa da cewa, “Mun ciro takardun neman aiki a ciki, na sassa daban-daban inda ake buƙatar ma’aikatan, kuma yanzu mu na duba su.

“Daga lokacin da aka buɗe gidan yanar a ranar 6 ga Disamba, mun riƙa ciro takardun neman aiki daga masu neman aiki na muƙaman jami’an duba zaɓe (SPOs), ‘Presiding Officer’ (PO) da ‘Assistant Presiding Officer’ (APO).

“Bayan an rufe gidan yanar a ranar 7 ga Janairu, mun samu nasarar ciro jimillar waɗanda mu ke buƙata na muƙamin SPOs, wato 285 daga cikin 638 da su ka nema.

“A shiryen-shiryen da ake yi na zaɓen ƙananan hukumomin na yankin Abuja, an rarraba kuɗaɗe na matakai daban-daban ga jami’an zaɓe domin ɗauko hayar motoci, yi wa janaretoci sabis da zuba masu mai, da sauran su.”

Ya ce ya zuwa ranar 25 ga Janairu, an kai sama da kashi 75 cikin ɗari na kayan aikin zaɓe marasa haɗari zuwa ƙananan hukumomin, yayin da ake ci gaba da ilmantar da masu zaɓe gadan-gadan.

Bello ya ce daga yanzu hukumar za ta maida hankali da ƙarfin ta wajen tabbatar da an yi ingantancen zaɓen na watan Fabrairu, mai adalci kuma karɓaɓɓe.

Daga bisani, Shugaban na INEC, Farfesa Yakubu, ya shiga taron sirri tare da jami’an hukumar na ofishin gundumar Abuja don ƙara tattaunawa kan shirye-shiryen da ake yi.

Loading

Tags: Area CouncilsBabban Birnin TarayyaFarfesa Mahmood YakubuFCT pollHukumar Zaɓe ta ƘasaINECzabe
Previous Post

Cewar jarumin barkwanci Bawan Mata: Duk girman namiji, mace ce ta haife shi

Next Post

‘Yan Kannywood sun kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hanifa Abubakar

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Umar Gombe, edita Suleiman Abubakar da jaruman Kannywood mata a lokacin ziyarar

'Yan Kannywood sun kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Hanifa Abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!