‘YAN fim ɗin Hausa su na daga cikin ɗimbin mutanen da su ke yin tururuwa zuwa wajen kai ziyarar ta’aziyya ga iyayen ƙaramar yarinyar nan ‘yar shekara 5 wadda malamin makarantar su ya kashe, wato Hanifa Abubakar.
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Kano, ita ce ta wakilci ‘yan fim ɗin wajen kai ziyarar a yau Alhamis a ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na riƙo, fitaccen jarumi Umar Mohammed Gombe.
A makon da ya gabata ne dai aka gano gawar Hanifa bayan wanda ake zargin ya sace ta tare da kashe ta ta hanyar ba ta shinkafar ɓera ta sha, sannan ya daddatsa ta, kuma ya binne ta a harabar makarantar su ta Noble Kids da ke unguwar Dakata a birnin Kano.
Da ya ke bayyana alhini kan lamarin ga mujallar Fim, Umar Gombe ya nuna matuƙar alhini game da ɗanyen aikin da malamin makarantar ya aikata, ya ce, ”Ban taɓa ganin tashin hankali irin wannan lamari da ya faru kan wannan baiwar Allah ba, a ce yau malami wanda ake iya ba shi amanar rai shi zai yi irin wannan aika-aika, ba ƙaramin tashin hankali ba ne kuma a ƙasa ƙasar Musulunci, Musulunci da aka san shi da jinƙai da aiwatar da abu daidai.
“To ba abin da za mu ce sai dai Allah ya tsare mu daga mummunar ƙaddara.”
Mata ‘yan fim a gidan su marigayiya Hanifa Abubakar

Shugaban ƙungiyar ta MOPPAN ya sha alwashin tsayawa tsayin daka wajen ganin an ƙwato wa yarinyar haƙƙin ta.
Tawagar ‘yan Kannywood da su ka je ta’aziyyar tare da Umar Gombe sun haɗa da Sulaiman Abubukar, Saima Mohammed, Asma’u Sani, Aisha Yola da Asma’u Muhammad.
Shi dai wanda ake zargi da kisan kan, mai suna Abdulmalik Tanko, an gurfanar da shi a gaban kotun majistire da ke Gidan Murtala, a ranar Litinin da ta gabata, 24 ga Janairu, 2022.