TSOHON Editan mujallar Fim kuma sanannen mai ɗaukar hoto, Malam Sani Mohammed Maikatanga, ya bayyana farin cikin sa dangane da lashe gasar ɗaukar hoto ta duniya mai ‘Wiki Loves Africa 2023’ da ya yi. Ya ce bai taɓa zaton zai lashe gasar ba.
An yi gasar ne a kan jigon sauyin yanayin duniya, wato ‘Climate & Weather’
A gasar ta bana, fasihai daga ƙasashen Afrika sun shiga gasar da hotuna 13,386, sautuka 28 da bidiyoyi 228 a kan maudu’in ‘Climate & Weather’.
Alƙalai sun yi nazari kowane hoto, sauti da bidiyo da aka shigar. Alƙalan sun haɗa da ɗimbin ‘yan sa-kai, da kwamitin alƙalai gwanayen hoto na mutum 11 daga sassa daban-daban na duniya. A ƙarshe, alƙalan na ƙasa da ƙasa su ka zaɓi zakaru uku na gasar, kuma Maikatanga ne a saman su.
Maikatanga ya zo na ɗaya ne da wani hoton ambaliyar ruwa da ya ɗauka a garin Auyo, Jihar Jigawa, kuma tukwicin da ya samu shi ne dalar Amurka 2,000.
Taken hoton shi ne, ‘Auyo village flood’.

Wanda ya zo na biyu, Mohamed Nasr daga ƙasar Somaliya, ya samu kyautar $1,500 da hoton sa na hadari da ya dirkako wani sansanin ‘yan gudun hijira, yayin da na uku, Mohammed Osman daga Sudan, ya samu $1,000 da hoton sa na wasu yara da ke tsaye a bakin gulbi.
Maikatanga ya nuna farin cikin nasa ne yayin zantawar sa da mujallar Fim, inda ya ce, “Abu ne da ban taɓa tunani ba. Saboda na san an ce Afrika, amma kuma sai Allah ya yi ikon sa kamar yadda na samu na lashe gasar ‘Global Landscape Forum Africa’ da aka yi a shekarar 2022, sai ga shi wannan ta ‘Wiki Loves Africa Photo Competition 2023’ ɗin da aka yi a kan ‘Climate & Weather’, ita ma na zama zakara.”
A kan nasarar da ya samu a cikin mutanen da su ka shiga gasar, tsohon editan namu ya ce: “To, ba na fi kowa iyawa ba ne. Allah ya ƙaddara dai hoto na ne ya yi daidai da abin da ake so a gasar.
“Ina yi wa Allah godiya. Kuma ina gode wa alƙalan wannan gasar da su ka zaɓi hoto na ya zama na ɗaya a cikin hotuna sama da dubu goma sha uku da aka shiga da su gasar daga ƙasashe 51 na Afrika, amma ni daga Nijeriya kuma Jihar Kano na zama na ɗaya. Ina yi wa Allah godiya, kuma na yi farin ciki matuƙa.”
Ita dai wannan gasa, Gidauniyar Wikipedia ce ke shirya shi a duk shekara domin ƙarfafa gwiwa ga ‘yan Afrika masu fasaha a ɓangarorin ɗaukar hoto, haɗa hotuna (graphics), ɗaukar sauti, da kuma shirya guntun fim, wato bidiyo.

A bana, an ba da dalar Amurka 750 ga wanda ya ci gasar a ɓangaren sauti; $1,000 ga gwanin ɗaukar bidiyo, da $750 ga gwanin haɗa hotuna.
Akwai kuma kyautar musamman ta $2,000 ga wanda ya fi nuno yadda sauyin yanayi ya shafi rayuwa a Afrika, da $500 ga wanda ya kawo tarin hotuna masu bayyana tasirin sauyin yanayi a nahiyar.
