DALILI mai ƙarfi ya saka ni yin rubutun nan a wannan rana, ba domin ina da natsuwar yin sa ba. Facebook ga amanar wannan rubutun.
Na zaɓi wannan rana domin in sanar da ku halayyar maza da ban cika ji ana faɗa ba. Dalilin hakan ko yana da nasaba da ƙarancin su ne?
Muna rubutu a kan soyayya, sai mutanen mu suka yi ta kashe mana zuciya a kan babu soyayyar nan fa, da zarar an yi aure sai zaman haƙuri.
Alhamdu lillah… In-sha Allahu miji na ɗan Aljanna ne. Na san kowa zai sha mamakin idan na gaya maku a tsawon zaman da na yi da shi ban taɓa ganin ya yi mini tsawa wai don na yi ba daidai ba, sai dai cikin nasiha da ban baki. Ba ni kaɗai ba, haka ma sauran.
Duk da haka bai sa wata a cikin mu ta raina shi ba, idan ya saka kara ya ce, “Fatima kada ki tsallaka,” ba na iya tsallakawa.
Idan na ce masa ina son abu, idan har kuka ga ban samu abin nan ba ku tabbata bai da shi ne, kuma ba zai iya gaya min kai-tsaye ba, sai dai in fahimci yana ƙoƙari ne wajen nema mani abin.
Ban taɓa kai ƙarar sa gidan mu ba, bai taɓa kai ƙara ta ba. Babu matsalar da ta taɓa gagarar mu warware ta a dare ɗaya.
Kun ce maza ba su bai wa mace haƙuri ko? Miji na ya kasance wanda ko a fuska idan ya ga kin sauya zai kirawo ki ya ce idan shi ya ɓata maki rai ki yi haƙuri. Ban haƙuri sosai ba irin na izgilanci ba, kuma ba zai samu natsuwa ba har sai ya tabbatar da kina dariya.
Ina da saƙonnin sa masu tarin yawa kowanne yana bayyana mini yadda yake son Fatin sa ne. A kullum idan na ji kewar sa idan na koma makaranta saƙonnin sa suke ɗebe mini kewa.
Idan na fito aji kuwa ban ga kiran sa ko saƙon sa ba, sai in ji kamar an yi mani mutuwa. Yana kira zai fara ba ni haƙuri yana gaya mani dalilai, tare da rufewa da kalmar “Kin san ina son ki, komai nake kina rai na.”
Shafin zamantakewar mu sirri na ne, amma mun yi mata kyakkyawar shimfiɗa, mun shirya ta bisa gaskiya, ya fahimce ni na fahimce shi.
Akwai abin da idan ka gaya masa Fatin sa ta yi, kai-tsaye zai ce ƙarya ce ba dai Fatin sa ba.
Ko fuskar sa ce na gan ta ba daidai ba, ba na barin sa ya fita yana ɓacin rai, sai na san duk yadda zan yi in gan shi cikin farin ciki. Sau tari yana ɓoye damuwar sa domin gudun shiga ɗimuwar Fatimar sa, sai dai fa a idanun sa kaɗai idan na kalla ina gane ‘yan kaya na.
Idan bai da lafiya, sai ya yi ta ƙarfin hali saboda ya san yadda nake ruɗewa a kan sa, ya san yadda ciwon sa ke hana ni barci, ya san yadda ciwon sa ke saka ni kuka da rashin walwala.
(Murmushi😁) Komai na saya sai in ce miji na na saya wa. Ban taɓa yin tafiya ba tare da na yo masa tsaraba ba, ko da kuwa a kasuwa na saya, sai na saya masa abin da zai saka shi farin ciki, ko da kuwa abin bai fi naira ɗari biyar ba.
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan posting ɗin taimako ɗaya nake buƙata: ku yi masa addu’ar Allah ya inganta lafiyar sa. Allah ya taimake ni ya ci gaba da ba ni aron sa. Na sani, shi ɗin ba nawa ba ne, duk yadda nake son sa bai kai yadda Shi yake son sa ba. Haka duk yadda yake so na bai kai yadda Allah ke so na ba.
Allah Kai ne Allah, Allah Kai ka haɗa ni da bawan ka ba tare da na san shi ba, Allah kai ka ba mu ikon rayuwa a cikin farin ciki, Allah Kai ka ba shi ikon canza mini rayuwa, Allah Kai ka ba mu kyautar yaro ɗaya jal! Allah Ka san zuciya ta, Allah domin alfarmar Annabi Muhammadu (S.A.W.) Ka inganta lafiyar miji na. Allah Ka ba mu ikon renon Ahmad da hannayen mu.
Ba na bayyana nasara ta, amma ina so ku ɗauki wannan a matsayin nasarar rayuwa ta.
Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka 1st September mai ɗauke da kambun girmamawa. Allah ya ƙara lafiya da kwanciyar hankali.
