Allahu Akbar! A safiyar yau ne Allah ya karɓi ran tsohon Alƙalin Alƙalan Jihar Kaduna, Mai Shari’a Tanimu Zailani, bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa a garin su, wato Rigachikun, da ke bayan garin Kaduna.
Mai Shari’a Zailani dai ya riƙe muƙamin shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Kaduna kuma Babban Alƙali (Chief Judge) na Babbar Kotun Jihar Kaduna daga 2013 zuwa 2018 lokacin da ya yi ritaya.
Shi ne mijin fitacciyar marubuciya Hajiya Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno (wato Teemah Ɗanborno).
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa marigayin ya rasu ya bar mata uku da kuma ‘ya’ya da jikoki da dama.
Allah ya rahamshe shi, ya albarkaci abin da ya bari, kuma ya ba iyalin sa haƙurin jure wannan babban rashi, amin.
![]()







