ƊAYA daga cikin manyan daraktoci a Kannywood, Sir Hafizu Bello, ya yi raddi ga furodusa Salisu Mohammed Officer kan iƙirarin sa na cewa harkar finafinan Hausa ta gama mutuwa, babu komai a cikin ta.
Idan kun tuna, a ranar 5 ga Disamba, 2022 mujallar Fim ta kawo maku hirar da ta yi da Alhaji Salisu Mohammed Officer, wanda ya ke ɗaya daga cikin jagororin Kannywood, inda ya ce harkar fim ta lalace tun daga lokacin da ta tashi daga kan tsarin ta na da inda ake buga finafinai a kaset a kai kasuwa.
Officer, wanda mazaunin Kano ne, ya ce: “Ita masana’antar Kannywood ta na nan a matsayin ta na masana’anta tun daga lokacin da aka kafa ta, amma idan ka duba yadda kasuwancin masana’antar ya ke da kuma yadda ake tafiyar da ita, to a yanzu za a iya cewa babu komai, saboda a yanzu idan ka duba ayyukan da ake fita wasu ‘yan kaɗan ne da ba su wuce guda biyar ko shida ba su ne waɗanda ake ɗorawa a YouTube da wanda ake haskawa a gidan talbijin, saɓanin yadda ake yi a baya lokacin da kasuwancin ya na tafiya da za ka furodusa ɗaya ya buga fim sama da dubu ɗari ya shigar da shi kasuwa.
“Sai ya zama abin yanzu ya koma YouTube da kuma gidan talbijin, to su kuma ba kamar yadda za ka yi ka kai kasuwa ka sayar ba.”
To a nasa martanin, Hafizu Bello ya ce a gaskiya babu wani lokaci da masana’antar Kannywood ta ke samun cigaba da kuma bunƙasa kamar a yanzu.
A tattaunawar sa da mujallar Fim, sanannen daraktan ya ce: “Ai Kannywood ba a ma fara ta ba, ina ganin sai shekara mai zuwa ma za a fara harkar fim ɗin. Saboda matsalar ita ce mutane su na manta cewa harkar cigaban rayuwa ta cinye abubuwa da yawa.
“Yanzu ba lokaci ba ne na yin bidiyo kaset, sidi, da sauran abubuwa makamantan su. Harkar ta koma ‘online’, YouTube canel da sauran abubuwa na cigaba da a yanzu ake da su.”
Da ya ke tsokaci kan iƙirarin da Officer ya yi, Hafizu ya ce saboda sauyin da aka samu, “a yanzu ba zai yiwu ba kawai wani ya zo ya ce Kannywood babu ita. Kawai zance ya ke yi, ko kuma bai san inda aka dosa ba.”
Da ya ke kawo hujjar cewa Kannywood ƙara ma ƙarfi ta ke yi, sai ya ce, “A yanzu babu yadda za a yi a ce da ni Kannywood ta mutu, domin kuwa daga watan Janairu zuwa yanzu na san an sayi kayan aiki a masana’antar Kannywood ya fi na naira miliyan 250 daga kyamara zuwa fitulu da sauran abubuwa na aiki. Ko a yanzu waɗannan finafinan da ake yi, duk da sababbin kyamarori ake yin su. To amma kuma za a ce Kannywood ta mutu? Sannan kuma a bayan da ake cewa ana yin fim ɗin, ba a samu irin wannan kayayyakin ba.”
Game da batun cewa yanzu ‘yan fim ba su samun aikin shirya fim, Hafizu ya ce, “Duk wanda ya ke cewa babu aiki, to shi ne ba ya aikin. Saboda abin da ya ke faruwa a yanzu shi ne Kannywood ɗin ce ta girma, kuma mutane ba su san ta girma ba. An samu ɓangarori da yawa. Ai da fim kala ɗaya kawai ake yi wanda za a yi a kai kasuwa. To amma a yanzu, akwai masu yin fim mai gajeren zango na sakawa a YouTube, akwai masu yin na gidan talbijin, akwai masu yin na sinima. Duk irin wannan daga farkon shekara zuwa yanzu an yi masu yawa. Sannan kuma a zo a ce harkar fim ta mutu? Ai wannan ba hujja ba ce. Don haka a yanzu masana’antar Kannywood bunƙasa ta yi, ba baya ta yi ba.
“A yanzu ka ga a ‘yan kwanakin nan an yi ‘film festival’ har guda biyu a Kannywood, wanda a baya ba a yi ma kuwa shi wannan ya na ɗaya daga cikin matakin arziki a cikin masana’antar fim; ina nufin ‘KILAF Awards’ da kuma ‘Kano International Films’ da aka yi. Ɗaya ma daga cikin su mutane daga ƙasashen waje sun ma an yi da su. To gaskiya ni ban yarda Kannywood ta mutu ba.
“Kuma bayan haka a yanzu duk inda ka samu ɗan fim a yanzu za ka ji ya ce ya na son ya yi fim wanda za a haska a Netfilix ko Amazon domin sun zo cikin Kannywood. Da man mu su ke jira, don ko a kwanakin nan akwai wani taro da aka yi a Legas, har Dakta Ahmad Sarari ya je, a kan irin wannan tsari da za a yi, kuma akwai taron da aka yi wanda ba ma a nan ƙasar ba ne. Amma na ga Rahama Sadau ta tashi ta na magana a kan Kannywood.
“Duk waɗannan abubuwa an yi su, kuma za a ce Kannywood ta mutu?”
Dangane da cewar ‘yan fim sun koma siyasa kuwa, cewa shahararren daraktan ya yi: “Ai idan aka ce ‘yan fim, mutane su na ɗauka jarumai ne. Su waɗannan ai ba za ka hana su ba. Manhaja su ke zuwa talla.
“Sannan kuma duk waɗannan jaruman da ake faɗa, duk YouTube ne ya ɗaga su har aka kira su su ke wannan harkar siyasa.
“Sannan kuma mu na da YouTube canel da mu ke da ita a nan Kannywood; ita ce ma ta 20 a duk Nijeriya. Ai da labarin mu ke ji, sai mu ji an ce ai YouTube ɗin ‘yan Kudu kaza da kaza, amma a yanzu ‘yan Kudun ne su ke kallon YouTube ɗin mu, don a yanzu fim da ake sakawa na Hausa, sai ka ga an samu masu bibiyar sa sama da mutum miliyan biyu.
“Sannan kuma a yanzu akwai fim ɗin da mu ka yi, bin mu ake yi za a saye shi miliyoyi.
“Don haka a yanzu tsarin ne ya canza. A baya idan ana yin finafinai da yawa, to a yanzu dole ne ka je ka yi mai inganci.”
Hafizu ya ƙara da cewa ya kamata a zo a yi wa shugaban ƙungiyar MOPPAN, Dakta Ahmad Sarari, godiya saboda irin wannan tafiye-tafiyen da ya ke yi daga Legas zuwa Abuja duk a kan harkar fim, “amma duk mutane ba sa gani. Kuma duk taimaka wa harkar fim ɗin ake yi.”
Kuma wai har ana maganar an samu ƙarancin jarumai, bayan a yanzu ne ma jaruman su ka fi yawa. Ka duba Abale, Lawan Ahmad, Isa, Aisha Najamu, Momee Gombe, duk ga su nan YouTube ne ya ɗaga su. Kuma a yanzu akwai manyan jarumai da idan ka faɗi sunan su ma ba a sani ba, sai ka faɗi sunan da su ka fito a cikin fim.
“Don haka a yanzu ne ma jaruman su ka fi yawa, saboda ni a yanzu, da yake jaruman sun yi yawa wasu da yawa ma ban san su ba, saboda a yanzu akwai jaruman da su ka shigo harkar fim sun fi ɗari biyar, sai dai mutum in ba ya zawa wajen lokeshin, don yanzu ne ake da jaruman, ba da ba.
“A baya idan ka na aiki idan jarumi ya ba ka matsala ka shiga uku. Amma a yanzu ga jarumai nan sun fi dubu, a yanzu babu maganar sai wane da wane. Don haka idan babu aiki ai ba za su yi yawa ba.
“Don haka masana’antar Kannywood daga nan zuwa 2025 idan ba ka da miliyan hamsin ma ba za ka iya yin fim ba saboda a yanzu harkar fim ta canza, don akwai manyan kamfanoni da su ka fara zuwa daga waje ana ƙulla yarjejeniya da su wanda sai da masu ƙarfi za su yi harkar.
“Don haka na ce da kai nan gaba idan ba ka da miliyan hamsin to ba za a yi harkar fim da kai ba a masana’antar finafinai ta Kannywood.”