BAYAN kammala shagulgulan bikin auren ‘ya’yan sa da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata, 28 ga Yuli, 2024, mujallar Fim ta tuntuɓi uban amaren uku, wato Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), don jin yadda ya samu kan sa a karo na farko da ya aurar da ‘ya’ya uku:
FIM: Muna taya ka murnar auren ‘ya’yan ka da aka yi a Lahadin da ta gabata. Masu karatun mu za su so su ji yadda ka samu kan ka a cikin hidimar bikin.
ALHAJI AMINU ALA: To, muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan lokaci na aure wanda aka saka rana wata uku, kuma ga shi a yanzu muna tattaunawa bayan an kammala biki, kowa ya watse bayan an yi hidimar bikin an gama lafiya, kuma duk waɗanda suka zo sun koma gidan su lafiya.

FIM: Da yake wannan shi ne karo na farko da ka aurar da ‘ya’yan ka kuma har su uku, ko yaya hidimar bikin ta zo maka?
AMINU ALA: Ka san wani abu ne wanda yake ko ba ka da ƙwarewa a kan sa, to yana faruwa a kan idon ka, ka na maƙwafta da abokan arziki, don haka an yi a gidan ku da wasu da kake gani. Amma duk da haka sai ka samu wasu ‘yan bambance-bambance idan aka ce kai ne za ka yi.
Saboda haka, akwai muhimman mutane na kurkusa waɗanda sai ka manta ba ka sanar da su ba waɗanda ka na ganin su a cikin hidimar ma suke.
Yanzu dai ka ga mafi kusa a cikin masarautun da na ke kusa da su, masarautar Gobir, saboda ni ɗan Sarkin Gobir ne, to ban kai katin gayyata can ba. Sannan dubi yadda muke da masarautar Dutse, ban kai katin gayyata can ba!
To, ka ga irin wannan, sai ka ga mutane na kurkusa sai ka ga ka yi kuskure a kan su. Haka kuma akwai amintattun mutane waɗanda tare kuke faɗi-tashi, amma sai ka ga ka manta da wani mafi kusa kuma ka gayyato wani na nesa. To irin waɗannan abubuwan su ne wanda aka rinƙa cin karo da su.
Kuma ka san an canza lokaci, 4 ga watan Agusta za a yi, sai ake ganin masu zanga-zanga sun ce babu fashi, kuma ba mu san da sigar da za ta zo ba, amma dai muna fatan Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya a ƙasar mu. To wannan shi ne ya sa su masu neman auren suka ga dacewar a matso da shi baya zuwa 28 ga Yuli. To wannan ma ya ɗan daburta abubuwa da dama. Amma dai muna murna don an yi taro an tashi lafiya kuma cikin nasara.
FIM: Tara jama’a irin wannan akwai darussa masu yawa. Ko wane darasi ka samu?
AMINU ALA: Akwai darussa sosan gaske har ma da wasu ilimummuka da za ka samu. Kamar yanzu ka ga a matsayin mu na ‘ya’yan Sarki muna da al’adun mu da yawa wanda muka bari saboda nisa da kuma tsoron halin da ake ciki na rayuwa da kuma rashin tsaro da ake ciki musamman a Arewa-maso-gabas, to wannan ya sa muka haƙura.
Amma idan za a wanke ‘ya’yan Sarki ana kai su wajen Sarauniya ta Gobir saboda ita za ta yi masu wankan lalle; akwai wankan al’ada da kuma kayan al’ada da suke sakawa, akwai takalmi da sauran kayan al’ada, sannan za a je a gabatar da su a gaban Sarki ya yi masu huɗuba da nasiha, sannan su yi bankwana da shi. Sannan mu dawo da su a fara hidimar bikin. Ka ga duk wannan ba mu yi ba.
Sannan a nan masarautar Kano ta karɓe mu, wanda ka san Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, uba ne a gare mu kuma ya tsaya a matsayin uba, don haka sai muka tsaya muka yi al’amuran mu a ƙarƙashin wannan masarauta, wanda bayan an kammala biki ya kamata a ce ranar da aka ɗaura auren za a kai amaren, to sai da muka kai su kashegari don su je su yi sallama da Sarki, suka je suka yi hotuna da Sarki suka yi sallama.

Kuma muna yin amfani da wannan dama wajen godiya ga waɗannan masarautu, musamman masarautar Kano da ya zama suka zo kamar ƙwan su da kwarkwatar su, don akwai hakimai da yawa waɗanda suna ma ba zai yiwu ka kama sunan su ba saboda lokaci, waɗanda suka taho ƙarƙashin masarautar Kano da fadawan Sarki da masoya duk gabaki ɗaya suka zo suka cika wajen, don in ka lura har da motar Sarki ta dogarai aka zo don taya mu murna.
Haka kuma idan ka kalli masarautar Zazzau, Ciroma ma aka taso, wadda sarautar Ciroma ta babban ɗan Sarki ce, to shi ne ya zo. Kuma amini na ne kuma yaya na ne, maigida na ne, kuma ina da kusanci da shi, don a Zazzau idan ka ɗauke Ɗanburan Barden Kudu, to babu wanda na ke zuwa gidan sa sama da shi Ciroma. Ina zuwa gidan sa mu yi hira mu ci abinci. Muna hulɗar arziki da shi, amma na manta ban kai masa katin gayyata ba, sai kuma ya zama shi ne wakilin Sarki.
Kuma akwai hakimai da suka zo, irin su Shattiman Yamman Zazzau da sauran hakimai da yawa da suka zo daga Zazzau. Sannan akwai hakiman Misau, kamar Muƙaddam ya turo saƙo da wakili, sannan akwai Dujuman Misau.
Sannan akwai hakimai daga Gombe, kamar Zannan Nafaɗa, wato Alhaji Ibrahim Jalo Sarkin Zangon Dukku, da kuma hakimai da suka zo daga ƙasar Gumel, wato Lautai, da kuma hakimi da ya zo daga masarautar Lafiya, wato Bulaman Lafiya.
Sannan kuma ga Salanken Gaya, Salanken Ƙasar Hausa ta Daura kuma Salanken Mubi, da Sa’idu Gombe, El-Mu’az Birniwa da sauran mutanen da suka zo waɗanda ba za su misaltu ba. Don ka ga akwai Sarkin Dawaki Babba, ga Sheikh Ibrahim Khalil, su ne waliyyai, ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Sharif Muhammad Rijiyar Lemo wanda shi ne ya ɗaura auren ya yi huɗuba.
Saboda haka babu abin da zan ce wa mutane, musamman waliyyan nan guda uku, Sheikh Ibrahim Khalil da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da kuma Sharif Muhammad Rijiyar Lemo da suka yi walicci na waɗannan amare.
Sai ‘yan dangin juna abokan mu’amala a cikin masu wasan kwaikwayo da finafinai da rubutu, akwai marubuta sun zo, irin su Ado Ahmad Gidan Dabino, Kabiru Yusuf Fagge, sai tsohon Akanta na Ƙasa.
Na ji daɗi na yi farin ciki, don unguwar mu suka ce ba su taɓa ganin shigar manyan mutane cikin unguwar ba kamar wannan rana da aka yi ɗaurin auren ‘ya’ya na saboda masu kanti a unguwar har gajiya suka yi da tambayar ina ne gidan Ala.
Babu shakka, wannan aure ya ɗaga martaba ta, don martaba ce ta ‘ya’yan, amma ya ɗaga martaba ta a matsayi na na mahaifin su a idon al’ummar unguwar, kuma su ma al’ummar unguwar sun ba ni haɗin kai, duk da su aka yi wannan hidima.

Sannan akwai mawaƙa irin su Fati Nijar, Fantimoti, Maryam A. Baba, Ahmad Yariman Tiga, Shalelen Waƙa da ya zo daga Zazzau tare da mahaifiyar sa.
Don haka babu abin da za mu ce sai dai Allah ya saka wa kowa da alheri, kuma Allah ya maimaita mana irin wannan alherin.
Yaran nan da aka aurar da su Allah ya ba su zaman lafiya da mazajen su, Allah ya azurta su, kuma Allah ya hore wa kowa, ƙasar mu Allah ya ba mu zaman lafiya.
FIM: Madalla, mun gode.
AMINU ALA: Ni ma na gode sosai.