• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tallafi: Rahama Sadau ta yi wa mabiyan ta na Facebook ruwan naira

by ABBA MUHAMMAD
August 2, 2024
in Labarai
0
Tallafi: Rahama Sadau ta yi wa mabiyan ta na Facebook ruwan naira

Rahama Sadau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Juma’a jaruma kuma furodusa Hajiya Rahama Sadau ta yi wa mabiyan ta na Facebook mutum ɗari kyautar kuɗi don tallafawa kan halin matsi da ake ciki.

Tun da farko, jarumar ta rubuta cewa, “Barkan mu da Juma’a … Yau dai Let’s do some small giveaway, shall we? Drop Aza & I will pick randomly. Love Y’ll.”

Kafin ka ce kwabo, jama’a su ka yi caa su na tura lambar asusun bakin su a sashen sharhi (comment section) na shafin ta, wanda aƙalla an samu lambar asusun mutum sama da 23,800.

Bayan awa huɗu, Rahama ta rubuta cewa, “The target is to credit 100 people today with different amount. My hand don tire already. Please confirm receipt once you see alert. (I would also post receipts later). To be continued much later insha Allah. Till then, stay safe.”

Mujallar Fim ta fassara kamar haka, “Mutane ɗari ne hari na a yau da adadi mabambanta. Hannu na ya riga ya gaji. Don Allah ku aiko da rasit da zarar kun ga alat. Zan kuma buga rasit ɗin daga baya. Zan cigaba da ya daga baya in-sha Allah. Sai lokacin, ku zauna lafiya.”

Wasu daga cikin waɗanda su ka samu nasara sun fara tura rasiɗin kuɗin da Rahama ta tura masu.

A shekarun baya Rahama Sadau ita ce jarumar Kannywood da ta yi ƙaurin suna a soshiyal midiya, musamman idan ta yi abin da wasu ke ganin ba daidai ba ne.

Amma a yanzu jarumar ta na ɗaya daga cikin jaruman da ake yabo, musamman ganin ta daina saka ire-iren tufafin da ta ke sakawa masu nuna jikin ta.

A yau dai ta wanke kan ta, ta na ta shan ruwan addu’a wajen ɗimbin mutane, ana ta shi mata albarka.

Loading

Tags: kyautar kuɗiRahama Sadautallafi
Previous Post

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

Next Post

Mun yi gargaɗin cewa zanga-zanga za ta iya zama tarzoma – Idris

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Mun yi gargaɗin cewa zanga-zanga za ta iya zama tarzoma – Idris

Mun yi gargaɗin cewa zanga-zanga za ta iya zama tarzoma - Idris

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!