• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buhari ya naɗa daraktan Ma’aikatar Jinƙai Grema memba a hukumar haɓaka arewa-maso-gabas

by DAGA WAKILIN MU
May 8, 2023
in Nijeriya
0
Alhaji Grema Ali

Alhaji Grema Ali

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa hukumar gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas (NEDC) mai wakilai goma sha biyu da su ka haɗa da Daraktan Sashen Harkokin Jinƙai a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya, Alhaji Grema Ali.

A sanarwar da mai ba ministar harkokin jinƙai shawara kan aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta raba a Abuja a ranar Litinin, an bayyana cewa Buhari ya aika da takarda zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan a ranar 3 ga Mayu, 2023, inda ya buƙaci majalisar da ta amince da naɗin sababbin membobin hukumar gudanarwar.

Shugaban ƙasar ya ce: ‘‘Kamar yadda Sashe na 1, ƙaramin sashe na 2(5)(b) na Dokar Kafa Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas ta 2017 ya tanadar, ina farin cikin gabatar wa da Majalisar Dattawa mutum 12 da aka zaɓa, kamar yadda aka jero su a nan ƙasa, a matsayin membobin Hukumar Gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas. 

‘‘Ina kira ga Majalisar Dattawa da ta lura da cewa wa’adin ‘yan Hukumar Gudanarwar Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas zai ƙare a ranar 7 ga Mayu, 2023.’’

Waɗanda aka zaɓa ɗin dai su ne: Lauya Bashir Bukar Baale, Ciyaman (Arewa-maso-gabas, Yobe), Suwaiba Idris Baba, Babbar Darakta, Harkokin Jinƙai (Arewa-maso-gabas, Taraba), Musa Umar Yashi, Babban Daraktan Gudanarwa da Kuɗi (Arewa-maso-gabas, Bauchi), Dakta Isma’ila Nuhu Maksha, Babban Daraktan Ayyuka (Arewa-maso-gabas, Adamawa), da Umar Abubakar Hashidu, Shugaba (Arewa-maso-gabas, Gombe).

Sauran su ne Grema Ali, memba (Arewa-maso-gabas, Borno), Onyeka Gospel-Tony, memba (Kudu-maso-gabas), Hon. Madam Hailmary Ogolo Aipoh, memba (Kudu-maso-kudu), Air Commodore Babatunde Akanbi (ritaya), memba (Kudu-maso-yamma), Mustapha Ahmed Ibrahim, memba (Arewa-maso-yamma), Hadiza Maina, memba (Arewa ta Tsakiya), da wakili daga Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa ta Tarayya.

Loading

Tags: Ahmed LawanArewa-maso-gabasGrema AliHarkokin JinƙaihukumaMajalisar DattawaMuhammadu BuhariNEDCNneka Ikem AnibezeSadiya Umar Farouq
Previous Post

Maza sun saba da tauye haƙƙin mata a fagen adabi – Maryam Ali Ali

Next Post

Rasuwar Kawu Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta girgiza jama’a

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Marigayi Malam Aminu Muhammad, 'Kawu Mala a shirin 'Daɗin Kowa'

Rasuwar Kawu Mala na shirin 'Daɗin Kowa' ta girgiza jama'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!