• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maza sun saba da tauye haƙƙin mata a fagen adabi – Maryam Ali Ali

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
May 6, 2023
in Marubuta
0
Dakta Maryam Ali Ali: "Tarihin rubutun Hausa ba zai cika ba sai an haɗa da mata"

Dakta Maryam Ali Ali: "Tarihin rubutun Hausa ba zai cika ba sai an haɗa da mata"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa tauye haƙƙin mata da marubuta maza su ke yi wani abu ne da ya daɗe kuma har yanzu sai ƙara ci gaba ya ke yi.

Marubuciya kuma malamar makaranta, Dakta Maryam Ali Ali, ita ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke tsokaci a wajen taron da marubuta su ka shirya a ranar Lahadi da ta gabata a Kano.

Dakta Maryam, wadda babbar malama ce a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, ta faɗa wa mahalartan taron cewa: “Su maza ba za su rabu da son kan su ba a duk wata harka ta rayuwa, don haka ko a wannan taron ma sai da su ka nuna halin nasu na son kai. Don haka tun da aka fara taron har zuwa yanzu babu wata marubuciya mace da aka ambata a matsayin gwarzuwar da ta bayar da gudunmawa a cikin adabin Hausa; duk wanda ya zo jawabin sa sai ya ambaci maza marubuta a matsayin waɗanda su ka bayar da gudunmawa, duk da kowa ya san mace ce farkon marubuciya a adabin Hausa, wato Hafsat Abdulwahid, amma har aka kusan tashi daga taron nan ba a ambaci gudunmawar da ta bayar ba.”

Malamar, wadda ita ce ta rubuta littafin ƙirƙira mai suna ‘Fuskokin Naira’, ta ƙara da cewa, “Bayan ita, akwai manyan marubuta mata irin su Bilkisu Salisu Funtua, Balaraba Ramat, da sauran su, amma su da yake mata ne kamar babu wata gudunmawa da su ka bayar. 

“Wannan kuma ɗabi’ar maza ce ba tun yanzu ba. Domin ko a lokacin Manzon Allah (s.a.w.) da aka zo rubuta sunayen gwaraza saboda son kai na maza sai su ka rubuta littafi ‘Arrijalu Haula Rasulu’. Sai daga baya da aka yi magana, su ka dawo su ka rubuta ‘Annisa’u Haula Rasulu’.

“Don haka wannan wani abu ne sananne a tarihi na tauye haƙƙin mata da maza su ke. Mu kuma ba za mu zuba ido mu na kallon ana tauye mana haƙƙi ba, don haka in dai za a yi taro a faɗi gwarazan marubuta, to tarihin rubutun Hausa ba zai cika ba sai an haɗa da mata. Saboda haka ya zama dole a gyara in dai ana son a yi adalci.”

Loading

Previous Post

Abba Zakin Hausa zai angwance da Asiya

Next Post

Buhari ya naɗa daraktan Ma’aikatar Jinƙai Grema memba a hukumar haɓaka arewa-maso-gabas

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Alhaji Grema Ali

Buhari ya naɗa daraktan Ma'aikatar Jinƙai Grema memba a hukumar haɓaka arewa-maso-gabas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!