• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Afakallah: Na yafe wa Aliyu Sabo Bakin-Zuwo cin mutunci na da ya yi, to amma…

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
October 26, 2021
in Labarai
0
Cikin gajeren bidiyo, Aliyu Sabo Bakin-Zuwo (a hagu) ya nemi afuwar Isma'il Afakallah (a dama)

Cikin gajeren bidiyo, Aliyu Sabo Bakin-Zuwo (a hagu) ya nemi afuwar Isma'il Afakallah (a dama)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya ce ya yafe wa wani matashi ɗan fim mai suna Aliyu Sabo Bakin-Zuwo wanda ya zazzage shi a wani guruf na WhatsApp.

Wannan ya biyo bayan gafarar sa da ya nema.

Shi dai Aliyu, ya shiga guruf mai suna ‘Kannywood Vanguard’ ne ya tarar ana sukar Afakallah kan dokar nan da ya kafa ta hana yin fim a kan kidinafin ko ƙwacen waya. Ba tare da ya bi zaren tattaunawar ba sai ya rubuta muggan kalamai a kan shugaban.

Amma a wani bidiyo da ya yi, Aliyu ya nemi afuwar Afakallah kan abin da ya yi.

Ya ce ya yi kalaman ne bisa kuskuren fahimta kuma hakan ba zai ƙara faruwa ba.

Da ya ke bada lamarin yadda abin ya faru, Aliyu ya ce, “Akwai wani guruf wanda mu ke amfani da shi na ‘Kannywood Vanguard’, da ya haɗa jarumai, masu bada umarni da masu shirya fim, a cikin wannan group a Whatsapp, kasan cewar akwai masu ra’ayi daban-daban da su kan kawo maganganu na suka, musamman ga shi Afakallahu ɗin. To da yawa yawancin mutune saboda maganganu su na da yawa ba ka da damar da za ka ce sai ka je ka jiwo tun daga rajin magana wajen ɗari biyu ce, to sai na yi kuskure na fara da tsar daga inda bai kamata na ji ba sai na ji kamar an zo da ra’ayin shi Afakallahu na ba ya ƙaunar masa’antar ne.

“Amma cikin ikon Allah, bayan na fahimce shi ba daidai ba, sai na yi zage-zage na ɓatancin kalamai a kan sa.

”Ana haka kuma sai na yi wa kai na adalci cewa in koma baya mana in ji me ma Afakallahu ya yi har ake masa wannan kalaman a gidan. Sai na je na saurari bayanan da ya yi a wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC, sai na ji ashe shi Afakallahu ƙokari ya ke ya kare mutuncin al’adar mu ta Hausa da kuma harka ta tsaro ɗin nan da ta lalace ya ke ƙoƙarin cewar bai kamata a dinga nuna wa mutane yanda ake kidinafin ake satar waya ba wanda ma bai san ana yi ba in ya kalli irin wannan fim ɗin sai ya zo ya koya ya ce au, haka ma ake yi? Kamar misali an yi wani fim, ‘Gwaska’, yara duk ba su san ya ake a shiga makaranta a fasa a mammanna takardu dalilin wannan fim sai aka samu yara su na fasa abu su mammanna abu a bango sai su rubuta daga ‘Gwaska’ ne.”

Aliyu ya nemi afuwar masoyan sa bisa kalaman da ya yi kan Afakallah.

Lokacin da mujallar Fim ta ji ta bakin Afakallah kan wannan lamari a yau, shugaban hukumar ya ce, “Na haƙura kamar yadda ya bada haƙuri”.

“Ba za mu bari don Allah ya yi wa wani ni’ima ba kawai mutane su zauna su na zagin mu. 

“Kuma wannan haƙuri da ya bayar, mun karɓa kuma mun yarda da cewa hakan ya zama horo a gare shi da kuma izna ga duk wanda ya ke so ya yi, da sauran su.”

Sai dai Afakallah ya nuna cewa mahassada ne su ka taso shi gaba, amma daga yanzu ba zai lamunta da haka ba.

Ya ce, “Ta ya za a yi don Allah ya ba wa mutum ni’ma ko ya ba shi shugabanci kawai mutane su ɗauki wannan abin ya zama abu ne da kawai na za su ci mutuncin mutum ya tafi kawai? Ba zai yiwu ba!”

Afakallah ya gargaɗi duk wani mai niyyar aikata irin wannan da cewa, “Duk wanda ya ke tunanin yin haka nan gaba ya shirya wa haka.”

Loading

Tags: Aliyu Sabo Bakin Zuwohausa filmsKannywoodKano State Censorship Board
Previous Post

Jami’ar Jihar Sokoto ta shirya gasar rubuta ‘waƙa kwaikwaye’

Next Post

Nana Firdausi, matar mawaƙi El-Bash, ta kwanta dama

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Marigayiya Nana Firdausi tare da mijin ta da 'yar su a cikin mota

Nana Firdausi, matar mawaƙi El-Bash, ta kwanta dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!