• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Hadiza Gabon: Ƙarya ne, ba ni da wata alaƙa da Shehu Gabam

by DAGA ALI KANO
June 29, 2022
in Labarai
0
Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Aliyu Gabon

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar Kannywood, Hajiya Hadiza Aliyu, wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa ta jini da sanannen ɗan siyasar nan na Jihar Bauchi kuma Shugaban jam’iyyar ‘Social Democratic Party’ (SDP) na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam.

Wata jaridar intanet mai suna ‘Grassroots Africa’ ta wallafa wani labari a gidan yanar ta a yau cewa wai Hadiza Gabon ƙanwa ce shaƙiƙiya ga shi Shehu Gabam.

A rahoton da ta yaɗa mai taken “Actress Hadiza Gabam, a Nigerian, Sister to former Jonathan’s protocol”, wato ‘Jaruma Hadiza Gabam ‘yar Nijeriya ce kuma ƙanwar tsohon jami’in Jonathan’, jaridar ta bayyana cewa buga labarin da ta yi zai kawo ƙarshen tunanin da ake yi na cewar Hadiza ‘yar ƙasar Gabon ce.

A cewar labarin, wanda tsohon ɗan jarida Sani Muhammad Sani ya rubuta da hannun sa, an ce: “Da farko iyayen ta ba su amince mata ta shiga harkar fim ba, wanda hakan ne ya sa ta riƙa ɓoye gaskiyar inda ta fito kuma ba ta taɓa faɗa wa duniya gaskiyar yadda ake rubuta sunan ‘yan gidan su ba, wato Gabam.”

Sai dai binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa labarin ƙanzon kurege ne.

Da wakilin mu ya tuntuɓi Hadiza Gabon, sai ta ce labarin “ba gaskiya ba ne ba.”

Haka kuma jarumar ta tabbatar da cewa ita ba ta ma san Shehu Gabam ɗin da ake magana ba. 

Ta ce, “Wanene shi ɗin? Ba ni da kowace irin alaƙa da shi.”

Alhaji Shehu Musa Gabam

Su ma ƙawayen jarumar, irin su fitacciyar mawaƙiyar nan Sadiya Yarima, sun ƙaryata labarin tare da tabbatar da cewa Hadiza ‘yar asalin Gabon ce.

Wani tsohon ubangidan jarumar, fitaccen furodusan nan da ke Kaduna, Alhaji Yakubu Lere, ya ce mawallafin wancan labarin “bai san Hadiza Gabon ba.”

Ya ƙara da cewa in da ya san ko ita wacece, “da bai rubuta labarin ba.”

Lere, wanda shi ne ya shirya fim ɗin ‘Wasila’, ya ce hasali ma dai Hadiza ta zo Nijeriya ne saboda shi.

“Kuma wani ya ce wai ‘yar Bauchi ce, bai ma san komai game da ita ba kenan,” inji shi.

Ya ce, “Daga Gabon ta zo. Ta biyo a mota daga ‘Central African Republic’, ta Kamaru, ta zo Adamawa.

“Kuma ta ce mini ta na da ‘yan’uwa ta wajen uwa a Adamawa.”

Ya ce lokacin da ta zo Nijeriya, ko Turanci ba ta ji, kuma Hausa ba ta ishe ta ba, “sai Fulatanci da Faransanci.”

Ya ce farkon zuwan ta, a gidan wasu ‘yan’uwan ta ta sauka a unguwar Nasarawa a garin Kaduna, kuma da ta ce masu Yakubu Lere ta ke so ta gani sai su ka ce mata, “In dai Lere ne, ki kwantar da hankalin ki, zai zo nan gidan.”

Lere ya ce a lokacin, akwai wani abokin sa mai suna Sulaiman Lere wanda ke neman aure a gidan, kuma shi ya na raka shi.

Wata rana da su ka je gidan, Sulaiman ya gabatar da shi gare ta, daga nan Lere ya zama ubangidan ta har ta na zuwa ofishin sa.

Lere, wanda ɗan siyasa ne a yanzu, ya ce, “A lokacin ma har ina zuwa ofishin mujallar Fim tare da ita wajen marigayi Abaab (Abdulrasheed Kankiya) a Yoruba Road.”

Ya ce abin da ya fara fito da jarumar shi ne fim ɗin ‘Wasila’ da aka sake ɗauka a cikin 2010, wanda shi ne ya saka ta a ciki.

Lere ya ce ya san Shehu Gabam sosai, domin sun yi aiki tare a lokacin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a shekarun baya.

Ya ce, “Zancen ma Sani ya ce daga Bauchi ta fito bai taso ba. Ba sa ma kama da juna.

Hadiza Aliyu Gabon

“In ka lura har yanzu ba ta iya Hausa sosai ba, sai Faransanci. Ta ma taɓa zama a ƙasar Faransa kafin ta zo Nijeriya.”

Ya ce ya san Hadiza sosai, domin har gobe ta kan zo gidan shi ta gaisa da iyalin sa.

Lere ya ce: “Su mutane… haba! Ba daɗi irin wannan. Me (Sani) ya ke so yai ‘achieving’ to?”

Loading

Tags: 'Wasila'Abdulrasheed Kankiya Abaabfake newsFaransaFaransanciFulatanciGrassroots AfricaHadiza Aliyu Gabonlabarin ƙaryaMujallar FimSadiya YarimaSani Muhammad SaniShehu GabamSuleiman LereYakubu Lere
Previous Post

Ba za mu tace finafinan kamfanoni marasa rajista ba, inji Gwamnatin Tarayya

Next Post

Furodusan Kannywood Murtala Aniya ya yi rashin ‘yar sa Fatieha

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Marigayiya Sayyada Fatieha Murtala Aniya

Furodusan Kannywood Murtala Aniya ya yi rashin 'yar sa Fatieha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!