MAWAƘI kuma jarumi a Kannywood, Misbahu M. Ahmad ya yi ƙorafi tare da tunatarwa kan irin salon jagorancin da Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya ke yi.
Misbahu ya yi ƙorafin ne a cikin wani guruf ɗin WhatsApp da ya ƙunshi jagororin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
Bayan ya fara da sallama da miƙa gaisuwa, sai fitaccen jarumin ya ci gaba da bayani cikin shauƙi cewa, “Na sheƙo da gudu zuwa wannan gida domin wasu dalilai guda biyu zuwa uku. Dalili na farko ƙorafi, na biyu tunatarwa, na uku kuma neman mafita.
“Alal haƙiƙa na sani, kwanaki biyu zuwa uku da ake ciki ko su ka gabata, akwai iyaye da yayye na wannan masana’anta waɗanda su ke cikin gidan ‘Vanguard’, da ma waɗanda su ke cikin sauran guruf, da yawa na san sun ji irin maganganu ko tataɓurza na ƙorafe-ƙorafe, wanda kusan ni na assasa wannan abu, ni na kawo magangagun na koke-koke a kan wasu abubuwa da su ka shige mana duhu, musamman na jagorancin shugabannin MOPPAN na ƙasa, daga kan firesiden da kuma sauran ‘exco’ ga baki ɗaya.
“Abin ya taso ne bayan wasu ‘yan maganganu da na ci karo da su. Ɗaya daga ciki shi ne zama da ‘exco’ na ‘national’ su ka yi da shugaban ita ƙungiyar ga baki ɗaya na ƙasa, wato ‘president’.
“Akwai wasu ‘yan kalamai da su ka tada mana da hankali ko su ka tada min da hankali, waɗanda su ka fito daga bakin sa, bayan an kawo gida an faɗi ‘minutes’ shi zaman da aka yi da ‘achievement’ da aka samu na zaman da kuma wasu da su rinƙa alhini da tausayawa da kuma kokawa a kan shi ‘president’ na yanayin da ya ke jagorantar ita kan ta ƙungiyar. Daga ciki akwai ƙorafin wasu daga cikin ‘exco’ ko kuma kusan dukkan su ban da mutum ɗaya da ya kama sunan sa, shi ne Alhaji Habibu Barde, kusan duk sun tafi sun bar shi, shi kaɗai ya ke gudanar da ƙungiyar. Wannan abin ya ɗaga min hankali sosai.
“Sannan daga ciki akwai kwamiti da ake so a ba da wakilci za a kafa, wanda kwamitin nan ya na da alaƙa da wasu abubuwa na rijista ko kuma wasu abubuwa da su ka taso na ‘Federal Government’ a kan ‘Censorship Board’, bayan an je an yi mitin za a je a kawo wakilci na ɓangaren ƙungiya. Abin da na yi tunani, ‘national president’ ko kuma ‘national MOPPAN’ za ta ba da wakili ko da za ta nemi ta ba da dama a ‘state chapter’, ita ma ta ba da wakili, ganin cewa Kano dai cibiya ce mai girma in an karɓi wakilin ta ba laifi ba ne, sannan a ba wata ƙungiya kamar yadda aka nemi Arewa ta bayar. To sai na ga wakilci abin da ‘president’ kawai ya tura shi ne ya ba wa MOPPAN ta ‘state chapter’ ta ba da wakilci ba tare da ya tura wakilci na ‘exco’ ba na ‘national’ ko kuma ya su damar tuntuɓar ‘vice president’ ne, ko sakatare-janar a kan ya yi ‘handling’ wannan kes ɗin, saboda shi zai tafi, zai bar ƙasa.
“So, wannan sai na haɗa shi, mutumin da zai bar ƙasa a matsayin sa na shugaba ga baki ɗaya, ya kamata ya tafi da ƙungiya a aljihun sa? Kamata ya yi ya bar ƙungiyar ga mataimakin sa, in ba mataimakin sa, ta na hannun sakatare, a haka, a haka dai ba zai yiwu a ce ‘exco’ ɗin nan mutum goma sha babu kowa ba. Sai ya ce kawai ‘state chapter’ su je su ba da wakilci, a haɗa Arewa ta ba da mutum ɗaya. Ita state chapter MOPPAN ta Kano ta ba da mutum biyu a je a yi. To wannan abin shi ne gaskiya.
“Gaskiya daga cikin abin da su ka zaburar da ni na ga cewa gaskiya ba shugabanci ake yi ba, ba mulkan mu ake ba, ba mulki ake yi na dimokiraɗiyya ba, mulki ake yi mamulkatu, mulki ne na mulkin mallaka, magana ta Allah. Kuma na san gidan nan shaida ne, duk wanda ya ke gidan nan iyaye ne, kun sani, kun san irin yadda mutane su ka fito su ka yi kamfen, su ka rinƙa neman goyon bayan ire-iren ku su taimake su a ba su dama su dawo mulkin nan, wasu kuma su ka ce ba za su dawo ba, su ka haƙura da wanda tun farkon mulkin ma na farko su ka sauka.
“Kuma yawa-yawan waɗanda su ka sauka wasu, mun ji ƙorafe-ƙorafen su: irin wannan mulkin mallakan ne ya sa su ka ga ba za su iya ba. Saboda na yi magana da ɗaiɗaiku, wasu daga cikin su, su na cewa su ba su ga amfanin zaman su ‘exco’ ba domin za a zauna mitin ba ka da dama da za ka ba da shawara a ɗauka, mulki ake yi na mutum ɗaya, abin da duk firesiden ya yanke shi ne daidai; sannan idan ka kawo wani abu in bai yi daidai da abin da ya ke so ba, ba za a zartar ba; sannan idan aka zauna mitin ɗin ba lallai ya ba ka cikakken lokaci ka yi magana da shi ba! To, irin waɗannan abubuwa su ka zaburar da wasu su ka ga ba za su iya ba.
“Wasu kuma abin da ya sa su ka zama ‘discouraged’, su ka ga ba za su iya ba su ka haƙura, sau da yawa ya kan tafi ya yi wasu abubuwa shi kaɗai ba su sani ba. Idan ya dawo, in ya ga dama ya sanar da su, wani sanarwar ma ba za su sani ba sai bayan sun zauna su na wata maganar ko gun mitin ko su na wani abu a guruf, ya ce ga abin da ya yi kwanaki, idan sun yi magana ya zama kamar gori-gori ko ƙorafi cewa sun san lokacin da ya je ya yi irin da zafi-zafi, kamar su na ganin kamar ya na faɗa ba su san irin wahalar da su ke yi ba. Su kuma ba a neme su su yi ba, ba su ce ba za su yi ba.
“To irin waɗannan abubuwan shi ne ya tarwatsa su, daga ƙorafin da ya ke fitowa daga bakin su, ɗaiɗaikun su, daga kwana uku zuwa biyu da ake maganar nan na yi magana da wasu, su ce shi kaɗai ya ke abin sa, ba izinin mu, ba ra’ayin mu, sannan ba lallai ne idan an dawo a faɗa mana abin da aka yi ba.
“So, ni abin da ya sa na kawo maganar gidan nan, nan dai ita ce ƙololuwar uwar daka a masana’antar nan, duk wani mai ji dakan sa ko ya isa, ko ya sani ko ana yi da shi ko an yi da shi, na san ba zai wuce ya na gidan nan ba duk mai kan shi da furfura a cikin masana’antar nan, wanda ko da shi aka haife ta, ko ya na cikin ta ko tsohon shugaba ne, duk wani abu da ka ke nema na san ba za a rasa mutanen da ke gidan nan sun san shi ba. Shi ya sa sai na waiwayo, na ce maganar ma a can kusan ba ta da tasiri kashi hamsin, can duniya ce za ta ji ta masana’antar, nan kuma aƙilai ne mutanen da su ke da ciwon masana’antar, wanda idan magada ne su ke da su a masana’antar, masu magadan su ne a nan, so nan ya kamata na zo na yi wannan maganar, na yi ƙorafi, sannan mu na neman mafita.
“Babban abin da ke damun mu yanzu ‘exco’ sun tarwatse, a wannan yanayin mulkin a ina aka samar da kwamitin da aka gyara ‘constitution’? Shi a wannan gidan shugabannin ko waɗanda aka kafa da su ka gyara ‘constitution’, da ake faɗa a cikin ‘achievement’ ɗin da ake cewa an yi, tunda shi wannan duk abin da ake faɗa cewa MOPPAN ta yi a yanzu a wannan shugabancin da aka yi na shekara biyu zuwa wannan shekara ɗaya da wani abu, ba fa mu gan shi a ƙasa ba. Faɗa ake yi da baki, kuma wasu mutane ne ma da bai fi ka sanin masana’antar ba shi zai zo ya na gaya maka abin da ka fi shi kusa da inda za ka ji. Kuma wasu maganganun ma sun fito ne sakamakon maganganun da mu ka yi yanzu.
“To ka ga ba lallai ne mu gaskata su ba. Idan ma ya faru na ‘achievement’ da wasu ke faɗa, daga ciki mai ɗan gwaɓi-gwaɓin da hankali na ya koma kan sa, na ga ya kamata na tashi yau da magana a kan sa shi ne maganar ‘constitution’. Duk abin da za a ce an yi, in an yi, an yi, in ma ba a yi ba, a je a ba yi ba, amma taɓa kundin tsarin mulki ba tare da cikakken goyon bayan ‘elders’ da shugabannin da su ka riƙe shugabanci a masana’antar ba da masu ruwa da tsaki a cikin masana’antar, ina ganin wannan shi ne babbar asara lalacewa da za a sa ido da masana’antar nan ta yi.
“So, abin da ni na ke tambaya a gidan nan, don Allah akwai kwamitin da su na da masananiyar cewa su ne su ka gyara ‘constitution’ a cikin ‘elders’ ɗin mu ko a cikin tsofaffin shugabannin mu?
“Sannan idan akwai kwamitin nan, ko kuma da aka zo aka shawarta, kwamitin da aka kafa su ka ba da shawarar abin da za a saka ‘constitution’, ko za a ƙara ko za a rage, wannan kwamitin su na nan? An nemi hakan ta yiwu? To idan kwamitin su na nan da su ka ba da shawarwari, bayan an yi abin an dawo masu da ‘constitution’ ɗin sun yi ‘review’ sun duba abin da su ka saka ɗin ko su ka ba da shawarwari ko shawarar ta karɓu? Saboda ‘problem’ ɗin, babu yadda za a yi ana dimokiraɗiyya, kuma ƙungiya shugabanci ne ka zaɓi mutane su yi, ba mulkin soja ba, ba kamfani na ba ko kamfanin ka ko kamfanin wani, ba yadda za a yi a ƙyale wasu tsiraru ko wani mutum haka kurum daga shugabanci ka ɗauki tunanin mutum dubu, ka dunƙule shi ka sa a aljihu, ka je ka aiwatar da wani abu. Ba lallai ne wannan abin da ka sa ra’ayin ka ba ne ko ra’ayin ku ku biyu ba tare da sanin al’umma ba, ya zamo ya taimaki waɗannan dubunnan mutanen, ba lallai ba ne wannan abin ya zame masu mafita a kan masana’antar su da su ke cin abinci shekara da shekaru ba.
“Wannan abin, don Allah ni dai na kawo wannan magana gidan nan. Kuma na sani ni ana kallo na da wasu fuskoki da yawa, musamman fuska biyu: su waɗanda na ke faɗa masu gaskiya ‘direct’ ko na ke jawo hankalin mutane a kalli abin da su ke yi, daga kan shugabanci zuwa kan yadda su ke gudanar da rayuwar su a cikin masana’antar nan, su na kallo na wani rigimamme, wani mara kunya, wani kaza, ni kuma Allah ya sani – shi ne shaida a tsakani na da Ubangiji – damuwa ta da masana’antar nan ita ta sa ni na ke magana. Ban taɓa magana don na ci wa wani mutunci ba ko don na yi wa wani rashin kunya ko don na isa na yi magana, ni ba na iya haɗiyewa idan na ga abin da zai yi ‘tampering’ da tunanin mutanen da ke cin abinci a cikin masana’antar nan, a cutar da mu mu faɗa wani layi. A haka ma mu na ta rarrafe, mun rasa ina za mu miƙe ƙafafun mu.
“To don Allah ina kira ga wannan gida, kwamitin da su ka gyara ‘constitution’ ɗin nan, a neme su in akwai su. Sannan in an gyara ‘constitution’ ɗin nan, kafin ya zama doka, in an yi ‘stamp’ a jiki an yi komai, a kirawo masana masana’antar da mutanen da su ka cancanta su zauna su ga me aka sa a ciki. Idan sun gani, to hakki ne na al’ummar da ake shugabanta a karanta masu abin nan saɗara-saɗara, ko da ‘congress’ ne a yi, a zaɓo wakilci na shugabanni, ‘exco’ na ‘state-state chapter’ su ba da wakilci su zo su ji abin da aka yi, su kuma su tafi su faɗa wa sauran al’umma ko da ƙungiyoyin da su ka yi ‘affliating’ da MOPPAN ne su ka yarda da MOPPAN uwar su ce, ta hanyar siyasa da hanya ta yadda aka yi aka ja su a jiki, da kuma abubuwa da dalilan da su ka sa MOPPAN ta zama ‘umbrella’, to ya kamata a kalli wannan abin a ba wa mutane ‘yancin su, a ba waɗannan ƙungiyoyi dama su san me aka saka, me su ke yi?
“Don Allah gida ina roƙon alfarma, a kalli wannan maganar da idon basira da tunani, kada a bar wannan masana’anta ta zama tunanin wasu mutane ko wani mutum guda ɗaya, don Allah. Hakkin ku ne gaba ɗaya, dukkan mu nan hakki ne. Mu iya abin da za mu yi kenan, mu yi magana, wanda ya ke sa bakin da zai iya yi wa wani na kusa da shi shi ma ya yi motsi na ya ce a dakata a kalli abin a gyara ko a ga ingancin sa, ko a tabbatar da ingancin sa ya yi, ya yi ya gani bai yi magana ba, akwai hakki.
“Ina kira ga iyaye da ‘yan’uwa, abokai da yayyen mu da ke cikin wannan gida, na san mu ne dai waɗannan da mu ke cikin wannan gidan nan, duk wani da zai yi alfahari ko da ya ke gadara ko da ya ke jin ya isa da sunan Kannywood, in dai ɗan Hausa ne Bahaushen fim, ka san cewa waɗanda su ka yi ka su na gidan nan. Ko iyayen ka ko yayyen ka ko abokan ka, to don Allah wannan abin a kalle shi.
“A je ni mara kunya ne, a je ni ɗan rigima ne, a kalli ‘point’ ɗin na maganar da na ke yi, shin maganar ta na da amfani daidai ne a duba, a kalla. In ba daidai ba ne shi kenan, in kuma daidai ne a kalli abin nan don a fitar da mutane ko kuma son a samu maslaha masana’antar nan ta zauna da ‘yancin ta. Kada a bari a ɗauki masana’antar nan ta zama wani tunani, ta fita daga ‘culture’ ɗin mu da tsarin mu na addini da ya kamata mu mu yi rayuwar mu. Saboda da yawa mun aan akwai mutanen da sun samu dama a masana’antar nan su na kallon mutanen da su ka tarar ko su ka kafa masana’antar su kallon su daƙiƙai, ko ba su iya ba ko kuma su ba su sa wayewa, to mu wayewar ce ba mu so a sa mana ita da za ta yi yawan da za ta sa mu fita daga ‘culture’ ɗin mu tsallaka wani waje.
“Duk yadda mu ka kai Bahaushen fim, Hausa fim sunan sa Hausa fim, kuma duk irin abin da za mu yi na kwaikwayo ba mu isa mu tsallaka mu ce sai mun haɗa tunanin mu, addinin mu da al’adar mu irin na mutanen da ba addinin mu ɗaya ba, ba ‘culture’ ɗin mu ɗaya da su ba.
“To wannan shi ne dalilin da ya sa na kawo maganar nan. A yi haƙuri don Allah da hali na, kar a kalli wai ni na cika kaza, na cika kaza, a’a, a kalli maganar in gaskiya ce, ina roƙon alfarma a ɗauki wannan abin a aje shi a layi na gaskiya a zo a zauna mutanen da ya kamata a ba su dama ko a nusar da su su zo su waiwayi wannan abin a bibiya, idan Allah ya sa abin nan successfully ya yi daidai, babu wani gyara ba komai, shi kenan a sanar da mu mu zauna da ƙwarin jikin mu, mu samu natsuwa. Amma a gaskiya halin da mu ke ciki, wallahi musamman ni dai a rai na wallahi ba ni da natsuwa, don ban san me aka sa a ciki ba, har yanzu kuma ban ci karo da wani mutum da ya ce min ni ɗin nan da ni aka yi gyaran ina zaune. Duk wannan surutun da mu ke yi, babu wanda ya kira ni a waya ya ce wallahi ina cikin kwamitin ina zaune aka yi, kuma ga abubuwan da aka sa, kuma daga su ba ƙari ba ragi. Da ma ni ba na so in ji wannan daga wani mutum, na fi so in ji daga cibiya da iyaye da shugabannin ƙungiya da cewa da izinin su da ra’ayin su da tunanin su da kuma shawarwarin su aka aiwatar da abin har ya kammala, wannan shi ne abin da ya kawo ni gidan nan. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.”
Bayan Misbahu ya kai aya, sai ɗaya daga cikin dattawan Kannywood, Malam Khalid Musa, ya ba shi amsa. Ya ce: “Babu laifi yin tambaya don an ce matambayi ba ya ɓata.
“Gyaran tsarin mulki ba laifi ba ne matuƙar an yi bisa ƙai’dar da shi tsarin mulkin ya tanadar. A ƙungiyar MOPPAN gyara a tsarin mulki ba ya tabbata har sai ya sami amincewar ‘ya’yan ƙungiyar a ‘delegate congress’. Abin tambaya a nan shi ne shin an yi hakan?
“Exco’ na ƙasa a wani zama da aka yi sun kafa kwamitin da zai duba tsarin mulkin MOPPAN da nufin kawo gyara a sassan da su ka kamata a gyara saboda tun da aka kafa ƙungiyar ba a taɓa duba tsarin mulkin da nufin gyara ba. An samar da wannan kwamiti da aka ɗora wa alhakin wannan gyara a ƙarƙashin jagoranci na. Kuma mun nemi memo daga kowace jiha ta ƙarƙashin jagororin jiha, amma babu jiha ko ɗaya da ta gabatar da takardar shawarwarin ta kamar yadda mu ka nema.
“Dukkan wuraren da ya kamata a duba mun duba kuma mun samar da yadda ya kamata sashen ya zama. An gabatar da dukkan gyare-gyaren da da aka bijiro da su a gaban ‘congress’ kamar yadda dokar ta tanadar domin amincewar su saboda gyara ‘consititution’ abu ne da ya fi ƙarfin ikon ‘exco’ sai dai ‘congress’. Ɗaya bayan ɗaya aka rinƙa karanta gyararrakin ana neman amincewar ‘congress’, kuma sun amince da dukkan abin da aka gabatar ban da buƙata ɗaya, ita ce ta ƙara wa’adin ‘exco’ zuwa shekaru uku maimakon biyu.
“Bayan doguwar muhawara a kan wannan lamari, ‘congress’ ya amince da ƙara ‘tenure’ ta koma shekara uku-uku amma dokar ba za ta fara aiki a kan wannan ‘exco’ ɗin ba sai a zaɓaɓɓu na gaba.
“Dukkan wata gaɓa da doka ta yi tanadi kafin gyaran tsarin mulki an bi ta, don haka ba ra’ayin ‘exco’ ko ‘President’ ba ne. Kafin ma a gabatar da gyaran a gaban ‘congress’ sai da mu ka zauna da ‘trustees’ mu ka sake tsefe gyararrakin.
“Ina fata wannan ɗan gajeren jawabin zai gamsar da duk mai tambaya ko neman bahasin yadda aka yi aka haihu a rabauta.”
A nan, sai Misbahu ya yi tambaya, ya ce, “Alhamdu lillahi. Allah shi gafarta mallam. Mallam ina dan yanzu mutum na da buƙatar kwafi ina zai samu?”
Malam Khalid Musa ya amsa: “Mun miƙa ‘clean copy’ ga su ‘exco’. Hakkin su ne su yi ‘printing’ don wadatar da shi ga ‘members’ masu buƙatar su mallaki ‘copy’.”