• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Okoye: Jam’iyyu 18 kaɗai INEC ta sani a yanzu

by DAGA WAKILIN MU
March 20, 2021
in Nijeriya
0
Cewar Okoye: Jam’iyyu 18 kaɗai INEC ta sani a yanzu
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ita jam’iyyun siyasa 18 kaɗai ta sani kuma su ne za ta yi aiki da su har sai Kotun Ƙoli ta gama yanke hukunci kan jam’iyyun da aka soke rajistar su.


Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Wayar da kan Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai na hukumar, MistaFestus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai. 


A sanarwar, ya yi kira ga jam’iyyu 74 waɗanda hukumar ta soke rajistar su da su jira hukuncin na Kotun Ƙoli.


Okoye ya ce, “Hukumar Zaɓe Mai Zaman kan ta ta Ƙasa (INEC) ta na ƙara bada shawara ga jam’iyyun siyasa guda 74 da aka soke rajistar su da su jira hukuncin Kotun Ƙoli kan ɗaukaka ƙarar da su ka yi game da hurumin Hukumar na soke jam’iyyun siyasa kamar yadda sashe na 225A na kundin Tsarin Mulki ya tanada.


“A shirye Hukumar ta ke a ko taushe ta bi umurnin kotu kuma za ta yi aiki da kowane irin hukunci da Kotun Ƙolin ta zartar.

“Wannan sanarwar ta zama wajibi saboda ganin yadda wasu daga cikin jam’iyyun da aka soke rajistar su su ke ta turo wa Hukumar Zaɓe da wasiƙu a cikin ‘yan kwanakin nan, su na bayyana niyyar su ta gudanar da zaɓen share fage tare da kawo sunaye da bayanan ‘yan takarar su a zaɓen gwamnan Jihar Anambra.


“Jam’iyyun da aka soke ɗin su na kafa buƙatar su ta fitar da ‘yan takara a kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar a ranar 11 ga Yuni, 11, 2020.


“Hukumar za ta ci gaba da amincewa tare da yin hulɗa da jam’iyyun siyasa guda 18 kaɗai masu rajista har sai mun ga yadda aka ƙarƙare batun ɗaukaka ƙara daban-daban da ke gaban Kotun Ƙoli.”


Ya ƙara da cewa, “Saboda haka, INEC ba za ta sa ido kan kowane irin zaɓen share fage da kowace daga cikin jam’iyyun da aka soke rajistar su za su gudanar ba kuma ba za ta bayar da kalaman sirri ko karɓar  suna da bayanan kowane ɗan takara da aka fitar daga waɗannan zaɓuɓɓukan share fagen.


“Jam’iyyar National Unity Party ta ɗaukaka ƙara a kan wannan hukuncin zuwa Kotun Ƙoli ta Nijeriya kuma yanzu haka maganar ta na gaban kotun. Wannan ɗaukaka ƙarar da wanda Hukumar ta shigar a kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya danganci jam’iyyu 22 da aka soke rajistar su duk su na gaban Kotun Ƙoli.”

Okoye ya tuno da “cewa a ranar 10 ga Agusta, 2020 Hukumar ta fitar da bayani inda ta  nanata cewa hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke inda aka ba jam’iyyu 22 da aka soke gaskiya ya saɓa wa hukuncin da ita dai wannan kotun ta bayar a kan ƙarar jam’iyyar National Unity Party (NUP) da INEC inda kotun ta tabbatar da ikon hukumar na soke rajistar NUP da sauran jam’iyyun siyasar.


“Bayan ta dubi saɓanin da ke akwai tsakanin waɗannan hukunce-hukunce biyu, hukumar ta bada shawarar cewa ‘Abin da ya fi alfanu ga tsarin gudanar da zaɓe shi ne a gama da maganganun biyu a lokaci guda. Tsarin gudanar da zaɓe zai fi inganta ta hanyar samun matsayar ƙarshe a kan batutuwan soke rajistar jam’iyyun siyasa da aka yi. Kuma hakan zai bada dama ga hukumar ta tsaya a kan tsandauri maimakon ta je ta na tunanin wane mataki ne cikin da su ke karo da juna za ta yi wa biyayya.”


Ya ce, “A yanzu dai, ana tunatar da jam’iyyu masu rajista da su tabbatar sun kiyaye tanadin da tsarin mulkin su ya tanadar wajen zaɓen ‘yan takara musamman wajen gudanarwa da fito da ‘yan takara. Wannan ya zama tilas idan aka yi la’akari da ɗimbin koke-koken da ke biyo bayan rushe Kwamitin Zartaswa na rassan jihohi inda wa’adin su bai ƙare ba da kuma umurnin kotu daban-daban masu karo da juna waɗanda su ka shafi zaɓen share fage tsawon lokaci bayan Hukumar Zaɓe ta gama zaɓuɓɓuka.


“Girmama Tsarin Mulki da bin doka da oda su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya. Don haka ana tunatar da jam’iyyun siyasa irin nauyin da ya rataya a wuyan su na tabbatar da sun bi tsarin dimokiraɗiyya a cikin gida tare da bin doka da oda.


“Hukuma na amfani da wannan dama ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su mara wa ƙoƙarin ta na ƙarfafa tsarin gudanar da zaɓe baya. Wannan ƙoƙarin a yanzu ya haɗa da amma ba a iyakance shi ba ga tsarin da aka kawo na ƙara buɗa wa masu zaɓe samun ƙarin rumfunan zaɓe, da ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe,  da yin garambawul ga Dokar Gudanar da Zaɓe, da shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan gwamna a Anambra, Ekiti da Osun da kuma wasu zaɓukan cike gurbi, da zurfafa yin amfani da na’urorin fasaha na zamani a wajen gudanar da zaɓe da kuma shiryawa da wuri don Babban Zaɓen  2023.”

Previous Post

Gwamnati ta taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa

Next Post

Dare Sahibi Na

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Dare Sahibi Na

Dare Sahibi Na

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!