• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cika shekara 60: Buri na a rayuwa ya cika – Ado Ahmad Gidan Dabino

* 'Ban shigo harkar rubutu don neman kuɗi ko suna ba'

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 18, 2024
in Tattaunawa
0
Cika shekara 60: Buri na a rayuwa ya cika – Ado Ahmad Gidan Dabino

Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A RANAR 1 ga Janairu, 2024 ne fitaccen marubuci kuma jarumi a Kannywood, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya cika shekaru 60 a duniya. An haife shi a ranar 1 ga Janairu, 1964. Tun daga lokacin da labarin ya bazu a soshiyal midiya, ‘yan’uwa da abokan arziki suka riƙa rubuce-rubuce na taya shi murna tare da yi masa fatan alheri. 

Ado zaƙaƙuri ne a fagen rubutu da shirya fim, kuma jarumi ne wanda ya fito a ɗimbin finafinai. Yana daga cikin marubutan littattafan soyayya na farko-farko, musamman da littafin sa, ‘In Da So Da Ƙauna’. A yau kuma ya na daga cikin jaruman fim da aka fi sani, musamman saboda da rol ɗin sa na Gwamnan ƙirƙirarrar Jihar Alfawa a cikin diramar talbijin ta ‘Kwana Casa’in’ da ake nunawa a Arewa 24.

Bayan haka, shi ne Ciyaman na kamfanin Gidan Dabino International Publishing Company Limited, Kano, masu wallafa littattafai. Sananne ne a fagen nazarin adabi da al’adun Hausa. Gwagwarmayar da ya yi a waɗannan fagage abar kwatance ce a tarihin ƙasar Hausa.

Wakilin mujallar Fim, MUKHTAR YAKUBU,a yi hira da Ado, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Kwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, domin jin yadda rayuwar sa ta gudana a tsawon waɗannan shekaru sittin da ya yi a duniya, musamman a fagen adabi inda ya yi shuhura.

Mun nemi ra’ayoyin sa kan rawar da ya taka a wannan fagen da kuma burin sa a nan gaba. Kai, hatta batun ƙara aure ba mu bari ba; shin me ya sa ya kasance mai mata ɗaya, kuma ko zai iya ƙara aure kuwa? Ga hirar kamar haka:

FIM: Malam Ado Ahmad, a farkon wannan shekara ta 2024 ne ka cika shekaru sittin, don haka kamar dai sauran jama’a masoya da masu yi maka fatan alheri mu na taya ka murnar cimma wannan muhimmin zango. Kuma za mu so ka yi wa masu karatun mu tsokaci a kan yadda rayuwar ka ta kasance a tsawon wannan lokaci.

MALAM ADO AHMAD GIDAN DABINO: To, alhamdu lillahi, ina godiya sosai. Ina yi wa ɗimbin jama’ar da su ka taya ni murnar kawowa wannan lokaci ina raye cikin nasarar Ubangiji na samu damar gudanar da wasu abubuwa da har mutane su ke amfana da shi, don haka ina ƙara yi wa Allah godiya bisa ni’imomin sa a gare ni.

Kuma gaskiya wannan rayuwa ta tsawon shekaru sittin za a iya cewa rayuwa ce ta gwagwarmaya da idan ka auna za ka ga gwagwarmaya a adabi. Saboda na fara harkar rubuce-rubuce a 1984, wanda a yanzu idan ka duba na shekara arba’in a cikin harkar rubutu.

Hakan ya nuna cikin 60 da na ke ciki a yanzu kaso biyu bisa uku duk a harkar adabi su ka tafi wanda su ka haɗa da rubutun zube, wasan kwaikwayo ko waƙa ko yin aktin ko ba da umarni ko shiryawa, duka a cikin su aka yi wannan shekaru arba’in ɗin.

Kuma daga lokacin da na fara harkar rubutun, ina jin ban daina ba, sai dai ko a yau idan an ji ni a fagen fim na yi shiru, to na koma ɓangaren rubutu ne, ko a ji ni shiru a harkar rubutu, na koma harkar fim, ko kuma duka a ji ni shiru, amma dai hakan ba ya na nufin na daina ba, wata harkar ce dai da ta shafi adabi ta ɓoye ni.

Ana bai wa Malam Ado kyautar karramawa ta musamman (Lifetime Achievement Award) a taron duniya kan adabin Hausa (HIBAF) da aka yi a Kano a Disamba 2023

FIM: A cikin rubuce-rubucen da ka yi a tsawon wannan lokaci akwai na zube, waƙoƙin rubutun fim, maƙaloli, da sauran su. Za mu su ka yi mana bayanin wasu daga cikin su.

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To, na yi rubutun zube na soyayya, ‘In Da So Da Ƙauna’, wanda na fara bugawa a shekarar 1990, wanda da fitowar sa zuwa yanzu ana maganar shekara 34 kenan. Amma su kuma sauran rubuce-rubucen da na yi a baya kafin wannan lokacin, na yi su na gajerun labarai da na ke aikawa gidajen rediyo, musamman na waje, kuma su na karantawa su na biya, don haka a lokacin a nan na fi ba da ƙarfi.

Kuma da na zo fagen littafi shi ma a na soyayya na fi yawan rubutun. Kamar ‘In Da So Da Ƙauna’, ya yi magana a kan soyayya, da ‘Hattara Masoya’, ‘Masoyan Zamani’, ‘Kaico!’

Amma dai ban tsaya a nan ba, na tsallaka na shigo tarihin rubutun tarihi da bincike, inda na rubuta tarihin Sarkin Ban Kano. Musamman na rubuta littafin ‘Mata Da Shaye-shaye na Kayan Maye’, da rubutun takardu da na rinƙa yi don gabatar da su a wajen manyan tarurruka, da waƙoƙi wanda har littafi na wallafa, ‘Dausayin Fasaha’, wanda kuma a yanzu ina rubuta littafi na tafiye-tafiyen da na yi zuwa ƙasashe wanda na ke son na ba da tarihi. To, haka dai rayuwar ta ke tafiya har zuwa yanzu.

FIM: Wannan za mu iya cewa ta ɓangaren littattafai kenan. Idan muka koma ɓangaren fim, yaya rayuwa ta kasance?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: Zan iya cewa da rubutu da harkar wasan kwaikwayo duk lokaci ɗaya na fara, a 1984, lokacin da ƙungiyar Gyaranya Drama su ke taro a nan Shahuci, ina karatu a makarantar Masallaci. To a nan na fara tun a lokacin, don haka shi ma shekara ta arba’in kenan ina yi.

Amma dai ita harkar fim ban shige ta ba sai a 1994 lokacin da na yi fim ɗin littafi na, ‘In Da So Da Ƙauna’, wanda kuma ni na zama mai ɗaukar nauyin shiryawa kuma na zama jarumi kuma marubucin labarin. To ka ga zan iya cewa tun farawa na fara da fagage ba ɗaya ba. Kuma daga lokacin zuwa yanzu na shirya finafinai masu yawa a kamfanin Gidan Dabino wanda idan aka tattara su za su kai guda ashirin, kuma idan aka haɗa da wasu da na yi da ba nawa ba, na yi finafinai a kamfani na za su kai guda arba’in duk da cewa a finafinai na kamfani na sau ɗaya na taɓa fitowa a matsayin jarumi, a ‘In Da So Da Ƙauna’, sai dai fitowa ta musamman. Don haka ina ganin tun daga farawa ta zuwa yanzu, ban fito a finafinan da su ka kai guda hamsin ba.

Fostar taya Malam Ado murnar cika shekaru sittin da iyalin sa suka buga

FIM: Duk da yawan finafinan da ka fito a cikin su, sai ya zama akwai finafinan da aka fi sanin ka da su, musamman ‘Kwana Casa’in’ da ka fito a matsayin Gwamnan Alfawa, wanda shi ne ya fito da kai a duniya. Ko yaya kake kallon wannan fim ɗin a rayuwar ka?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To ina ƙara godiya ga Allah don da yawa mutane suna na su ka sani a rubutu ko a ba da umarni ko a shiryawa, amma a matsayin jarumi ba a san ni ba sai a fim ɗin ‘Kwana Casa’in’, shi ne akuya ta ta yi kuka har mutane suke cewa ai wane marubuci ne a yanzu ya zama jarumi. To gaskiya wannan haka yake, ‘Kwana Casa’in’ shi ne sila ta a gane fuska ta sosai fiye da kowane fim, saboda na yi wasu finafinai a baya amma ba su fito ba.

Misali, na yi ‘Juyin Sarauta’, bai fita kasuwa ba, na yi ‘Bilkisu’, bai fita kasuwa ba; duk suna nan a ajiye waɗanda kuma duk sun riga ‘Kwana Casa’in’ amma saboda wasu dalilai da suka sa ba su fito ba, sai ya zama an fi sani na a ‘Kwana Casa’in’, don haka shi ne ya zama silar sanin suna na kuma ina alfahari da shi da ya zama shi ne ya fito da fuska ta na tuna wasu ina nan da rai. Wasu kuma da ba su san ni ba – kamar ‘yan shekaru talatin – sai a yanzu suka san ni, don ba su san fim ɗin ‘In Da So Da Ƙauna’ ba.

Saboda haka duk wani abu da ake so a samu, in dai don shahara ne ko ɗaukaka, to sai godiyar Allah, don ya yi mini su. Domin zai yi wahala na zo waje a yi abu a gama ba tare da an samu mutum ko ɗaya da bai san ni ba a wajen, ko a rubutu, ko a fagen shirya fim.

To, ka ga sai a gode wa Allah, don akwai waɗanda suna yi amma idan sun shiga wani wajen ba za a gane su ba. Ka ga wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mini wadda wasu bai ba su ba.

Don haka duka abin da nake so na zama na zama, don na kai yanayin da tarihi ba zai manta da ni ba a fagen rubutu ko a fagen harkar fim. Don haka na cimma buri na na shigowa ta harkar adabi, domin ni da man buri na da na shigo harkar rubutu ina da burin na ilimintar kuma na faɗakar.

Ban shigo harkar rubutu don neman kuɗi ba, kuma ban shigo don neman suna ba. Kawai dai ina da wani abu da yake a rai na da nake so na faɗakar da mutane cewa su ma idan sun samu kan su a irin wannan yanayi ga abin da za su yi su yi maganin kaza.

Kuma sai godiyar Allah, mun faɗakar mun ilimintar, kuma wasu saboda rubuce-rubucen mu sun koya, wasu sun koyi rubutu, wasu sun koyi karatu, ba ma a Nijeriya da Nijar da sauran ƙasashe da ake yin Hausa ba, za ka ga wasu suna nan suna sauraron shirye-shiryen mu ta hanyar kallo da sauraro, da haka har su koyi Hausa.

To, ka ga buri na na in faɗakar in ilimintar na same shi. Saboda waɗanda ba Hausawa ba sun iya ta, sun iya rubutun da karatun duk ta sanadin gudunmawar da muka bayar.

Suna kuma na same shi. Kuɗi kuma ina da rufin asiri, don ba zan ce ni mai kuɗi ba ne, don shi rufin asiri shi ne rayuwa; da yawa akwai masu kuɗi amma asirin su bai rufu ba. Don haka ake neman rufin asiri a rayuwa kuma Allah ya ba ni mutane iya nawa.

Malam Ado Ahmad tare da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

FIM: A tsawon waɗannan shekaru a ɓangaren iyali, ko Ado yaya kasance?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To a yanzu dai mata ta ɗaya kuma ‘ya’ya na shida, maza biyu mata huɗu. Kuma a 1992 muka yi aure; zuwa yanzu shekarar mu 32 da ita.

FIM: Wasu za su ce a tsawon waɗannan shekaru me ya sa Ado Gidan Dabino bai ƙara aure ba?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To, ka san kowa da yadda Allah yake yin sa, wani ma’abocin son ya yi aure ne, ya yi ta aure-aure, wani kuma ba mai son ya yi haka ba ne don yana ganin ko ɗayar ta ishe shi ko kuma yana da niyyar ƙarawa Allah bai kawo lokacin ba, ka ga mutum ba zai yi ba. Amma dai akwai niyya ma, don haka kowa da yanayin yadda tsarin sa yake, saboda haka aure da mutuwa lokaci ne.

FIM: Ko a tunanin ka kana da burin ƙara aure a nan gaba?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To me zai hana? Ai ni mutum ne, kuma dalilan da za su kawo a ƙara aure ai suna da yawa. Don akwai rasuwa, idan mutum yana tare da iyalin sa ta rasu sai ya ce ba zai ƙara aure ba?

Don haka idan na ce ba zan ƙara aure ba kuma Allah ya yi ita za ta riga ni mutuwa sai na ce ba zan ƙara aure ba? Saboda haka ni a yanzu ba zan ce wai ba zan ƙara aure ba, ko zan ƙara, saboda Allah ne ya san wannan a tsarin rayuwar ka.

Ado yana miƙa kyautar littattafan Dakta Bukar Usman, OON, ga tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Matawallen Bauchi Malam Isa Yuguda, a lokacin taron Dangin Juna Masoya Ala Foundation a Bauchi a ranar 6 ga Janairu, 2024

FIM: A daidai wannan lokacin da aka kai ga shekaru sittin, ko wane irin buri ko rayuwa ka tsara a shekarun ka na gaba?

ADO AHMAD GIDAN DABINO: To, rayuwa ta gaba dai shi ne za mu ci gaba da abin da muke yi wa mutane na taimako a fagen da muka saba ta hanyar adabi. Shi na iya, shi nake yi, don shi na kwashe biyu bisa uku na rayuwa ta, don haka zan ci gaba da yi har ƙarshen rayuwa ta. Wannan shi ne abin da nake fata in taimaki sababbin marubuta da masu shirya finafinai da jarumai da duk wani mai harkar adabi ta duk yadda na ga zan taimaka musu.

Da man muna yi kuma za mu ci gaba, domin mu tamu ta yi kyau, domin ba alfahari ba, tun da na fara harkar adabi, ba na jin an taɓa mantawa da suna na. Ko da ba a gani na, ana jin suna na. Don na san akwai lokacin da na shekara wajen goma ban yi sabon littafi ba, tun daga littafin da na yi a 1997, ‘Duniya Sai Sannu’, sai da shekara goma sannan aka ga littafi na ya fito, amma wannan ba ta sa an daina jin suna na ba ko a taron marubuta ko kafa ƙungiya ko kafa jarida ko mujalla, harkar rediyo, harkar talbijin, duk ana nema na.

Don haka ina nan ban taɓa tafiya hutu ba. Idan ba ka same ni ba a harkar littafi, to na tafi harkar fim ko harkar rediyo. Saboda haka ka ga abin da muke fata kenan – taimaka wa adabin da kuma bunƙasa shi, da yayata shi da kuma tallata shi a duniya.

Don haka ina kira ga ‘yan’uwa marubuta da ba su kai shekaru na ba da su kwaikwayi yadda muka yi tamu rayuwar ta harkar adabi, wato su tsaya su jajirce, domin duk abin da ka tsaya za ka yi shi da gaske, to za ka yi nasara.

FIM: To madalla. Mun gode.

ADO AHMAD GIDAN DABINO: Ni ma na gode.

Ado Ahmad Gidan Dabino riƙe da hatimin karramawa ta musamman da aka ba shi a taron HIBAF a Kano cikin Disamba 2023

Loading

Tags: adabiAdo Ahmad Gidan Dabinocika shekaru sittinKannywoodzagayowar ranar haihuwa
Previous Post

Idris ya ƙaddamar da shugabannin hukumar gudanarwar NIPR, ya jaddada aiki tare domin cimma nasarar Ajandar Sabon Ƙudiri

Next Post

‘Yar jarumin Kannywood, marigayi Aminu Mai Chemist za ta yi aure gobe

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Next Post
‘Yar jarumin Kannywood, marigayi Aminu Mai Chemist za ta yi aure gobe

'Yar jarumin Kannywood, marigayi Aminu Mai Chemist za ta yi aure gobe

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!