• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Daraktocin Kannywood sun samu horo kan yadda za su gudanar da aikin su

by MUKHTAR YAKUBU
November 17, 2024
in Labarai
0
Daraktocin Kannywood sun samu horo kan yadda za su gudanar da aikin su

Wani bangare na mahalarta taron suna sauraron jawabi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A sakamakon buƙatar ilimintarwa da ƙwarewa da ake da ita a masana’antar Kannywood, Kamfanin AMAAH Media Innovations Limited, ya ɗauki nauyin shirya taron horas da masu bayar da umarni wato Daraktocin Kannywood na tsawon wuni uku domin koyar da su yadda za su bunƙasa sana’ar ta su.

Taron wanda aka gudanar da shi a ɗakin taro na American Corner dake ɗakin taro na Murtala Muhammad dake titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano, an gudanar da shi ne daga ranar Juma’a 8 zuwa Lahadi 10 ga Nuwamba 2024.

Ameen M Auwal, Shugaban Kamfanin Amah Media Innovations Limited, da ya ɗauki nauyin shirya taron

Tun da farko da yake jawabi a kan manufar shirya taron, Shugaban Kamfanin Amah Media Innovations Limited Alhaji Ameen M Auwal, ya ce “Manufar shirya wannan taro na Daraktocin Kannywood a wannan lokacin shi ne samar da hanyar ƙwarewa da kuma ilimintarwa a game da yadda harkokin fim suke tafiya a duniya ta hanyar ci gaban zamani, ta yadda za mu samar da ilimin harkar fim mai inganci a cikin masana’antar Kannywood.

“Wannan wani tunani ne da yake a zuciya ta tun a lokacin da aka yi sabon zaɓe na Ƙungiyar Daraktocin Kannywood.

A yanzu muna cikin takaicin yadda ita harkar fim ɗin take a yanzu, da kuma yadda daraktoci da yawa ba su san su waye su ba a wajen yin mu’amala da furodusoshi da jarumai da su kansu masu kallon fim ɗin da ma al’ummar gari baki ɗaya.

“Saboda idan ka duba shi darakta daga cikin al’ummar ya fito, sai ya zam su daraktocin daban, kuma kallon da ake yi musu daban. To wannan abin shi ne yake ta yi mini ciwo, saboda yadda na samu damar zuwa wurare da yawa wanda ina ganin da yawan su ba su samu sun je ba, kuma ilimin harkar ne da yawa ya hana su zuwa ba wai rashin ƙwazo ko kaifin basira ba.

Dakta Musa Abdullahi Sufi tare da Abba El-Mustapha a wajen taron

“To idan na je irin wannan waje har kunyar gabatar da kaina nake yi a matsayin wanda ya fito daga masana’antar Kannywood, saboda yadda ake yi mana kuɗin goro, ana yi mana kallon wasu irin mutane na daban. To wannan ya sa na fito da takaice na don samar da duk wata hanyar da za a kawo sauyi ta hanyar ci gaban zamani da kuma ilimintarwa a wannan masana’antar tamu wajen ɗaukar nauyi na horaswa, wadda za ta nunawa darakta wanene shi kamar yadda ya kamata ya zama ta wajen mu’amala da tunani kamata da kuma yadda zai gudanar da aikin sa cikin ƙwarewa da gogewa.

“To kasancewa jagoran ƙungiyar Nasir B Muhammad kowa ya san shi da ƙwarewa a wajen aiki yana da ƙwazo kuma yana da ilimin sanin abin da kuma basira, sai ya ci gaba da tuntuɓa ta a kan alƙawarin da na yi, wanda shi ne a yanzu ya kawo mu ga shirya wannan taro, don haka muna fatan za mu amfana da abubuwan da za a gabatar na tsawon wuni uku da aka shirya za a yi ana gudanar da taron, yadda za a samar da tunani na ci gaba.”

Bayan ya kammala jawabin an ci gaba da taron in da Nasir B Muhammad ya jagoranci koyar da yadda za a tsara labari da yadda za a gane yadda za a yi kasafin sa kuma a aiwatar da shi yadda ya kamata har zuwa bada umarni, in da aka shafe tsawon wuni guda ana bayar da horo.

Ameen M Auwal tare da Nasir B Muhammad suna koyar da yadda ake aikin bada umarni

Horaswar ba ta tsaya iya koyar da bayar da umarni ba kaɗai, domin kuwa, Dakta Amina a nata ɓangaren ta yi magana ne a kan muhimmancin lokaci yadda za a yi amfani da lokacin wajen gudanar da aikin.

Hakanan ta bayar da ilimi a kan aikin haɗaka a game da gudanar da harkar fim. Haka nan ta yi magana a kan ilimin yin mu’amala, domin canza tunanin mahalarta a kan yadda mu’amalar za ta kasance a wajen gudanar da aikin su.

Shi kuwa Dakta Musa Abdullahi Sufi ya yi nasa jawabi ne a kan mu’amalar ‘yan fim da sauran ƙungiyoyin ciki ga kuma na ƙasashen waje da kuma yadda za su ci moriyar yin mu’amalar.

Dakta Musa Abdullahi Sufi yana jawabi yayin taron

Haka nan ya yi magana a kan yadda Daraktoci za su bi matakai na neman tallafin ko rance daga gwamnatoci ko ƙungiyoyin bayar da tallafi domin bunƙasa harkar ta su.

An dai yi jawabai da dama a tsawon wuni uku ɗin da aka yi ana gudanar da taron kuma daga ƙarshe, Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya jagoranci bayar da takardar shaida ga mahalarta taron.

Abba El-Mustapha yana bayar da katin shaida ga mahalarta taron

Da yake jawabi yayin kammala taron, Ameen M Auwal ya ce “Wannan taro ya ƙara mini wajen ƙara shirya wani a nan gaba, don haka idan duk abin da zan mallaka ne, zan iya bayarwa don ganin an canza daga yadda ake tafiyar da harkar fim a yanzu, domin a daina kallon ‘yan Kannywood a matsayin waɗanda ba su ƙware ba, don haka ina ƙalubalantar Gwamnatin Jihar Kano ta hanyar Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, wanda a yanzu muke tare da shi, wanda idan har a matsayina na kamfani mai zaman kansa na fitar da wasu kaso na kuɗaɗe na wanda ya kamata na yi wata hidima ta da su, na zo na zuba su a kan wannan harkar, su a matsayin su na Gwamnati me suke so su yi don haka muna son mu ga an samar da irin wannan taro domin ilimintarwa ga wannan babbar masana’anta tamu ta Kannywood mai albarka.”

Loading

Tags: daraktocihoraswa
Previous Post

Zainab ‘yar jarumi Ahlan ta yi saukar karatun Alƙur’ani

Next Post

An ɗaura auren jarumin barkwanci Ayatullahi Tage

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
An ɗaura auren jarumin barkwanci Ayatullahi Tage

An ɗaura auren jarumin barkwanci Ayatullahi Tage

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!