BAKIN fitaccen jarumi Shariff Aminu Ahlan ya cika da fara’a saboda murnar saukar karatun Alƙur’ani mai girma da ‘yar sa Zainab ta yi.
Jarumin ya wallafa a shafin sa na Facebook tare da nuna godiyar sa ga Allah cewa: “Alhamdu lillah. Alhamdul lillah… Saukar Alƙur’ani na daughter ɗi na Zainab Shariff Aminu Ahlan. I am feeling on top of the world. Abin alfahari ‘ya’ya na uku duk sun sauke Alƙur’ani and Zainab is simply a genius….Ita tata brain ɗin ta daban ce. She is simply unique… Alhamdu lillah. Enjoy ur weekend.”

Aminu Ahlan ya yi wa mujallar Fim ƙarin bayani da cewa, “Abin da ya sa na ce ita ƙwaƙwalwar ta ta daban ce, saboda ita Zainab saukar karatun Alƙur’ani ta hadda ta yi, don haka ina alfahari tare da jin daɗin wannan saukar karatun Alƙur’ani mai girma da Zainab ta yi. Allah ya sa mai amfani ne a gare mu da ita duniya da lahira.”
An dai yi taron bikin saukar karatun ne a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2024 a gidan Ahlan da ke unguwar Gaida a cikin garin Kano.