• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Samira Saje: Abin da ya sa na daina fim na kama sana’a

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 25, 2019
in Labarai
0
Samira Saje (a dama) tare da Kamal S. Alƙali da Hauwa S. Garba a lokacin ƙaddamar da Samsaj Beauty Parlour

Samira Saje (a dama) tare da Kamal S. Alƙali da Hauwa S. Garba a lokacin ƙaddamar da Samsaj Beauty Parlour

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAYA daga cikin matasan jaruman Kannywood, Ruƙayya Suleiman Saje, wadda aka fi sani da Samira Saje, ta bayyana cewa ƙoƙarin dogaro da kai tare da sama wa jama’a aikin yi ne ya sa ta buɗe shaguna nata na kan ta.

 Shagunan sun haɗa da wajen gyaran gashi na mata da na gyaran jikin mata da kuma na sayar da kayan kwalliya irin su tufafi, turare, jakunkuna da takalma. 

Samira Saje ta bayyana haka ne a hirar da ta yi da mujallar Fim kwana kaɗan bayan an kammala bikin ƙaddamar da shagunan nata masu suna Samsaj Beauty Parlour, wanda aka yi da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Laraba, 20 ga Nuwamba, 2019. 

An yi ƙwarya-ƙwaryan bikin a shagunan da ke lamba 148, Titin Lawan Dambazau, daura da filin kasuwar duniya (Trade Fair) kuma kusa da shagon ɗaukar hoto na Balancy Photography da ke garin Kano.

Samira tare da ‘yan’uwa da abokan arziki

 A tattaunawar ta da wakilin mu, kyakkyawar matashiyar, wadda ta daɗe da barin fitowa a fim, ta fara ne da hamdala, ta ce, ““Alhamdu lillah! Babu abin da zan ce sai dai in yi godiya ga Allah da Ya nuna mani ranar da na buɗe wannan shago.  

“Tun da farko da ma na taɓa buɗe shago a Katsina, wanda na buɗe a shekarar 2016.  

A kan bambancin da ke tsakanin wannan sabon shagon da na Katsina, Samira ta ce, “Wannan da na buɗe ya fi wancan girma da kyau.

 “Shago na na Katsina ɗaki ne guda ɗaya, wannan kuma ‘three-bedroom apartment’ ne da falo, kuma falo ɗin kaɗai ya kai girman ɗaki uku ko huɗu ma.  

Ana raba abin tanɗe-tanɗe a wajen ƙaddamar da Samsaj Beauty Parlour

“Yadda na raba abin, falo ɗin na yi ’boutique’ ne (wato wajen saida tufafi), ɗaki ɗaya kuma ‘saloon’ ne da duk abin da ya shafi gyaran kai. 

“Akwai ‘makeup studio and academy’ – wurin yin kwalliya da kuma koyo. 

“Akwai kuma ofis ɗi na, akwai wurin gyaran jiki (spa) irin na gargajiya, irin su Halawa, Dilka da sauran su.

“Sannan a falo ɗin ba kayan mata kawai ba ne na saka, har da na maza, irin su ɗinkakkun shadda, huluna, leshi, takalma da sauran su. Ka ga ‘unisex’ kenan a falo ɗin.  

“Ɓangaren mata kuma akwai dogayen riguna, takalma, ‘yankunnaye, agoguna da sauran su.”

Samira tare da wasu ma’aikatan shagunan

 Mujallar Fim ta yi mata zancen aikin albashi tunda dai ta yi karatun digiri har ta gama, kuma ta yi bautar ƙasa, wato NYSC. Sai Samira ta ce, “A gaskiya tun can baya na daɗe da sha’awar in zama ‘entrepreneur’ (wato ‘yar kasuwa). Tun tuni na ke da sha’awar hakan. A haka dai na ke ta yi kaɗan-kaɗan, har na fara girma na buɗe shago na na farko a Katsina.
  “Ban da wannan, na yi difloma ɗi na a ‘Banking and Finance’, digiri kuma na karanta ‘Accounting’.” 

Samira ta bada shawara ga matasa, ta ce, “Ba Nijeriya ba kawai, duk duniya bai kamata mutum ya tsaya ba don shi ya gama jami’a ya ce lallai sai ya yi aikin gwamnati ko ya na jiran gwamnati ta ba shi aiki. 

 “Abin da ya kamata, kai ma ka samu aikin da za ka rinƙa yi, saboda sai ka taimaka wa gwamnati sannan ita ma za ta samu ƙarfin da za ta riƙe jama’ar ta. Don haka jama’a su ne gwamnati, in babu jama’a babu wani abu wai shi gwamnati.”

 Shugabar kamfanin na Samsaj Limited ta yi nuni da cewa ita tun a gidan su ta ga yadda iyayen ta su ka tashi tsaye wajen neman na kan su.  

“Mahaifiya ta ma’aikaciyar banki ce, amma duk da haka ta na da sana’a,” in ji Samira.  

“Na tashi na samu akwai shagon ɗinki a ƙofar gidan mu, wanda maman mu ta buɗe. Ta na da ma’aikata matan aure, su su ke yin ɗinkin. Da ta dawo daga ofis za ta je shago ta yanka masu kayan, za su yi ta ɗinki dare da rana.


“Ka ga ina iya cewa ni ‘yar gado ce ta wani ɓangaren! Don mahaifi na ma duk da abubuwan su na sarauta, wannan bai hana shi yin sana’a da kasuwanci ba, don mahaifi na bai taɓa aikin gwamnati ba.  

Samira Saje cike da farin ciki a wajen ƙaddamar da shagunan ta a Kano

“Ni kawai na tashi ne na zaɓi in zama ni da kai na. Don haka ni yanzu ba kowane irin aiki zan yi ba. Don a gani na sana’ar da zan yi zai sa in zama ‘boss’ ɗin kai na har ni ma in samu.”  

A game da batun sama wa mutane aiki da ta yi, Samira Saje ta ce, “Ni yanzu abin alfahari ne a ce ina ɗaukar ma’aikata kamar yadda gwamnati za ta ɗauka. Yanzu haka na ɗauki ma’aikata biyar, da ni shida. Kenan ka ga yanzu akwai mutum biyar da na ke biyan su albashi. Yanzu ni ina da shi, wani na da shi, ka ga mun rage wa gwamnati nauyi.” 

To ina batun fim? Samira ta ce, “Gaskiya ni kam yanzu babu maganar fim. Don na daɗe da daina yin fim, tun shekarar 2016.  

“Sai dai in zan yi wani abu nan gaba in shirya fim, tunda kamfani na na da rijista, kuma ‘limited liability’ ne, zan iya yin komai da komai. Don haka wataƙila nan gaba zan iya bada umarni da kuma shirya fim, amma ba aktin ba.” 

Samira Saje ta faɗa wa mujallar Fim burin ta game da wannan sana’a da ta sa a gaba. Ta ce: “Yanzu shiri na a kan wannan shago shi ne yadda na buɗe wannan shago babba haka, shaguna wurin biyar a ciki, a nan gaba Allah ya ba ni iko in buɗe wanda ya fi shi, wanda zan samu mutane da yawa su amfana da abin da na ke da shi.”

Samira da yayan ta

 Ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki dai sun halarci bikin buɗe shagon na ‘Samsaj Beauty Parlour’, cikin su har da wasu ‘yan fim da su ka haɗa da darakta Kamal S. Alƙali, jarumi kuma mawaƙi Ado Gwanja, furodusa Naziru Ɗanhajiya, jaruma Hauwa S. Garba (Maama), da tsohuwar jaruma Halisa Muhammad. 

Kowa ya tafi ya na ta sa albarka tare da faɗin cewa a gaskiya Samira Saje ta burge shi.

Loading

Previous Post

An naɗa Fati Nijar Gimbiyar Mawaƙan Turai

Next Post

Sirrin Abdul D. One, yaron Umar M. Shariff

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Abdul D. One a cikin ofishin sa a Kaduna

Sirrin Abdul D. One, yaron Umar M. Shariff

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!