• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, November 2, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Duk da gobara, mun shirya wa zaɓen gwamnan Ondo, inji shugaban INEC

by DAGA WAKILIN MU
October 6, 2020
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmud Yakubu

Farfesa Mahmud Yakubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta gama duk wani shiri don  gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Ondo a ranar Asabar mai zuwa, 10 ga Oktoba, 2020.
 
Farfesa Yakubu ya ce, “Hukumar ta shirya wa zaɓen. Yau kwana na biyu a nan Jihar Ondo ina duba shirye-shiryen da mu ka yi kuma na gamsu da abin da na gani.”
 
Shugaban ya bada wannan tabbacin ne a wajen wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki  a wani babban zauren taro da ake kira Dome International Culture and Event Centre a birnin Akure a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2020.
 
Ya yi wannan bugun ƙirjin ne duk da yake an yi wata gobara wadda ta laƙume injinan karanta katin zaɓe kamar yadda aka faɗa a labarai kwanan nan.
 
Farfesa Yakubu ya ƙara da cewa,  “Game da gobarar nan abin baƙin ciki da ta faru wadda a watan jiya ta cinye dukkan injinan mu na karanta katin zaɓe a Jihar Ondo,  mun kawo isassun madadin su daga Jihar Oyo kuma mun sake saita su don zaɓen da za a yi ran Asabar. Mun yi isasshen shiri tare da Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Ƙasa don tabbatar da cewa irin wannan abu bai ƙara faruwa ba.”
 
Yayin da ya ke lissafa irin natakan da aka ɗauka don samun gudanar da zaɓen ranar Asabar cikin nasara, Farfesa Yakubu ya ce, “Mun ɗauki dukkan ire-iren ma’aikatan wucin gadi da mu ke buƙata, mun horas da su, mun tantance su, saboda zaɓen. Mun kai kayan aiki marasa hatsari zuwa dukkan Ƙananan Hukumomi guda 18 na Jihar Ondo. Mun gargaɗi ma’aikan mu (na wucin gadi da na dindindin) da su yi aiki bisa ƙwarewa kuma ba tare da wariya ba wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora masu. Ana ci gaba da aikin wayar da kai da faɗakar da masu zaɓe. 
 
“Mun gama shirin kwasar ma’aikata da kayan aiki zuwa wuraren zaɓe a dukkan rumfuna 3,009 da mazaɓu 203 da ke faɗin jihar. 
 
“Yau da yamma, Babban Bankin Nijeriya zai kai dukkan kayan aiki masu hatsari zuwa reshen sa na Akure.”
 
Ya ce: “Mu na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa tare da hukumomin tsaro a ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomi kan Tsaro a Zaɓen (Inter-Agency Consultative Committee on Election Security, ICCES) don tabbatar da yin zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsaro a ranar 10 ga Oktoba.” 
 
Ya miƙa godiya ta musamnan ga dukkan hukumomin da ke cikin ICCES, musamman jagorar hukumomin, wato rundunar ‘Yansandan Nijeriya, saboda yadda su ke ci gaba da bada goyon baya da aiki cikin ƙwarewa a lokacin da ake shirin zaɓen.
 
Shugaban na INEC ya kuma faɗi cewa: “Tun daga lokacin da Hukumar ta fitar da jadawalin ranaku da ayyukan zaɓen gwamna na Jihar Ondo watanni takwas da su ka gabata a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, mun yi ta aiki tare da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su a wajen tarurruka daban-daban. Kuma mun yi ta musayar ra’ayoyi da hukumomin tsaro a mataƙin ƙasa da na jiha. 
 
“Mun yi tuntuɓa tare da neman goyon baya da addu’ar Majalisar Sarakuna ta Jihar Ondo. Mun zauna da shugabannin addini, ƙungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafofin yaɗa labarai. 
 
“Mun tattauna da Kwamitin Wanzar da Lumana na Ƙasa (National Peace Committee) da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abdulsalami A. Abubakar, GCFR, wanda ya gayyato jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar don su zauna su rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a nan Akure gobe.”
 
Farfesa Yakubu ya ce, “Babban burin mu shi ne mu tabbatar da cewa zaɓar wanda zai zama Gwamnan Jihar Ondo gaba ɗaya ya na hannun masu zaɓe. 
 
“Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zaɓe cewa kowace ƙuri’a da za a kaɗa za ta yi tasiri kuma wanda jama’ar Jihar Ondo su ka zaɓa kaɗai ne zai kasance sakamakon zaɓen.
 
“Ina so in tabbatar wa da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su cewa za mu ci gaba da kasancewa masu bin dokoki da ƙa’idojin aikin mu. 
 
“Bari in ƙara tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa Hukumar Zaɓe ba za ta ɗauki kowane irin mataki don ta daɗaɗa ko baƙanta wa wata jam’iyyar zaɓe ko ɗan takara ba.
 
“Hukumar ta yi nazarin yadda ta gudanar da zaɓen gwamna kwanan nan a Jihar Edo. A shirya mu ke mu ci gaba da inganta aikin mu. Saboda wannan dalilin, mun gano wurare 16 da ke buƙatar inganta aiki, waɗanda su ka haɗa da kayan aiki, ɗaukar mataki kan injin zaɓen da ya samu matsala cikin gaggawa a Ranar Zaɓe, matsalar sayen ƙuri’a a lokacin zaɓe, da kuma bin dokokin kare kai daga cutar korona. 
 
“Don haka, mun ɗauki hayar motoci da jiragen ruwa na sufuri don kai da kawon kayan aiki a wurare masu tsandauri da kuma waɗanda ke yankunan da ruwa ya ke. 
 
“Mun ƙara ɗaukar ma’aikatan wucin gadi guda 104 don bada tallafi a yankunan da masu zaɓe su ka yi rajista don su yi aikin gaggawa kan injinan karanta kati a Ranar Zaɓe.”

Loading

Previous Post

N-Power: Ana so waɗanda aka tsallake wajen biya su garzaya a tantance su

Next Post

Ciroma: Yadda wani amini na ya so kashe mani aure da Wasila

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Wasila Isma'il tare da Al-Amin Ciroma

Ciroma: Yadda wani amini na ya so kashe mani aure da Wasila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!